Najeriya: An gudanar da zanga-zangar adawa da wasu shirye-shiryen gwamnati
Published: 8th, April 2025 GMT
An gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wada ta barke a wasu manyan biranen Nijeriya da suka haɗa da Abuja da Legas da kuma Fatakwal.
Zanga-zangar wadda wata kungiyar gwagwarmaya ta Take It Back ta shirya na gudana ne duk da gargadin da ’yan sanda suka yi na neman a jingine ta.
A Abuja, babban birnin Nijeriya, fitaccen dan gwagwarmaya, Omoyele Sowore da lauyan nan mai kare hakkin bil Adama, Deji Adeyanju ne ke jagorantar zanga-zangar duk da yunkurin ’yan sanda na hana su rawar gaban hantsi
An kuma hangi masu zanga-zangar ɗauke da alluna da kwalaye masu dauke da rubutun bayyana buƙatunsu a wasu hanyoyi da ke Ikeja, babban birnin Jihar Legas.
A Jihar Ribas kuma, masu zanga-zangar sun yi dandazo a filin Isaac Boro da ke birnin Fatakwal, amma dai ’yan sanda sun rika harba musu barkonon tsohuwa domin daƙile manufar da suka fito ita.
Kungiyar ta Take It Back na cewa babu gudu babu ja da baya domin nuna adawa da dokar ta-baci da aka sanya a Jihar Ribas da kuma abin da ta kira cin zarafin bil’adama da kuma amfani da dokar ta’addancin yanar gizo ba bisa ka’ida ba.
Wannan dai na zuwa ne a yayin da rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta gargaɗi masu shirin zanga-zangar a ranar Litinin 7 ga watan Afrilu a faɗin kasar su sake tunani domin a ranar ce ‘yan sandan kasar suke bukukuwa domin nuna gudunmawar da suka bayar don ci-gaban Nijeriya.
Rundunar ta ce zanga-zangar tana zuwa ne a lokacin da bai dace a yi zanga-zanga a kasar ba.
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan kasar, Olumuyiwa Adejobi, ya fitar ta ce rundunar ba ta adawa da ‘yancin ‘yan kasar na taruwa da yin gangami da Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya ba su.
Sai dai kuma sanarwar ta ce rundunar na fargaba game da burin wadanda suka shirya yin zanga-zangar rana daya da ranar da aka ware domin yaba wa irin jajircewa da sadaukar da kai na ‘yan sandan Nijeriya.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: zanga zangar
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin Sin Sun Bi Sahun Shiga Ayyukan Ba Da Agajin Ambaliyar Ruwa
Rundunar sojojin ‘yantar da jama’ar kasar Sin, da rundunar ‘yan sandan kasar masu dauke da makamai, da dakarun sa-kai na cikin gida sun aike da dakaru domin shiga ayyukan ba da agajin gaggawa a yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa a kasar Sin.
A baya-bayan nan ne aka tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya a gabashi, da arewaci, da arewa maso gabas na kasar Sin, lamarin da ya haddasa ambaliya da sauran ibtila’i na zaftarewar kasa da suka yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi.
Rundunar ‘yan sanda masu dauke da makamai ta birnin Beijing ta aike da jami’ai da sojoji sama da 2,000 don taimaka wa ayyukan ba da agajin, inda aka kwashe sama da mazauna yankin da abin ya shafa 4,100 tare da kai akwatunan kayayyakin agaji fiye da 3,000 da tsakar ranar yau Talata. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp