Aminiya:
2025-10-13@17:54:12 GMT

Yajin aiki: Likitoci sun ba wa gwamnati wa’adin kwana 30

Published: 29th, September 2025 GMT

Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Najeriya (NARD) ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 30 domin biyan buƙatun ’ya’yanta, ko kuma ta fuskanci yajin aiki.

Wa’adin  na ƙunshe ne a sanarwar Bayan taron ƙungiyar, ɗauke da sa hannun shugaban NARD, Dakta Mohammad Suleiman; Sakatare Janar, Dakta Shuaibu Ibrahim; da Sakataren Yaɗa Labarai, Dakta Abdulmajid Ibrahim.

Shugaban NARD, Dakta Suleiman, wanda aka zaɓa a taron domin maye gurbin Dakta Tope Osundara, ya ce wannan wa’adin ba a bayar da shi da wasa ba.

“Ba za mu ci gaba da kallo mambobinmu suna aiki cikin yanayi marar tsaro yayin da aka yi watsi da walwalarsu ba. Idan ba a warware matsalolin cikin kwanaki 30 ba, za mu ɗauki mataki,” in ji shi.

Ɗan sanda ya harbe kansa da bindiga bisa kuskure a Kano NAJERIYA A YAU: Abin Da Ɗangote, PENGASSAN Ba Su Yi Ba Don Magance Rikicinsu

Muhimman bukatun sun haɗa da biyan bashin kuɗin karin girma da ya taru, sakin sabbin lissafin alawus na ma’aikata, dawo da likitoci biyar da aka kora daga Asibitin Koyarwa na Tarayya a Lokoja, da kuma ɗaukar mataki kan jinkirin da aka yi wajen sabunta tsarin albashin likitoci (CONMESS).

Sanarwar bayan babban taron ƙungiyar da ya gudana a Katsina ya kara da cewa, “Babban taron ya buƙaci cewa Gwamnatin Tarayya ta biya duk kuɗaɗen karin girma da ake binsu a cikin kwanaki 30.

“Haka kuma, Ma’aikatar Lafiya da Asibitin Koyarwa na Tarayya, Lokoja, su dawo da likitoci biyar da aka kora a cikin kwanaki 30.”

Ƙungiyar ta kuma koka kan tsawon awannin aiki da ta bayyana a matsayin barazana ga lafiyar ma’aikata, inda ta umarci mambobinta kada su yi aiki fiye da sa’o’i 24 a jere daga ranar 1 ga Oktoba.

Ta buƙaci Ma’aikatar Lafiya ta tsara jadawalin aiki da ya yi daidai da tsarin ƙasashen duniya.

NARD ta kuma nuna damuwa kan matsalar barin Najeriya da likitoci ke yi da ɗaukar ma’aikata kan kwangila sa matsalar asibitoci da kuma ware likitoci masu koyon aiki daga tsarin ma’aikatan gwamnati.

Ta roƙi gwamnati ta aiwatar da tsarin maye gurbin duk ma’aikaci da ya bar aiki domin rage ƙarancin ma’aikata a asibitoci.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: lafiya Najeriya Yajin aiki

এছাড়াও পড়ুন:

Wasu Daga Cikin Muhimman Alamomin Ciwon Kansa

 

Ta wadanne hanyoyi cutar Kansa ke farawa?

Kowace kwayar halitta ta jikin mutum akwai aikin da take yi, asalin kwayar halittar ta kan kasu kashi-kashi; suna mutuwa idan aka fitar da su ko kuma suka lalace, sai wata kwayar ta maye gurbinsu. A irin wannan lokaci ne, Kansar ke samun gurin zama sai ta zuba tata kwayar halittar ta kori asalin kwayar halittar da ke jikin Dan’adam, wanda hakan ke jawo matsaloli a sassan jikin da Kansar ta kama.

Saboda haka, kwayar cutar Kansa; ta kan watsu a sauran sassan jiki, misali Kansar huhu ta kan tafi cikin kasusuwa ta girma, a yayin da kwayar ta yadu; ana kiranta da suna ‘meh-TAS-tuh-sis’, ita kuma Kansar huhu idan ta tafi cikin kasusuwa; ana kiran ta da suna ‘Lung Cancer’ a turance. A bangaren likitoci, kwayar cutar Kansar da ta shiga cikin kashi; daidai ta ke da ta huhu, sai dai idan ta yadu a cikin kashin.

 

Banbance-banbancen cutar Kansa:

Wata Kansar ta kan yadu ne cikin gaggawa, yayin da kuma wata ta ke yaduwa a hankali a hankali, sannan kowacce ana iya yin maganinta ta hanyoyi daban-daban, wata ta hanyar tiyata kadai za a iya samun waraka; wata kuma ta hanyar shan magani.

Idan mutum yana dauke da Kansa, likita ya kan yi kokari wajen gano irin Kansar da yake dauke da ita. Mutanen da ke da cutar Kansa, ana yi musu magani ne gwargwadon irin yanayin wadda suke dauke da ita.

 

Wane matsayi cutar Kansa ta taka?

Duk wanda ke dauke da wannan cuta ta Kansa, likita zai so sanin matakin da ta kai, daga inda ta fara ana kiran sa a turance ‘Cancer Stage’, sannan matsayin da Kansar ta ke shi ne zai taimaka wajen sanin maganin da za a dora mai dauke da lalurar a kai.

Kowace irin Kansa, akwai gwajin da ake yi domin gano matasayin da ta kai. A dokar gwajin matakinta na farko da kuma mataki na biyu, na nuna Kansar ba ta yi karfi sosai ba. Mataki na uku da na hudu kuma yana nuna ta yadu sosai. Mataki na hudu shi ne makura wajen yaduwar ta.

 

Alamomin 20 Na Kamuwa Da Cutar Kansa:

1- Shashsheka da karancin numfashi

2- Tari da ciwon kirji, alama ce ta Kansar huhu ko ta bargo ciwon kirjin kan kasance daga kirjin zuwa kafada, sannan ya sauko zuwa hannu

3- Zazzabi da saurin kamuwa da ciwo, hakan na faruwa ne dalilin asalin kwayar halittar jinin mutum ta tabu

4- Fama wajen hadiye abu, wannan na nuni da an kamu da wannan cuta

5- Futowar kurji me ruwa a wuya, hammata da kuma gwiwa

6- Yawan zubda jini

7- Kasala da yawan gajiya

8- Kumburin ciki

9- Rashin sha’awar abu da kuma daukewar dandano

10- Ciwon ciki da mara

11- Fitar jini daga dubura

12- Rama lokaci guda

13- Yawan ciwon ciki

14- Nono ya yi ja ya kumbura alama ce ta ‘breast cancer’

15- Canjawar kan nono

16- Nauyi da kuma ciwo na fitar hankali a lokacin al’ada, wannan ita ma alama ce ta ‘uterus cancer’, ana bukatar yin hoto (transbiginal)

17- Kumburin fuska

18- Canjawar farce, zai iya kasancewa ‘lung cancer’, idan kuma ya kode ya yi fari to ‘liber cancer’ ne

19- Ciwon baya a bangaren dama, yana nuni da ‘liber cancer’ ko ‘breast cancer’

20-Fesowar kuraje a jikin mutum

Amma sai an je asibiti an ga likita kafin a tabbatar.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Kiwon Lafiya Ko Kin San… Amfanin Sabaya Ga Mace? October 5, 2025 Kiwon Lafiya Matsalar Tasgadewar Kashin Baya September 27, 2025 Kiwon Lafiya Likitoci Sun Fara Yajin Aikin Gargaɗi Na Mako Ɗaya A Abuja September 8, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ba Bu Dalilin Da ASUU Za Ta Fara Yajin Aiki, An Biya Duk Buƙatunsu – Ministan Ilimi 
  • Ba Gudu Ba Ja-da-baya Kan Ci Gaba Da Kwaskwarima Ga Tsarin Haƙar Ma’adanai – Minista
  • ASUU ta tsunduma yajin aikin mako 2
  • Gwamnatin Tarayya Ta Gargaɗi ASUU Kan Yajin Aiki, Ta Ce “Babu Aiki, Babu Albashi”
  • Yajin Aikin ASUU:  Ba za mu biya duk wanda bai yi aiki ba — Gwamnatin Tarayya
  • Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU ta Shiga Yajin Aiki
  • Yanzu-Yanzu: ASUU Ta Tsunduma Yajin Aiki Na Tsawon Mako Biyu
  • ASUU za ta fara yajin aikin mako 2 daga ranar Litinin
  • Tinubu ya tafi Rome don halartar taro kan sha’anin tsaro
  • Wasu Daga Cikin Muhimman Alamomin Ciwon Kansa