Sojojin Mamayar Isra’ila Suna Ci Gaba Da Kashe Kansu
Published: 15th, August 2025 GMT
An gano gawar wani jami’in sojin gwamnatin mamayar Isra’ila da ya kashe kansa bayan yaki a Gaza
Rundunar sojin Isra’ila ta sanar da gano gawar wani jami’in sojin gwamnatin mamayar Isra’ila a wani dajin da ke arewacin Isra’ila. Sojan ya kashe kansa ne a lokacin da yake aikin soja, wanda ya kawo adadin sojojin da suka kashe kansu tun farkon wannan shekara zuwa 18, kamar yadda kafafen yada labaran haramtacciyar kasar Isra’ila suka bayyana.
Gidan rediyon sojojin mamayar Isra’ila ya bayyana cewa: Rundunar sojin ta bude bincike kan lamarin, tare da bayyana cewa jami’in da ya kashe kansa yana shiyya ta 99 da ke yaki a zirin Gaza.
Jaridar Yedioth Ahronoth ya watsa rahoton cewa: Jami’in dan shekaru 28 ya shiga yakin da ake yi a zirin Gaza ne a makonnin da suka gabata.
Wani bincike da sojojin mamayar Isra’ila suka gudanar, wanda aka buga sakamakonsa a ranar 3 ga watan Agusta, ya nuna cewa mafi yawan wadanda suka kashe kansu a cikin dakarunta, sun faru ne sakamakon yanayin fada a zirin Gaza.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Duniyarmu A Yau: Ranar 40 Ta Imam Hussain (a) A Bana August 15, 2025 Larijani: Iran Zata Mayar Da Martani Mai Tsanani Kan Duk Wanda Ya Kai Mata Hari August 15, 2025 HRW; Kai Hari Kan Gidan Yarin Evin Na Iran Laifin Yaki Ne August 15, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kai Wani Mummunan Hari Kan Gaza August 15, 2025 Gwamnatin Mali Ta Bankado Wata Makarkashiyar Janyo Hargitsi A Kasar Tare Da Wargaza Shi August 15, 2025 Iran: Suna Bukatar Kawo Karshen Makaman Nukiliya Da Kuma Furuci Maras Daɗin Ji August 15, 2025 Kungiyar Ansarullahi Ta Kasar Yemen Ya Ce; Yahudawan Sahayoniyya Suna Yakar Al’ummar Falasdinu Duka Ne August 15, 2025 Kungiyoyin Kasa Da Kasa Sun Koka Kan Hana Shigar Da Kayayyakin Jin Kai Yankin Gaza August 15, 2025 Laifukan Cin Zarafi Musamman Kisha Kiyashi A Kasar Siyasa Ya Doshi Laifukan Yaki August 15, 2025 Kungiyar Ba Da Agaji Ta Sanar Da Yadda Cutar Kwalara Take Lashe Rayukan Mutane A Kasar Sudan August 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: mamayar Isra ila
এছাড়াও পড়ুন:
Pakistan Ta Kai Hari Kan Kasar Afganistan, Inda Ake Rade-Radin Kashe Shugaban Taliban Na Kasarta
Jiragen saman yaki sun yi luguden wuta kan birnin Kabul fadar mulkin kasar Afganistan, kuma rahotanni masu karo da juna suna cewa an kashe shugaban Taliban na Pakistan
Kafofin yada labaran Afghanistan sun yi ikirarin cewa: Sojojin Pakistan ne ke da alhakin harin da aka kai a Kabul babban birnin kasar Afganistan a yammacin ranar Alhamis.
Tashar Talabijin ta Tolo News da Khabar Online Afganistan sun ruwaito cewa: Sojojin Pakistan sun dauki alhakin hare-haren da aka kai cikin daren jiya a Kabul.
Kakakin Taliban Zabihullah Mujahid ya rubuta a dandalin X a yammacin ranar Alhamis cewa: An ji karar fashewar wani abu a birnin Kabul.
Ya kara da cewa: “Babu wata damuwa, lamarin dai kamar yadda aka saba, ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, kawo yanzu ba a samu hasarar rayuka ba.”
Majiyar leken asirin Afganistan ta shaidawa Al-Araby Al-Jadeed cewa: Shugaban Taliban na Pakistan kuma wani babban kwamandan kungiyar ya tsallake rijiya da baya a harin da Pakistan ta kai kan Kabul.
A halin da ake ciki, wasu kafafen yada labaran Afghanistan sun sanar a cikin wani rahoto da ba a tabbatar da shi ba, y ace: An kashe Mufti Noor Wali Mehsud shugaban Taliban na Pakistan a wani hari da aka kai ta sama a Kabul a daren yau.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Putin: Natanyahu Yana Son Warware Matsaloli Da Iran Cikin Lumana Ba Tare Da Yaki Ba October 10, 2025 Majalisar Turai Ta Bukaci Kasashen Nahiyar Su Kakkabo Jiragen Yakin Rasha October 10, 2025 Sa’o’ii Da Fara Janyewar Sojojin HKI A Gaza An Fara Gano Gawakin Falasdinwa October 10, 2025 Falasdinawa Daga Kudancin Gaza Sun Fara Komawa Gidajensu Da Aka Rusa A Arewacin Yankin October 10, 2025 Rahotanni : Isra’ila ta fara janye dawa wasu yankuna na Gaza October 10, 2025 Amurka ta kakaba wa wasu kamfanoni 50 takunkumi saboda sayen man Iran October 10, 2025 Isra’ila ta ce yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta fara aiki October 10, 2025 Mohajirani: Iran na goyon bayan shawarar Falastinawa kan batun dakatar da bude wuta October 10, 2025 Khalil al-Hayya: Mun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin October 10, 2025 Ministan mai na Nijar ya gana da Jakadan Iran a Yamai October 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci