MDD : ba tabbas kan ko za’a kawar da zazzabin malaria nan da shekarar 2030
Published: 25th, April 2025 GMT
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa ba tabbas ko za’a iya kawar da cutar zazzabin cizon sauro nan da shekarar 2030, musamman a nahiyar Afrika.
Fiye da mutane miliyan 263 ne suka kamu da cutar a cikin 2023, kuma kusan 600,000 ne suka mutu sanadin cutar a cewar alkalumman na MDD.
Musamman a wannan lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ya rage kashe kudaden tallafi na kasa da kasa, inji rahoton.
A cikin shekaru 25, zuba jari a yakin da ake yi da zazzabin cizon sauro ya hana kamuwa da cutar ga mutane biliyan 2 da kuma mutuwar mutane miliyan 13, musamman a Afirka.
“Akwai babbar barazana, da kuma bukatar jajircewa wajen samar da magunguna in ji Philippe Duneton, darektan Unitaid, kungiyar da ke da fafatuklar samar da magunguna na HIV, tarin fuka ko TB da kuma zazzabin cizon sauro.
Bayyanin ya fito ne gabanin zagayowar ranar duniya ta yaki da cutar zazzabin sauro yau 25 ga watan Afrilu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Jiragen Yakin Amurka Sun Kashe Mutane Da Dama A lardin Sa’ada Na Kasar Yemen
Mutane da dama daga nahiyar Afirka ne suke cikin mutane kimani 50 wadanda suka rasa rayukansu sanadiyyar hare-haren da jiragen yakin Amurka suka kai kan wani gidan kaso a lardin Sa’ada na kasar Yemen.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran Al-Masirah yana cewa makaman Amurka sun fada kan wani gidan yarin da aka kebewa yan Afrika, kuma yawansu ya kai 115, amma har yanzun ba’a san yawan wadanda suka rasa rayukansu a gidan yari.
Labarin ya kara da cewa har yanzun ma’aikatan agaji suna aikin ceto a wurin, sannan hotunan da suka fara bayyana sun nuna gawaki da dama. Amma Al-Masirah ta bayyana cewa akalla mutane 68 sun rasa rayukansu.