Aminiya:
2025-12-12@20:52:43 GMT

Fashewar bam a mota ta kashe mutum takwas a Borno

Published: 12th, April 2025 GMT

Wani abin takaici ya sake afkuwa a kan hanyar Maiduguri zuwa Damboa a Jihar Borno mai cike da tashin hankali, yayin da wani bam ya tarwatse a safiyar Asabar da rana, inda aƙalla mutane takwas ne suka mutu.

Wasu shaidun gani da ido na nuni da cewa fashewar bam ɗin da ake kyautata zaton mayaƙan Boko ne suka dasa shi ya tarwatsa wata motar bas ƙirar Toyota “Hummer Bus” da ke ɗauke da fasinjoji zuwa Maiduguri babban birnin Jihar Borno.

An kashe Uba da ’ya’yansa biyu a ƙauyen Filato An kama mutum 8 kan faɗan daba a Kano

Wata majiya mai tushe da aka zanta da ita, ta tabbatar da cewa aƙalla mutane bakwai da suka haɗa da direban motar ne ake fargabar sun mutu a wannan mummunan fashewar.

Titin Maiduguri zuwa Damboa ya kasance muhimmiyar hanyar mota da ta haɗa birnin Maiduguri zuwa ƙaramar hukumar Damboa da sauran al’ummomin kudancin Borno wadda a kullum ake fargabar bin ta lura da cewar tana gab da dajin Sambisa.

Don haka wannan lamari na baya-bayan nan ya zama babban abin tunatarwa game da barazanar tsaro da ke fuskantar matafiya da ke bin wannan hanya mai muhimmanci.

Har yanzu dai hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba, har ya zuwa lokacin kammala wannan rahoto.

To sai dai kuma babu shakka wannan harin zai ƙara dagula al’amura game da lafiyar masu tafiye-tafiye da sufuri a yankin da kuma yankin da ake da ’yan tada ƙayar baya a yankin Arewa maso Gabas.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji sun kashe ’yan bindiga 3 a Binuwai

Dakarun Sojin Operation Whirl Stroke (OPWS), sun kashe wasu mutum uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, yayin wani samame da suka kai a Ƙaramar Hukumar Ukum, a Jihar Binuwai.

Mai magana da yawun OPWS, Laftanar Ahmad Zubairu, ya ce sojojin sun samu bayanan sirri kuma suka yi aiki tare da ’yan sandan Zaki-Biam.

Kotun Koli ta soke afuwar da Tinubu ya yi wa Maryam Sanda Dan sanda ya yi batan dabo a bakin aikinsa a Katsina

Maharan sun kafa shinge a kan hanyar Aturuku–Wembe–Ayati, inda suke tare matafiya suna ƙwace musu kayayyaki.

Da sojoji suka isa wajen, maharan sai suka fara harbe-harbe, wanda hakan ya sa sojojin suka buɗe musu wuta.

Hakan ya yi sanadin mutuwar uku daga cikinsu, sauran kuma suka tsere cikin daji.

Dakarun sun ƙwato babura guda biyu, yayin da suka ci gaba da farautar waɗanda suka tsere.

Bincike ya nuna cewa mutanen da suka mutu suna cikin wata ƙungiya da ta daɗe tana yi wa al’umma barazana ta hanyar garkuwa da mutane da kai hare-hare, musamman kusa da kasuwar doyar Zaki-Biam.

Mutanen gari sun tabbatar da sunan waɗanda dakarun suka kashe.

Kwamandan OPWS, Manjo-Janar Moses Gara, ya yaba wa sojojin bisa ƙwazo da jarumtarsu, tare da alƙawarin ci gaba da kare al’umma da tabbatar da zaman lafiya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 2, sun ƙwato makamai a Borno
  • Sojoji sun kashe ’yan bindiga 3 a Binuwai
  • Yadda APC Da ADC Ke Amfana Da Rikicin Jam’iyyar PDP
  • Kotu Ta Yanke Wa Wani Mutum Hukuncin Kisa Bisa Garkuwa Da Kashe Mai Gidansa A Kano
  •  Turkiya A Shirye Take Ta Aike Da Sojoji Zuwa Yankin Gaza
  • An kai hari gidan jami’in ɗan sanda a Yobe
  • Zanga-zanga ta ɓarke bayan haɗarin tirela ta kashe mutum a Yobe
  • Zanga-zanga ta ɓarke kan zargin sojoji da kashe mata a Adamawa
  • Sakkwatawa na murnar kisan da sojoji suka yi wa mataimakin Bello Turji
  • DAGA LARABA: Ko Ziyarar Tawagar Amurka Za Ta Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya?