Hisbah ta warware rigingimu 565 da lalata katan 51 na barasa a Yobe
Published: 10th, April 2025 GMT
Hukumar Hisbah ta Jihar Yobe ta ce, ta warware rigingimu 565 a cikin watanni 12 da suka gabata a jihar.
Wannan hukuma dai gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ne ya kafa ta a watan Maris, 2024 a wani ɓangare na ƙoƙarin magance munanan ɗabi’u a jihar.
Trust Radio 92.7FM za ta fara shirye-shiryen gwaji An kama masu garkuwa da mutane biyu a YobeShugaban Hukumar ta Hisbah, Dakta Yahuza Hamza Abubakar, ya ce matsalolin da aka warware sun haɗa da batutuwan da suka shafi: Harkar iyali da kasuwanci da gado da kuma basussuka.
Sauran matsalolin da hukumar ta Hisbah ke warwarewa sun haɗa da: Matsalolin da haddasa rikicin manoma da makiyaya da kuma rashin biyan kuɗin haya.
A cewarsa, an warware akasarin shari’ar ta hanyar sulhu da fahimtar juna.
Dokta Hamza ya ce, jami’an hukumar sun kuma ƙwace kwalayen barasa guda 56 da kuma 18 na sinadaran fosters na methylene chloride chemical (Madarar Sukurdai) a faɗin jihar.
Ya ce, addinin Musulunci da dokar da ta kafa hukumar a shekarar 2024 ta haramta sayar da barasa da sauran kayan maye a jihar.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara Ta Taya Oluremi Tinubu Murnar Nadin Sarauta a Ile-Ife
Daga Aminu Dalhatu
Uwargidar Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta taya Uwargidar Shugaban Kasa, Sanata Oluremi Tinubu, murna bisa nadin ta a matsayin Yeye Asiwaju Gbogbo Ile Oodua a Ile-Ife na Jihar Osun.
Nadin ya kasance wani bangare na bukukuwan cikar shekaru 10 na Mai Martaba Ooni Adeyeye Enitan Ogunwusi Ojaja II akan karagar mulki na Ooni Ife, wanda ya jawo sarakunan gargajiya, manyan jami’an gwamnati da fitattun mutane daga sassan kasar nan.
A wata sanarwa da sakatariyar yada Labarai ta Uwargidar Gwamnan, Rabi Yusuf, ta fitar, ta bayyana karramawar da aka yi wa Sanata Oluremi a matsayin abin yabawa, inda ta ce karramawar ta yi daidai da jajircewarta wajen ci gaban kasa, tallafawa mata, da kuma gudummawarta wajen karfafa iyalai da al’umma ta hanyar aikace-aikacen jin kai da manufofin raya al’umma.
Ta kuma yaba wa Ooni na Ife bisa zabar Sanata Oluremi Tinubu domin wannan girmamawa, tana mai cewa wannan zabe ya nuna irin jagoranci, tasiri da dogon lokacin da ta shafe tana hidima ga kasa.
A cewar Hajiya Huriyya, wannan zabe ya nuna rawar da masarautu ke takawa wajen gane karrama wadanda suka yi wa al’umma hidima.
Bikin ya nuna al’adun Yarbawa da kuma muhimmancin gudunmawar da masarautu ke bayarwa wajen gina hadin kan kasa.
Manyan shugabannin gargajiya da suka halarci bikin sun hada da Sarkin Musulmi, Olu na Warri, da Soun na Ogbomoso, da sauransu, wadanda suka hadu domin bikin cikar Ooni shekaru 10 a kan karaga da kuma nadin Sanata Oluremi Tinubu.