Ministan ya ce maganar da ya faɗa da farko wadda ba a ruwaito ta a daidai ba ita ce:

“E, lallai an samu cigaba a harkar tsaro a sassa daban-daban na ƙasar nan, ko da yake ba a kawar da duk wani aikin tashin hankali gaba ɗaya ba.

“Hukumomin tsaro suna aiki ba dare ba rana don tabbatar da cewa an shawo kan matsalolin da ake da su a wasu sassan Jihar Borno da wasu wurare.

“Haɗin gwiwar da muke gani tsakanin hukumomin tsaro, musamman a shekaru biyu da suka wuce, da kuma gagarumin zuba jari a kayan aiki da na’urorin zamani da ake yi, yana nuna yadda Gwamnatin Tarayya take ɗaukar batun tsaro da matuƙar muhimmanci.

“Gwamnatin Tinubu tana da ƙwarin gwiwar kawar da ayyukan ‘yan bindiga da ta’addanci a faɗin ƙasar.

“Nasarorin da hukumomin tsaro suka samu a cikin watanni 18 da suka wuce suna nuna cewa lallai Nijeriya tana komawa daidai a hankali a hankali.

“Gwamnati tana kira ga kowa da kowa, musamman gwamnatocin jihohi, da su haɗa hannu wajen kawar da ragowar ‘yan ta’adda da masu aikata laifuka a duk inda suke.”

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji sun daƙile harin ’yan ta’adda a Borno

Dakarun Sojin Operation HADIN KAI sun daƙile wani hari da ’yan ta’addan ISWAP suka kai sansanin soji na Mairari da ke Jihar Borno.

Harin ya fara ne daga daren ranar Juma’a zuwa safiyar Asabar.

’Yan sanda sun ba da tabbacin isasshen tsaro a zaɓen ƙananan hukumomin Borno Kotu ta sa ranar yanke hukunci a Shari’ar Abba Kyari da NDLEA

A cewar rundunar, ’yan ta’addan sun yi ƙoƙarin shiga sansanin ta hanyar amfani da motoci biyu da suka cika su maƙil abubuwan fashewa.

Jami’in yaɗa labarai na Operation HADIN KAI, Laftanar Kanal Sani Uba, ya ce sojoji sun gano motocin kuma suka tarwatsa su kafin su kai ga shiga sansanin.

Rahotanni sun nuna cewa an kashe ’yan ta’adda da dama, yayin da wasu suka jikkata.

Waɗanda suka tsira sun kwashe gawarwaki da waɗanda suka ji rauni a wajen bayan tafka artabu.

Bayan daƙile harin, sojoji tare da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro, sun gudanar da bincike a yankin.

A yayin binciken, sun gano gawar ’yan ta’adda tare da ƙwato makamai da kayayyaki da dama da suka bari.

Kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da bindigogi, harsasai, gurneti, babura, na’urorin sadarwa, kayan yaƙi, da kayayyakin jinya.

Laftanar Kanal Uba, ya ce ƙwato waɗannan kayayyaki ya rage ƙarfin ’yan ta’addan da ikonsu na ci gaba da kai hare-hare a yankin.

Ya ƙara da cewa dakarun sun lalata motocin da aka maƙare da kayan fashewa, wanda ya jawo lalacewar wasu wurare biyu, amma ba su yi nasarar shiga sansanin sojin ba.

Ya ce a halin yanzu sojoji na ci gaba da yin sintiri domin hana sake kai hare-hare tare da bai wa al’ummar yankin tabbacin tsaro.

Rundunar sojin ta jaddada ƙudirinta na kawar da ’yan ta’adda tare da dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Arewa maso Gabas.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tsaro: Abba ya kafa runduna ta musamman da za ta ke tsaron tashoshin mota a Kano
  • An kashe mai ciki da ɗanta a Kano
  • Taɓarɓarewar rashin tsaro ya nuna rashin shugabanci na gari — Obi
  • Sojoji sun daƙile harin ’yan ta’adda a Borno
  • ’Yan sanda sun ba da tabbacin isasshen tsaro a zaɓen ƙananan hukumomin Borno
  • Kungiyar NLC A Najeriya Ta Shirya Zanga-Zanga Kan Matsalar Rashin Tsaro A Fadin Kasa
  • Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 2, sun ƙwato makamai a Borno
  • Tinubu Ya Yaba Wa Jami’an Tsaro Kan Ceto Dalibai 100 Da Aka Sace A Neja
  • NLC Ta Shirya Zanga-Zangar Rashin Tsaro A Faɗin Ƙasa Ranar 17 Ga Disamba
  • ‘Sojojin Najeriya da na Ivory Coast 200 sun shiga domin tsaftace Jamhuriyar Benin’