Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Yi Watsi Da Matsawa Sauran Kasashe Lamba
Published: 14th, April 2025 GMT
Game da batun cewa ministan tsaron Amurka da sauran manyan jami’ai sun wallafa maganganun dake yada ra’ayin wai “Sin ta kawo barazana”, Lin Jian ya ce, wasu maganganun jami’an bangaren Amurka suna cike da bambancin akida da tunanin yakin cacar baka, gaba daya karya ce.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare.
এছাড়াও পড়ুন:
An Bukaci An Bukaci Asusun JICHIMA Ya Fadada Hanyoyin Samun Kudade Baya Ga Gwamnatin Jigawa
Kwamatin harkokin lafiya na majalisar dokokin jihar Jigawa ya ce gyaran fuskar da aka yiwa dokar da ta kafa asusun adashen gata na kiwon lafiya na jihar ya sahalewa asusun damar samo kudade daga wasu bangarori da ba na gwamnati ba.
Shugaban kwamatin kuma wakilin mazabar Guri, Alhaji Usman Abdullahi Tura Musari, ya yi wannan tsokaci lokacin da ya jagoranci ‘yan kwamatin domin ziyarar aiki a ofishin asusun da ke Dutse.
Ya bayyana bukatar ganin asusun JICHIMA ya nemo kudade daga hannun masu taimakon al’umma da cibiyoyi da ‘yan siyasa da kwamitocin zakka da na waqafi domin bunkasa asusun, ta yadda zai biya bukatun kiwon lafiyar al’ummar jihar.
Alhaji Usman Musari ya lura cewar fadada hanyoyin samun kudade ga asusun JICHIMA fiye da abinda ake yanka daga albashin ma’aikata zai tabbatar da ingancin aiki da kuma dorewar asusun.
Daga nan sai Alhaji Usman Musari ya shawarci asusun JICHIMA da ya rubanya kokari wajen kafa ofishinsa a dukkan kananan hukumomin jihar 27 domin biyan bukatun wadanda su ka yi rijista da asusun.
A nasa jawabin, wakilin mazabar Gwiwa Alhaji Aminu Zakari ya yi kira ga asusun JICHMA da ya inganta ayyukan sa a dukkan asibitocin da aka yiwa rijista domin gudanar da ayyukan asusun kamar yadda doka ta tanadar.
Da ya ke mayar da jawabi, Shugaban Asusun Inshorarar Lafia na jihar Jigawan, Pharmacist Hamza Maigari Kakudi ya ce an kafa asusun ne da nufin kawar da nakasu wajen kiwon lafiyar jama’a ta hanyar tabbatar da cewar masu rauni a cikin al’umma sun samu kulawar da ta kamata.
Ya ce asusun yana shirin kaddamar da gangamin wayar da kan jama’a domin yin rijista ga masu karamin karfi 1000 a kowacce mazaba, domin cimma kudurin gwamnatin Malam Umar Namadi na kula da lafiyar jama’a.
A lokacin ziyaran, jami’an JICHIMA da kwamatin majalisar sun tattaunawa kan batun samar da ofis na dindindin ga asusun.
Usman Mohammed Zaria