Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam Ta Amnesty International Ta Ce; Gwamnatin Mamayar Isra’ila Ba Ta Dace Da Bincike Laifukan Sojojinta Ba
Published: 21st, April 2025 GMT
Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Amnesty International ta bayyana cewa: Gwamnatin Mamayar Isra’ila ta tabbatar da cewa ba za a amince da ita ba a duk wani bincike laifukan sojojinta
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta tabbatar da cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta sake tabbatar da rashin sahihancinta wajen binciken laifukan da sojojinta suka aikata.
A yayin da take tsokaci kan binciken da gwamnatin mamayar Isra’ila ke yi kan harin da aka kaiwa ma’aikatan jinya a Gaza, kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta ce a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, 21 ga watan Afrilun wannan shekara ta 2025: Akwai zabi daya tilo na yin adalci, ta hanyar kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ko kuma kotun duniya.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta bukaci a gudanar da bincike kan wadanda ke da alhakin aikata laifukan da aka aikata cikin watanni 18 da suka gabata a Zirin Gaza.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Batun Ceto Wanda Ake Zargi Da Kwaya: Kwamishinan Kano Ya Yi Murabus
Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Ali Namadi, ya ajiye aikinsa bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi rahoton kwamitin bincike da ke duba rawar da ya taka a batun ceto wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu.
Wannan matakin na murabus ana kallonsa a matsayin wani muhimmin cigaba da ke nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen kare gaskiya, bayyana ta da kuma ɗaukar nauyin ayyukanta a bainar jama’a.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, Kwamishinan ya bayyana cewa ya yanke shawarar murabus ne duba da muhimmancin al’amuran da suka shafi jama’a da kuma halin da ake ciki.
Ya ce: “A matsayina na ɗaya daga cikin masu fada-a-ji a wannan gwamnati da ke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, ya dace na ɗauki wannan mataki, koda kuwa zai sosa zukata.
“Ko da yake ina ci gaba da musanta hannuna a lamarin, ba zan iya watsi da irin yadda jama’a ke kallon batun ba, da kuma bukatar kare ƙimar gwamnati da muka ginata tare.” In ji shi.
Alhaji Namadi ya nuna godiya ta musamman ga Gwamna Abba Kabir Yusuf saboda ba shi damar yi wa jiharsa hidima, tare da jaddada aniyarsa ta ci gaba da bin manufofin gwamnatin.
Ya ƙara da cewa: “A matsayina na ɗan ƙasa nagari, dole ne in ci gaba da kare amana da hangen nesan da muka haɗa kai wajen shimfiɗawa a jiharmu. Zan ci gaba da kasancewa mai biyayya ga akidun da suka kawo wannan gwamnati kan mulki.”
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi murabus ɗin cikin farin ciki, tare da yi masa fatan alheri a duk wani yunƙurinsa na gaba.
Gwamnan ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa wajen tabbatar da adalci, ladabi, da kuma yaki da miyagun dabi’u da laifukan da suka shafi kwayoyi da sauran matsalolin da ke shafan matasa da al’umma baki ɗaya.
Ya kuma ja hankalin duk masu rike da mukaman siyasa da su kasance masu hikima da taka-tsantsan wajen hulɗa da al’amuran jama’a, tare da neman izini daga hukumomi mafi girma kafin su shiga cikin wani lamari da ke da tasiri a bainar jama’a.
Abdullahi Jalaluddeen