Manchester Ta Kai Zagayen Semi Final A Europa Bayan Doke Lyon
Published: 18th, April 2025 GMT
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp.কীওয়ার্ড: Wasannin Europe
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu Ya Jaddada Goyon Bayan Gwamnatin Tarayya Ga Muhimman Tsare-Tsaren Kaduna.
Daga Abdullahi Shettima
Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya karɓi Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda suka tattauna kan manyan muhimman abubuwan ci gaban jihar musamman a fannoni na noma, ababen more rayuwa da tsaro.
A yayin ganawar, Gwamna Uba Sani ya bayyana godiyarsa ga Shugaban Ƙasa bisa goyon bayan da gwamnatin tarayya ke bai wa Jihar Kaduna, musamman wajen ci gaban harkokin noma da sarrafa amfanin gona. Ya ce kafa Special Agro-Industrial Processing Zone (SAPZ) da African Quality Assurance Centre (AQAC) ya ɗaga martabar jihar a matsayin jagora wajen ci gaban sarkar samar da kayayyakin noma da kuma faɗaɗa damar fitar da su ƙasashen waje. Shugaban Ƙasa ya yaba da wannan cigaba tare da tabbatar da cikakken goyon bayan gwamnatin tarayya.
Haka kuma, Gwamnan ya bayyana wa Shugaban Ƙasa ci gaba da aikin sabunta harkar sufuri a Kaduna, ciki har da aikin Light Rail da kuma tsarin Bus Rapid Transit (BRT) — wanda shi ne na biyu a Najeriya bayan na Legas. Shugaba Tinubu ya tabbatar da ci gaba da tallafi daga gwamnatin tarayya, tare da yabawa da irin hangen nesan Kaduna a bangaren gine-gine.
Shugaban Ƙasar ya kuma tabbatar da aniyar gwamnati wajen ƙarfafa zaman lafiya da tsaro a fadin Jihar Kaduna, tare da alkawarin gaggauta aikin gyara titin Abuja–Kaduna–Zaria–Kano. Ya jaddada cewa gwamnatin tarayya na aiki kafada da kafada da ajandar cigaban Jihar Kaduna domin samar da raya kasa mai fa’ida ga al’umma da inganta rayuwar ’yan ƙasa.
Karshe.