Kungiyoyin Kasa Da Kasa Sun Koka Kan Hana Shigar Da Kayayyakin Jin Kai Yankin Gaza
Published: 15th, August 2025 GMT
Kungiyoyin kasa da kasa guda 100 sun koka kan yadda gwamnatin mamayar Isra’ila ta yi watsi da bukatu har 60 kan ba da damar shigar da agaji zuwa Gaza
Sama da kungiyoyi masu zaman kansu 100 ne suka bayyana a wata wasika ta hadin gwiwa da aka buga jiya alhamis cewa, ana kara amfani da sabbin dokokin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta tsara kan ayyukan kungiyoyin agaji na kasashen waje wajen kin amincewa da bukatarsu ta shigar da kayayyaki zuwa zirin Gaza.
Wasikar ta ce: “Hukumomin gwamnatin mamayar Isra’ila sun yi watsi da bukatar da kungiyoyi masu zaman kansu da dama suka gabatar na kawo kayayyakin ceton rai, lamarin da ya bar miliyoyin daloli na agajin jin kai da suka hada da abinci, da magunguna, da ruwa, da na’urorin gaggawa, a rumbun adana kayayyaki a kasashen Jordan, Masar, da Ashdod.”
A cewar wasikar, wacce kungiyoyi irin su Oxfam da kungiyar likitocin da ba su da iyaka suka sanya wa hannu, sun fayyace cewa, an yi watsi da bukatu akalla 60 na kawo agaji cikin Gaza a watan Yuli kadai.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Laifukan Cin Zarafi Musamman Kisha Kiyashi A Kasar Siyasa Ya Doshi Laifukan Yaki August 15, 2025 Kungiyar Ba Da Agaji Ta Sanar Da Yadda Cutar Kwalara Take Lashe Rayukan Mutane A Kasar Sudan August 15, 2025 Miliyoyin Mutane Sun Taru A Karbala Don Juyayin 40 Na Shahadarsa Imam Hussain(a) August 14, 2025 Sayyid Huthi Ya Yi gargadi Yiyuwar Tarwatsewar kasashen yankin idan HKI Ta Tabbaga Shirinta August 14, 2025 An Bukaci Ficewar Marasa Lafiya da Likitoci daga Wani Babban Asbiti A birnin London August 14, 2025 Za’a Fara tattaunawar Kasa Dangane Da Talauci da Kuma Rashin Adalci A Rabin Arziki A kasar August 14, 2025 Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Yi Tsokaci Kan Furucin Netanyahu Game Da Kafa “Babbar Kasar Isra’ila’ August 14, 2025 Iran Ta Bukaci Mayar Da Martani Kan Aniyar Isra’ila Ta Mamaye Yankunan Kasashe Domin Kafa ‘Babbar Isra’ila’ August 14, 2025 Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ya Bayyana Isra’ila A Matsayar ‘Yar Yaudara August 14, 2025 Hizbullahi Ta Yaba Wa Iran Kan Irin Gudumawarta Ga Lebanon Da Gwagwarmaya August 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Hizbullah: Isra’ila na kuskure idan ta na tunanin kashe-kashen kwamandodinmu zai kawo karshen kungiyar
Kungiyar Hizbollah ta kasar Lebanon ta bayyana cewa Isra’ila na yin kuskure idan ta na tunanin kashe-kashe da kisan gillar da ake wa mambobi da kwamandojinta zai kawo karshen kungiyar.
Wannan na zuwa ne bayan kisan gillar da Isra’ila ta yi wa babban kwamandan sojin kungiyar da wasu makusantansa a ranar Lahadi, a wani hari da ta kai a kudancin babban birnin Lebanon.
Haitham Ali Al-tabataba’i da aka fi sani da Abu Ali, ya yi shahada ne tare da wasu dakarun hizbullah guda 4 a wani mummunan hari da Isara’ila ta kai a heret hareik dake kudancin birnin beirut.
Tabataba’I yana daya daga cikin jajircaccen dakarun kungiyar hizbullah , kuma ya taka rawa sosai wajen tsarin tsaron kungiyar tun shekarun farko da aka kafata.
Kisan nasan ya kara nuna irin yadda isra’ila ke keta yarjejeniyar dakatar da tsagaita bude wuta da aka cimma, kuma kisan nasa zai kara karfafa jajircewa a turbar gwagwarmaya a yankunan labanon da falasdinu.
Da yake bayyana hakan Shugaban Majalisar Zartarwa ta Hizbullah, Sheikh Ali Damoush ya ce duk lissafin Isra’ila game da kungiyar ya cutura, saboda ta yi imani da cewa kisan gillar manyan mutane da kwamandojin soja na kungiyar zai iya kai ta ga nasara in ji, a ranar Litinin.
“Irin wadannan kisan gillar suna karfafa kudurin kungiyar na fuskantar mamayar Isra’ila,” in ji shi yayin da yake jawabi a jana’izar Shahid Haytham Ali Tabatabai.
Ya yi wa Tabatabai godiya, yana mai jaddada cewa ya taka rawa a lokacin yakin farko na Hezbollah.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Tashar Talabijin ta Press TV ta kaddamar da sashen harshen Hebrew November 25, 2025 Bincike : Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa Akalla 100,000 a Gaza November 25, 2025 Kasar Gambia Ta Bai Wa Jagoran ‘Yan Hamayyar Siyasar Kasar Kamaru Mafaka Ta Wucin Gagi November 25, 2025 China Ta Yi Tir Da Yadda Kasar Japan Ta Girke Makamai Masu Linzami A Kusa Da Yankin Taiwan November 25, 2025 Velayati: Alakar Iran da Iraki tana da karfi November 25, 2025 Arakci Ya Yi Gargadi Akan Abin Zai Biyo Bayan Keta Dokokin Duniya Da “Isra’ila” Take Yi A Cikin Wannan Yankin November 25, 2025 An Gudanar Da Jana’izar Shahidai 300 A Dai-Dai Ranar Shahadar Zahra (s) A Jiya Litinin November 25, 2025 Amurka Da HKI Sun Kawo Karshen Hukumar GHF Mai Raba Abinci A Gaza November 25, 2025 Babban Kwamandan Sojojin Sudan Ya Yi Watsi Da Shirin Trump Na Zaman Lafiya November 25, 2025 Hamas Ta Ce Keta Hurumin Tsagaita Wutan Da HKI Take Yi Zai Iya Kawo Karshen Tsagaita Wutar November 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci