Firaministan Pakistan: Shugaba Xi Jinping Shugaba Ne Mai Hangen Nesa
Published: 4th, October 2025 GMT
A kwanakin baya, firaministan kasar Pakistan Muhammad Shahbaz Sharif ya yi hira da wakiliyar babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping shugaba ne mai hangen nesa, wanda ya jagoranci dukkan kasar Sin wajen cimma burin kyautata tsarin tattalin arziki, kana kasar Sin kasa ce ta biyu mafi ci gaban tattalin arzikin duniya, kana tana daya daga cikin manyan kasashe masu karfin soja a duniya, wadda take kokarin koyar da fasahohin ci gabanta zuwa ga kasashe marasa ci gaba a duniya.
Firaminista Shahbaz ya bayyana cewa, shugaba Xi Jinping ya kiyaye tunanin raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’adama, wanda ya bambanta da wasu shugabanni masu ra’ayin kin amincewa da saura. Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya da shugaba Xi ya gabatar tana da hangen nesa, wadda ta sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki, da samar da guraben aiki ga kasar Sin da kasashen da ke makwabta da ita da kuma duk duniya baki daya. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Kasar Sin Ta Kare Matakinta Na Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth
Ya ce barazanar kakaba karin haraji ba hanya ce da ta dace ta hulda da Sin ba, yana mai nanata cewa, kasar Sin ba ta sauya matsayarta kan batun yakin cinikayya ba, wato ba ta son hakan, amma kuma ba ta tsoro. (Fa’iza Mustapha)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA