Jaridar Wall Street Journal Ta Ce: Har Yanzu Isra’ila Na Ci Gaba Da Neman Wajen Da Zata Tura Falasdinawa Gudun Hijira
Published: 17th, August 2025 GMT
Jaridar Wall Street Journal ta bayyana cewa: Har yanzu gwamnatin mamayar Isra’ila tana ci gaba da neman kasashen da za su karbi ‘yan gudun hijiran Falasdinawan Gaza!
Jaridar Wall Street Journal ta buga wani rahoto da ke cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila tana ci gaba da gudanar da tattaunawar da ta bayyana na zaman natsuwa domin tura ‘yan gudun haijiran Falasdinawa daga Gaza.
Rahoton wanda Samar Sa’ed, Robbie Gramer, da Omar Abdel Baqi suka shirya, ya bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila da Amurka suke yunkurin tura dubban daruruwan Falasdinawa daga zirin Gaza zuwa gare su, matakin da suka gabatar cewa akwai hanyoyin jin kai, amma gwamnatocin yammacin Turai da kasashen Larabawa sun yi Allah wadai da shi da cewa ba gaskiya ba ne, kuma abu ne ba mai yiwuwa ba sannan keta dokokin kasa da kasa ne.
Jaridar ta kara da cewa: Ra’ayin da jami’an gwamnatin mamayar Isra’ila suka yanke lamari ne da ya bayyana a bainar jama’a tun farkon yakin Gaza kuma ya dauki hankula a farkon wannan shekarar lokacin da Shugaba Trump ya ce Amurka na son karbe ikon yankin tare da sake gina shi a matsayin wurin yawon bude ido na kasa da kasa, tare da mayar da da yawa daga cikin mazaunansa miliyan biyu matsuguni mai aminci.
Masana sun ce gwamnatin mamayar Isra’ila da Amurka suna kuma matsa wa Masar lamba don karba tsugunar da al’ummar yankin zirin Gaza a Sinai.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta Bayyana Cewa: Tana Sanya Ido Kan Abin Da Ke Faruwa A Kudancin Caucasus Cikin Lura August 17, 2025 Babban Sakataren Majalisar Tsaron Kasar Iran Ya Bayyana Cewa; Ba Zasu Amince Da Shiga Tsakanin Iran Da Iraki Ba August 17, 2025 Dakarun Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran Sun Jaddada Shirinsu Na Tunkarar Duk Wata Barazana August 17, 2025 Gwamnatin DR Kongo Ta Nuna Rashin Amincewarta Da Zabin Kenya Kan Wajen Da Zata Bude Karamin Ofishin Jakadancinta A Kasarta August 17, 2025 Amurka Ta Dakatar Da Bawa Falasdinawa A Gaza Visar Shiga kasar August 17, 2025 Isra’ila Ta Jefa Boma-Bomai Kan Tashar Samar Da Wutan Lantarki A Yemen August 17, 2025 Donal Trump Yana Goyon bayan Shawarar Putin Na Musayar Kasa Don Zaman Lafiya Da Ukraine August 17, 2025 Dubban Mutane Sun Yiwa Barikin Sojojin Sama A Burtaniya Kofar Rago Saboda Gaza August 17, 2025 Iran Ta Bada Agajin Gaggawa Ga Pakistan Bayan Ambaliyar Ruwa August 17, 2025 Shugaban Iran na Shirin fara wata muhimmiyar ziyara a Armenia da Belarus August 17, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: mamayar Isra ila bayyana cewa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnan Bauchi ya yi ta’aziyyar rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Bauchi, a matsayin babban rashi ga al’umma.
Gwamnan ya bayyana malamin a matsayin jagoran haɗin kai, zaman lafiya, da fahimtar juna tsakanin Musulmi da mabiya addinai daban-daban.
’Yan sanda sun gano harsasai 210 a kan titin Zariya-Funtuwa Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwaA cikin saƙon ta’aziyya da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Mukhtar Gidado, ya sanya wa hannu, gwamnan ya ce Gwamnatin Jihar Bauchi tana alhinin rasuwar malamin.
Dahiru Bauchi, ya rasu da safiyar ranar Alhamis, 27 ga watan Nuwamba, 2025 a Bauchi, yana da shekara 102.
Gwamnan, ya ce Sheikh Dahiru Bauchi babban malami ne na addinin Musulunci, mai imani, tawali’u da hikima.
A cewarsa ya sadaukar da rayuwarsa wajen yaɗa addinin Musulunci, koyar da Alƙur’ani, da kuma taimaka wa mutane wajen tarbiyya.
Marigayin, ya koyar da dubban ɗalibai da suka haddace Alƙur’ani tare da yaɗa addinin Musulunci a sassan nahiyar Afrika.
Gwamnan, ya ƙara da cewa gudunmawar da marigayin ya bayar a fannin tafsiri, fiqhu da tarihi sun taka muhimmiyar rawa wajen ɗora al’umma kan turbar tsira.
Har ila yau, ya ce Gwamnatin Jihar Bauchi za ta ci gaba da girmama marigayin ta hanyar tallafa wa makarantu da manufofin da ya gina, musamman a fannin ilimin addinin Musulunci, tarbiyya da ci gaban al’umma.
Ya yi addu’a rAllah ya gafarta masa kurakuransa, ya sanya shi aAljannatul Firdausi, ya kuma bai wa iyalansa, mabiyansa da ɗaukacin al’ummar Musulmi haƙurin rashinsa.