Farashin Kayayyaki A Nijeriya Sun Sauka Zuwa Kashi 21.88%
Published: 15th, August 2025 GMT
Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta bayyana cewa ƙimar hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ta sauka zuwa kashi 21.88% a watan Yuli 2025, daga kashi 22.22% da aka samu a watan Yuni 2025. Wannan na nuni da raguwa da kashi 0.34% idan aka kwatanta da watan da ya gabata.
Rahoton ya nuna cewa hauhawar farashin abinci na shekara-shekara a watan Yuli 2025 ya kai kashi 22.
A kan lissafin wata-wata, hauhawar farashin abinci a watan Yuli 2025 ya tsaya a kashi 3.12%, raguwa da kashi 0.14% daga kashi 3.25% na watan Yuni 2025. Hukumar ta ce hakan ya samo asali ne daga saukar farashin man gyaɗa, da wake fari, da shinkafar gida, da masara, da fulawa, da dawa, da alkama da sauran su.
Sai dai a fannin hauhawar farashin gaba ɗaya, rahoton ya nuna cewa a watan Yuli 2025 an samu ƙarin kashi 1.99% idan aka kwatanta da kashi 1.68% na watan Yuni 2025, ma’ana ƙimar hauhawar farashin wata-wata da ta fi ta watan da ya gabata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Kaya Masarufi a watan Yuli 2025 hauhawar farashin
এছাড়াও পড়ুন:
Ronaldo Zai Daura Aurensa Na Farko A Rayuwa Tare Da Budurwarsa Georgina
Sun fara soyayya ba da jimawa ba, inda suka fito fili suka bayyana alakar dake tsakaninsu a shekarar 2017, masoyan sun haifi yarsu ta farko, Alana, a watan Nuwamba na shekarar 2017, daga nan suka haifi tagwaye, Bella da Angel, a watan Afrilun 2022, amma jim kadan da haihuwarsu Angel ya rasu, Georgina ta kuma taimaka wajen renon wasu ‘ya’yan Ronaldo guda uku – Cristiano Jr., wanda aka haifa a watan Yuni 2010, da tagwaye Eva da Mateo wadanda aka haifa ta hanyar dashen kwayoyin halittta a watan Yunin 2017.
Ronaldo, mai shekaru 40, ya na cikin kakar wasa ta hudu tun bayan komawarsa kungiyar Al-Nassr ta kasar Saudi Arabia, tsohon dan wasan Real Madrid, Manchester United da Juventus ya lashe kyautar Ballon d’Or sau biyar, hakazalika, ya dauki kofin zakarun Turai biyar, ya kuma lashe gasar cin kofin nahiyar Turai da kasar Portugal a shekarar 2016.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp