’Yan bindiga sun kona masallacin Juma’a da asibiti da gidaje da Zamfara
Published: 13th, April 2025 GMT
’Yan bindiga sun kona masallacin Juma’a da asibiti da gidaje fiya da 10 a yankin Biyabiki da ke Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara.
’Yan ta’addan sun cinna kona wuraren ne bayan sallar Isha’i a ranar Asabar a wani da ake zargin na ramuwar gayya ne kan kashe Isuhu Yellow, kanin wani jagoran ’yan bindiga mai suna Adamu Aliero.
Shaida sun ce da misalin karfe 8 na dare ne ’yan bindigar da ake zargin yaran kasurgumin dan bindiga Adamu Aliero ne suka kai harin a kan babura, inda suka banka wa wuraren wuraren wuta, sannan suka tsere ba tare da taba mazauna ba.
“Wuraren da suka cinna wa wuta sun hada da masallacin Juma’a da wani karamin asibiti da kuma gidaje kimanin 10 da suka lalata,” in ji wani mazaunin garin da ya nemi a boye sunansa.
A daina cutar ’yan Najeriya ta hanyar rabon kayan tallafi ’Yan adawa sun zama kyanwar Lami duk da rinjayensu a MajalisaAna kyatuta zaton harin na da alaka da kashe Adamu Yelow a wani harin kwanton bauna da shi da tawagarsa suka kai wa jami’an tsaro, a yankin Keta, kimanin makonni uku da suka gabata, amma jami’an tsaron suka aika su lahira.
Tun da farko a ranar sai da ’yan ta’addan sun kuma kai wani hari a kauyen Tsageru a ranar, inda suka kona gidaje da dama.
Wani mazaunin yankin ya ce, “Ba mu san wace butaka suke neman cim ma da kona gidaje da kayan gwamnati da suke yi ba; Tun da aka kashe Isuhu Yellow yankunanmu ke ta fuskantar barazana, don haka muna kyatata zaton wanna harin ramuwar gayya ce.”
Wakilinmu ya yi kokarin tattaunawa da kakakin ’yan sanda na Jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar, domin samun karin bayani, amma hakarsa ba ta cimma ruwa ba, bayan ya yi ta kiran wayar jami’in.
Wannan hari na kara nuna alamr ci gaban matsalar tsao a Jihar Zamfara inda ’yan bindiga ke kara cin karensu a yankunan karkara, duk kuwa da kokarin hukumomin tsaro na yi wa tufkar hanci a yankin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga yan ta adda hari Zamfara yan bindiga Yan bindiga
এছাড়াও পড়ুন:
Xi Ya Yi Kira Ga Mazauna Wani Kauye Dake Xizang Da Su Rike ‘Yan Uwantakar Kabila
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira ga mazauna wani kauyen dake yankin Nyingchi na jihar Xizang mai cin gashin kai, da su rungumi akidar ‘yan uwantakar kabilarsu, da samar da yanayin gudanar da rayuwa mai kyau.
Shugaba Xi ya yi kiran ne cikin wasikar da ya mayar ga mazauna kauyen, wadda a ciki ya bayyana fatansa gare su, bayan da ya ziyarci kauyen cikin watan Yulin shekarar 2021. Ya ce, bayan fahimtar cewa kauyen ya samu sabbin sauye-sauye a shekarun baya-bayan nan, kuma mazaunansa sun samu karin kudaden shiga, ya yi matukar farin ciki.
Shugaba Xi ya kara da cewa, yana fatan karkashin manufofin JKS, mazauna kauyen za su gina yankunan kan iyakoki, tare da kyautata rayuwar al’ummunsu yadda ya kamata, kana za su zage damtse wajen kare kyakkyawan yanayin tuddan yankin, da raya sunan kauyen ta fuskar yawon bude ido, da bayar da gudummawa ga gina yankin kan iyaka mai wadata da daidaito.
Kauyen dai ya shahara sosai a fannin noman itacen Peach. A shekarun baya-bayan nan, ya cimma sabbin nasarori a fannin bunkasa sha’anin yawon bude ido na kauyuka, da karfafa sassan tattalin arziki, da ingiza ‘yan uwantakar kabila. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp