2025-11-08@22:20:17 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4169
«azumin ranar»:
BBC Hausa ta yi nazari kan kasashen Afirka da dakarun Amurka suka shiga da sunan dakile wata matsala kamar annoba ko kuma yakar “‘yan ta’adda”. Somalia (1992–1994) Kasar Somalia ta kasance daya daga cikin wuraren da Amurka ta aika da sojojinta a wani mataki mafi girma a farkon shekarun 1990s. A lokacin da kasar ke cikin rikicin yakin basasa da yunwa mai tsanani, Amurka ta tura sojoji don tallafawa da jigilar kayan agaji da tabbatar da zaman lafiya. Wannan ya haifar da sanannen yakin Mogadishu da ake kira “Battle of Mogadishu” a 1993, wanda ya jawo hankalin duniya kan irin kalubalen da ke tattare da tsoma bakin soja a rikicin cikin gida. Amurka ta kaddamar da harehare na jiragen...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin November 8, 2025 Daga Birnin Sin CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin November 8, 2025 Daga Birnin Sin Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong November 8, 2025
Rahotanni sun nuna cewa dan wasan Taekwando na kasar Iran mai suna Abulfazl zandi ya zamo shi ne na daya a duniya a bangaren maza a ma’aunin kilograme 58, bayan yayi nasarar samun lambar yabo ta zinariya a gasar taekwando ta duniya a kasar China, Hukumar kula da wasan taekwando ta duniya ta fitar da sunayen wadanda suka yi fice a duniya a watan nuwamba, inda ta sanya gasar teakwando ta duniya da aka yi a kasar china , yan wasan kasar Iran da dama maza da mata sun samu gagarumin ci gaba a jerin fannonii daban daban na wasanni. Zandi ya zo na daya a duniya da maki 170.80 kuma yana mataki na 4 a bangaren Olympic, A gefe...
Prime ministan kasar Iraki shiya Al-sudani ya sanar a birnin bagadaza cewa sun fara shirin kula wata yarjejeniya a hukumace da kasar Amurka, da zai kai ga ficewar sojojin kasashen waje daka kasar, daga nan zuwa wata satumbar shekara ta 2026, wanda wannan wata ishara ce ta bude wani sabon shafi a kasar na zaman tabbaci da tsaro mai dorewa. Kasar iraki na kokari wajen ganin an kawo karshen zaman sojojin mamayar Amurka dake kasar fiye da shekaru 20 da kuma tsoma bakin kasashen wajen, da ya fara daga lokacin da Washington ta shiga kasar a shekara ta 2003 domin kaddamar da hare-hare da dukkan duniya ta yi tir da shi da kuma bayyana shi a matsayin wanda ya sabama...
Rahotanni sun bayyana cewa a kasar Turkiya an fitar da hukumci kama prime ministan Isra’ila banjamin Natanyaho da wasu jami’an Isra’ila guda 37 da laifin keta hakkin bil adama da kuma yin kisan kare dangi kan alummar Gaza a lokacin yaki, Wannan yana nuna irin mataki mai tsauri na doka da aka dauka kan jami’an Isra’ila a baya bayan nan, kan laifuka yaki da suka tafka kan bil adam a yakin Gaza, da kuma karfafa kasashen duniya daukar matakin da ya dace kan zargin da ake mata na kai hare-haren kan fararen hula. Sabanin tsakanin Ankara da tel aviv ya kara tsananta ne tun bayan da ta fara kai hare-haren kan fararen hula a yankin gaza a shekara ta 2023...
Uwargidan Gwamnan Jihar Gombe, Hajiya Asma’u Muhammadu Inuwa Yahaya, ta jagoranci wani yunƙuri na ganin an tsawaita hutun haihuwa na mata ma’aikata daga watanni uku zuwa shida. Ta jagoranci manyan jami’an lafiya zuwa majalisar dokokin jihar domin neman goyon bayan doka kan wannan shiri. Barau ya nemi Trump ya janye kalamansa, ya nemi afuwar Najeriya Matsalar Tsaro: Mun samu gagarumin ci gaba a shekaru biyu — Tinubu A yayin taron wayar da kai a majalisar, Hajiya Asma’u ta bayyana cewa shayar da jarirai nono har watanni shida yana da matuƙar amfani wajen rage mace-macen jarirai, inganta garkuwar jikinsu, da bunƙasa ƙwaƙwalwarsu. Uwargidan ta roƙi majalisar, ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Abubakar Mohammed Luggerewo, da su samar da doka da za ta...
Ya ƙara da cewax gwamnatinsa ta fara gyara daga tushe, inda ilimi ya zama ginshiƙin farko. “Shekaru takwas kafin mu hau mulki, ɗalibanmu ba su samun takardun WAEC, sannan tsawon shekaru biyu suna fama da matsalar NECO. Na biya Naira Biliyan huɗu don magance wannan matsala,” inji shi. Gwamnan ya bayyana irin matsalolin da ya gada, yana mai cewa: “Na samu asusun gwamnati da naira miliyan huɗu kacal. Ma’aikata suna karɓar albashi cikin rashin tabbas, babu ruwa, asibitoci kuwa suna cikin mummunan yanayi.” Lawal ya ce, ya sake fasalin tsarin gwamnati, inda ya rage yawan kwamishinoni da manyan sakatarorin don rage ɓarna da ƙara inganci. “Yanzu muna daga cikin jihohi mafi ci gaba wajen tara haraji, inda kuɗaɗen...
Kotun koli ta tarayyar Najeriya ta tsayar da ranar 20 ga watan nan na Nuwamba domin zama shari’ar shugaban kungiyar ‘yan awaren Biafara Nnamdi Kanu. Zaman shari’ar da za a yi zai mayar da hankali akan tuhumar ayyukan ta’addanci da ake zargin shugaban kungiyar ‘yan awaren Biafara din da aikatawa. An bai wa Kanu kwanaki shida a jere domin ya kare kansa akan zargin ta’addancin, sai dai bai iya yin hakan ba. A jiya Juma’a Kanu ya gabatar da nashi bayanin akan cewa; Ai daina daukar ta’addanci a matsayin laifi a Najeriya, domin an yi wata sabuwar dokar da ta maye gurbin tsohuwar da ake da ita akan hakan. Har ila yau Kanu ya ce babu wata madogara ta doka...
Ministan harkokin wajen kasar Ukraine ne ya bayyana cewa da akwai ‘yan asalin kasashen Afirka 1,400 da suke cikin rundunonin Rasha suna tayata yaki. Ministan harkokin wajen kasar ta Ukraine, Adriy Sabiha ya ce; Moscow tana jan hankalin ‘yan Afirka akan su rattaba hannu akan wata yarjejniyar aiki, wacce take daidai da yankewa kansu hukuncin kisa. Har ila yau, ministan harkokin wajen kasar na Ukraine, ya rubuta a shafinsa na X cewa; ‘yan kasashen wajen da ake dauka a cikin sojojin Rasha, ana aike su zuwa inda za a yi saurin kashe su.” Jami’an gwamnatin kasar ta Ukraine sun sha yin kira ga gwamnatocin kasashen Afirka da su hana ‘yan kasarsu yi wa Rasha aikin soja da hakan yake da...
A yau Asabar ne jirgin kasa na dakon kaya na farko daga Rasha ya iso tashar jiragen ruwa ta “Abrin” na Iran. Zuwan jigin kasan dai yana a karkashin bunkasa alakar kasuwanci ne a tsakanin Iran da Rasha. Jirgin kasan yana dauke ne da hajar kasuwanci saboda kasuwannin Iran da kuma Iraki, yana kuma dauke da kwantena 62 masu girman kafa 40. Shi dai wannan jirgin kasan ya taso ne daga wani yanki mai nisan kilo mita 900 daga Arewacin birnin Moscow, ya kuma ratsa ta kasashen Kazakhstan da Turkmenistan, sannan ya shigo Iran. Kwanaki 12 jirgin ya dauka akan hanya kafin a karshe ya yada zango a cikin Iran. Gabanin tashin jirgin, sai an cimma yarjeniya da kasashen da...
Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta bayar da labarin cewa; Da safiyar yau Asabar ne jiragen yakin HKI su ka kai hari a garin Bint Jubail dake kudancin kasar. Harin na jiragen Sahayoniya dai ya kasance ne a kusa da aibitin Salah-Gandur da hakan ya yi sanadin jikkatar wasu mutane biyu. Wasu yankunan da jiragen sama marasa matuki na Haramtacciyar Kasar Isra’ila su ka kai wa hare-hare sun hada Jan’am dake gababsin Shaba’a, da Rashiyal-Wadi. Sai kuma kusa da garin Balida. A jiya Juma’a ma dai ‘yan sahayoniyar sun kai wasu hare-haren a kudancin Lebanon da su ka hada da Jabalus-Salihin,da Sahalul-Kiyam, sai Tallatul-Hamamis. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin ‘yan sahayoniyya ita ce babbar tushen rashin zaman lafiya a yankin Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi, yayin da yake magana kan kalaman Fira Ministan gwamnatin ‘yan sahayoniyya ya ce: “Gwamnatin Yahudawan Sahayoniyya ita ce babbar tushen rashin zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.” A shafinsa na Twitter, Araqchi ya rubuta cewa: Wannan abin da ake kira “tushen tsaro a Gabas ta Tsakiya” ana nemansa ne saboda kisan kare dangi da laifukan yaƙi. Yana sanya tsarin wariyar al’umma ga Falasdinawa miliyan 7.5, ya jefa bama-bamai a ƙasashe bakwai a bara, kuma ya mamaye yankunan Falasdinawa, Lebanon, da Siriya. Ya ƙara da cewa: “Gwamnatin ‘yan sahayoniyya tan zama ita ce babbar...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: A bayyane yake cewa Amurka tana da hannu dumu-dumu wajen wuce gona da iri kan kasar Iran Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ismail Baqa’i ya mayar da martani ga amincewar da shugaban Amurka ya yi na daukar alhakin harin da sojojin Sahayoniyya suka kai wa Iran, yana mai cewa: “Tun daga farko a bayyane yake cewa Amurka tana da hannu a harin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai wa al’ummar Iran.” Baqa’i ya rubuta a shafinsa na X-Platform: “Shin kuna tuna cewa Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya sanar a ranar 13 ga watan Yunin shekara ta 2025 cewa: Amurka ba ta da hannu a harin da ‘yan Sahayoniyya suka...
Kasashen Mexico da Iran sun yi watsi da zarge-zargen da ake yi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ofishin jakadancin Iran da ke Mexico ya yi watsi da “iƙirarin da Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi game da wargaza wani makircin da Iran ta shirya na kashe jakadan Isra’ila a Mexico.” A cikin wata sanarwa, ofishin jakadancin Iran ya bayyana zarge-zargen a matsayin “ƙirƙirar kafofin watsa labarai da kuma ƙarya bayyananna da nufin lalata dangantakar abokantaka da tarihi tsakanin ƙasashen biyu (Mexico da Iran),” yana mai jaddada kin amincewa da ikirarin tare da bayyana shi a matsayin makircin makiya a fili. A nata ɓangaren, hukumomin Mexico sun fitar da wata sanarwa suna cewa: “Ba su da wani rahoto game da...
A cewar ‘yansanda, “A ranar 10/10/25, an gayyato wani Mista Oke Emmanuel, dan NYSC kuma abokin dakin wanda ya bace, domin yi masa tambayoyi. Ya tabbatar cewa wanda ake nema ya kasance tare da iyalan George har zuwa 06/10/25. “An samu karin bayani daga George cewa dan NYSC din ya koka da rashin lafiya, aka kai su Asibitin Kaiama Referral Hospital a ranar 04/10/25, kuma aka sallame shi ranar 05/10/25. Sai dai a ranar 06/10/25, dan NYSC din ya bace zuwa wani wurin da ba a sani ba.” ‘Yansanda kuma suna binciken zargin karbar kudin rashawa na Naira 100,000 daga iyayen wanda ya bace, da wasu fursunoni biyu da ke gidan gyaran hali na Igbara, Abeokuta, Jihar Ogun, wadanda suka...
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi tsokaci kan yadda bangaren shari’a na Turkiyya ya bayar da sammacin kama Netanyahu fira ministan Isra’ila Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yaba da fitar da sammacin neman kama jami’an haramtacciyar kasar Isra’ila 37, ciki har da shugaban gwamnatin mamayar, Netanyahu mai aikata laifukan yaki, da ministocin tsaro Gallant da Katz. A cikin wata sanarwa da ta fitar a daren Juma’a, kungiyar ta ce wannan matakin “ya tabbatar da matsayin al’ummar Turkiyya da shugabancinsu, wadanda suka jajirce kan kyawawan dabi’un adalci da dan Adam, da kuma ‘yan uwantaka da ke tsakaninsu da al’ummar Falasdinawa da ake zalunta.” Kungiyar Hamas ta jaddada cewa: “Al’ummar Falasdinawa na ci gaba da fuskantar mummunan yakin kawar da...
Tarayyar Afirka Ta Yi Kiran Da A Girmama ‘Yancin Kai Na Najeriya Da Rashin Tsoma Baki A Harkokin Gidanta
Tarayyar Afirka ta yi kira da a girmama ‘yancin kai na tarayyar Najeriya kuma ta yi watsi da barazanar Trump Kwamitin Tarayyar Afirka ya bayyana damuwarsa game da kalaman da Amurka ta yi kwanan nan game da zargin gwamnatin Najeriya da hannu a kisan Kiristoci da kuma nuna alamun yiwuwar shiga tsakani na soja a karkashin hujjar “kare ‘yancin addini.” A cikin wata sanarwa a hukumance, wacce Al Jazeera ta samu kwafinta, Kwamitin ya jaddada jajircewarsa ga ka’idojin ‘yancin kai, rashin tsoma baki, ‘yancin addini, da kuma bin doka, kamar yadda aka tsara a cikin Dokar Tsarin Mulki ta Tarayyar Afirka da sauran kayan aikin da suka shafi hakan. Sanarwar ta tabbatar da cewa: Tarayyar Najeriya kasa ce mai muhimmanci...
Daga Usman Muhammad Zaria Gidauniyar Tunawa da Marigayi Sir Ahmadu Bello (ABMF) ta yaba wa Gwamna Umar Namadi bisa sauƙin kai, tawali’u da jajircewarsa wajen ci gaban Jihar Jigawa. Shugaban Kwamitin Amintattu na Gidauniyar kuma tsohon Gwamnan Jihar Neja, Dr. Mu’azu Babangida Aliyu ne ya yi wannan yabon yayin da ya jagoranci tawaga zuwa gaisuwar ban girma a fadar gwamnatin jihar da ke Dutse. Ya ce salon jagoranci na Gwamna Namadi na ɗauke da ƙima da marigayi Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato, ya shahara da su, musamman tsari, girmama jama’a da shugabanci na gaskiya da rikon amana. Dr. Aliyu ya yi kira ga shugabannin Arewa su rungumi jagoranci da ke maida hankali kan al’umma, tare da fifita ilimi a...
An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka
A nata tsokacin kuwa, kwamishiniya mai lura da ababen more rayuwa da makamashi a hukumar zartarwar kungiyar AU Lerato Dorothy Mataboge, kara tabbatar da alaka ta yi tsakanin hadin gwiwar Sin da Afirka, da burin da ake da shi na bunkasa masana’antu a sassan nahiyar. Mataboge ta kara da cewa, yunkurin bunkasa samar da masana’antu a Afirka na bukatar karfafawa ta hanyar gina kwarewa, da horar da sana’o’i, da samar da cibiyoyi da albarkatun al’umma, don haka ta yi kira da a hada karfi-da-karfe wajen tsara shirye-shiryen bunkasa sanin makamar aiki a cikin gida, da samar da cibiyoyin horo masu nagarta, don horar da jama’a fasahohin amfani da makamashi marar gurbata yanayi. (Saminu Alhassan) ShareTweetSendShare MASU ALAKA ...
Wanda ya jagoranci sallar juma’a a birni Tehran Hujjatul-Islami Wal Muslimin Muhammad Hassa Abu Turabi Fard, ya bayyana cewa; Tsayin dakar da kungiyar Hizbullah ta Lebabon da Ansurllah na kasar Yemn da kuma al’ummar Iran su ka yi wajen fada da masu girman kai na duniya, sakamako ne na koyarwar alkur’ani maigirma, Ahlul Bayt ( a.s) da kuma Ashura da jagorar matan duniya Fatima az-Zahra ( a.s). Kamfanin dillancin labarun “Mehr” ya ambato limamin na birnin Tehran yana kuma cewa; Makarantar gwgawarmaya tana yi wa zuriya bayan zuriya tarbiyya akan riko da gaskiya da kuma kalubalantar masu danniya. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name*...
Jami’i a Asusun yara na MDD y ace; Daga watan Oktoba na 2023 zuwa yanzu Yahudawa ‘yan share wuri zauna da sojojin HKI sun kashe kananan yaran Falasinawa 47,tare da yin gargadi akan hatsari dake tattare da hakan. Manaja mai kula da yanayi na musamman a karkashin Asusun kananan yaran da MDD Recardo Peres ya ce; “Yan share wuri zauna da sojojin HKI sun kashe Kananan yaran Falasdinawa 47 a yammacin kogin Jordan da birnin Kudus tun daga watan Oktoba na 2023. Haka nan kuma ya ce; Bayan abinda ya faru na barnar yakin tsawon shekaru biyu a Gaza, da tsagaita wutar da ake ketawa da kuma kashe yara a cikin sa’o’i kadan da su ka gabata, bai kamata a...
Tarayyar turai ta bayyana cewa ma’aikatan Agaji ba za su iya isha cikin garin Al-fahar ba,kuma birnin ya zama tamkar makabarta. Tarayyar turai din ta bakin mai Magana da yawunta Eva Herneserova ta kuma ce; Sudan ta zama daya daga cikin kasashen da gudanar da ayyukan agaji ya tsananta a duniya,kuma har yanzu da akwai fararen hula da aka killace su adaidai lokacin da ake ci gaba da kai wa asibitoci hare-hare. Eva Herneserova ta kuma ce; Babu sauki ko kadan a kokarin shiga cikin birnin domin isar da kayan agaji. Ma Magana da yawun kungiyar tarayyar turai din ta kuma yi gagradi akan cewa bai kamata a rika amfani da yunwa da kuma kisan kiyashi a matsayin makamin yaki...
Bugu da kari, a gefen taron na COP30, Ding ya gana da sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya Mista Antonio Guterres. (Bello Wang) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo November 7, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta November 7, 2025 Daga Birnin Sin Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru November 7, 2025
Wani yaro ɗan shekara biyu mai suna Danjuma Salman, ya rasu bayan ya faɗa cikin rijiya a Jihar Kano. Lamarin ya faru ne a Ƙaramar Hukumar Gwale. Gwamnatin tarayya ki amince damu a matakin ƙasa – Bijilanti Ma’aikacin jinya ya kashe marasa lafiya 10 saboda aiki ya masa yawa Rahotanni sun nuna cewa yaron ya zame ne sannan ya faɗa cikin rijiyar wadda murfinta ya lalace. Mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya bayyana cewa sun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 10:05 na safe daga wani mai suna Saminu Dayyabu, wanda ya sanar da su cewa wani yaro ya faɗa cikin rijiyar. “A lokacin da jami’anmu suka isa wajen, sun tarar...
Al’ummar Ƙauyen Sarai da ke Ƙaramar hukumar Dawakin Kudu a Jihar Kano sun shiga ruɗani a ranar Alhamis bayan da aka gano gawar wata mata mai shekara 96 a cikin masai. Jami’in hulɗa da jama’a na Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya bayyanawa manema labarai a ranar Juma’a. Ma’aikacin jinya ya kashe marasa lafiya 10 saboda aiki ya masa yawa Kamfanin wutar lantarki na Abuja ya salami ma’aikata 800 Abdullahi ya ce, sashin bayar da agajin gaggawa na hukumar ya samu kiran gaggawa daga wani mai suna Usman Adamu ranar Alhamis, inda ya bayyana cewa wata tsohuwa ta faɗa cikin masai a ƙauyen Sarai. “Hukumar kashe gobara ta...
“A yayin da ake tarwatsa masu kai harin, DPO na Sassan A da B sun tura ma’aikatansu suka harba hayaki mai sa hawaye, amma wasu motoci cikin motar gwamnan sun lalace,” in ji Abiodun. Ya bayyana cewa mutane uku na farko da ake zargi sune Ali Mohammed da Adamu Hussain, dukkansu daga yankin Nasarafu, Bida, da Isah Umaru na yankin Darachita, Bida. Ya kara da cewa an kama Nagenu, mai shekaru 39, daga yankin Bello Masaba, daga baya dangane da wannan lamari, sannan ya ambaci wasu biyu, Salihu Mohammed da Abdulrahman Baba, yayin tambayoyi. “Dukkan wadanda ake zargi suna karkashin bincike kuma suna taimaka wa ‘yansanda wajen gano wasu. Ana ci gaba da kokarin kama karin mutane da ake zargi,”...
Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya kaddamar da aikin samar da wutar lantarki ta hasken rana mai ƙarfin megawat 1 a garin Talasse, karamar hukumar Balanga. Aikin, wanda aka kulla ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Karkara (REA), Bankin Duniya, da kamfanin MIDS Dynamics, na da aniyar samar da wutar lantarki ba tare da yankewa ba ga sama da gidaje 8,000 a Talasse da kauyuka makwabta, idan aka kammala shi cikin watanni huɗu. Harin bam a masallacin Juma’a ya jikkata sama da mutum 50 a Indonesia Kamfanin wutar lantarki na Abuja ya salami ma’aikata 800 A wajen bikin kaddamar da aikin, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana shi a matsayin muhimmin ci gaba a...
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi Allah wadai da cin zarafin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke yi wa Lebanon Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta yi Allah wadai da babban harin soji da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai kan kasar Lebanon, tana dora alhakin kai harin kan Majalisar Dinkin Duniya, al’ummun duniya, da kuma kasashen yankin kan abin da ta bayyana a matsayin halin gwamnatin mamayar Isra’ila na kokarin tayar da masifar yaƙe-yaƙe. Ma’aikatar ta tabbatar da cikakken hadin kan Iran ga gwamnatin Lebanon da al’ummarta a kan wadannan hare-haren ta’addanci, tana mai jaddada goyon bayanta ga halaltacciyar gwagwarmaya wajen kare ikon mallakar Lebanon. Ta kara da cewa; Hare-haren soji da gwamnatin ‘yan Sahayoniyya take kai wa kan Lebanon, wadanda suka...
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi kira da a kafa kwamitin kasa da kasa domin tantance makomar wadanda suka bata a Gaza Shugaban Kwamitin Binciken Mutane da Suka Bace a tawagar Babban Hafsan Rundunar Sojin Iran, Birgediya Janar Seyyed Mohammad Baqirzadeh, ya gabatar da shawarar kafa kwamitin kasa da kasa don neman fiye shahidai 10,000 da suka bace a yankin Gaza. Birgediya Janar Baqirzadeh ya bayyana hakan ne a lokacin wani taro na bangarori uku wanda ya hada da Iran, Iraki, da Kwamitin Kungiyar Red Cross ta Duniya (ICRC), da nufin tantance makomar shahidai da suka bace da kuma mayar da gawarwakinsu ga iyalansu. Ya jaddada muhimmancin rawar da Kungiyar Red Cross take takawa wajen bin wannan batu na jin...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an November 6, 2025 Daga Birnin Sin CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST November 6, 2025 Daga Birnin Sin Baje Kolin CIIE Ya Bayar Da Tabbaci Ga Duniya November 6, 2025
Shugaban ya kuma yaba bisa gudunmawar da kwararrun matasa ke samar wa, musamman masu yiwa kasa hidima da ke yin aikin yiwa kasa hidama, a Hukumar ta NPA. Ya danganta su a matsayin matasan gobe da za su samar da sauyi wajen ci gaba da bunkasa fannin tattalin azrki na Teku da kuma ga daukacin tattalin arzikin kasar nan. An kirkiro da wannan ranar ta NMD ce, a shekarar 2014 wadda kuma aka kaddamar da ita a kasar Ingila a shekarar 2016, wadda kuma ake gudnar da bikin zagoywar ranar, a duk ranar 27 na watan Okutobar kowacce shekara. Kazalika, gudanar da bkin wannan ranar, ta yi daidai da cimma muradun karni, na Majalisar Dinkin Duniya. ShareTweetSendShare MASU ALAKA ...
Rahotanni su bayyan cewa zanga-zanga ta barke a wajen filin wasan kwallon kafa a Birmingham kafin fara gasar kwallon kafa tsakanin isra’ils maccabe tel aviv da kuma England Ason villa inda suke yi ta rera taken nuna damuwa da halin da yankin Gaza ke ciki da kuma yin kira ga hukumar fifa da ta kori Isra’ila daga cikintta, Wannan yana nuna irin yadda kin jinin Isra’la ya yadu a duniya saboda irin kisan gillan da take yi wa alummar gaza, inda lamarin ya shafi hatta a harkokin wasanni da sauran rayuwar alumma a kasashen turai . Rahotano da jaridar the independent ta nakalto ya nuna cewa magoya bayan falasdinawa sun lika hotuna a fadin birnin dake yin kira ga hukumar...
Kungiyar Genoa ta naɗa tsohon ɗan wasan tsakiyar Italiya, Daniele De Rossi, a matsayin sabon kociyarta, domin maye gurbin Patrick Vieira wanda ya bar ƙungiyar a ƙarshen mako. A wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, Genoa ta bayyana cewa tana “maraba da Daniele De Rossi” wanda ya jagoranci atisaye na farko da yammacin wannan ranar. Za a gudanar da taron manema labarai na farko da shi a ranar Juma’a.” Victor Osimhen ne kan gaba a yawan zura ƙwallaye a Champions League Ajax ta kori kocinta John Heitinga De Rossi, wanda ya taka leda na tsawon shekaru 17 a Roma kuma ya lashe Kofin Duniya tare da Italiya a 2006, ya taɓa horas da ƙungiyoyin Spal da Roma. Roma...
Ɗan wasan gaba na Nijeriya, Victor Osimhen, ya sha gaban fitattun ‘yan wasa irin su Erling Haaland, Harry Kane, da Kylian Mbappé a yawan zura ƙwallaye a gasar Champions League ta bana. Osimhen ya cimma wannan nasarar ce bayan ya zura ƙwallaye uku rigis a ragar Ajax a wasan zagaye na huɗu na gasar. Ajax ta kori kocinta John Heitinga Cin zarafin Wakilin NTA ya tada ƙura a Yobe Wannan ya kai adadin ƙwallayensa zuwa shida, yayin da Haaland, Kane da Mbappé ke da ƙwallaye biyar-biyar kowannensu. A watan da ya gabata, Osimhen ya kuma zura ƙwallaye uku a ragar Jamhuriyyar Benin a wasan neman tikitin shiga gasar Kofin Duniya ta 2026, abin da ya ƙara masa farin jini a...
Kungiyar kwallon ƙafa ta Ajax da ke ƙasar Netherlands ta sanar da sallamar kocinta, John Heitinga, a sakamakon rashin kataɓus da a yanzu ƙungiyar ta maƙale a ƙasan teburin gasar Zakarun Turai ta Champions League. A wata sanarwa da ta Ajax ta fitar a ranar Alhamis, ta ce tana neman sabon koci, inda a halin yanzu, Fred Grim zai riƙe aikin Heitinga har zuwa lokacin da za a naɗa sabon mai horarwa. Cin zarafin Wakilin NTA ya tada ƙura a Yobe An rantsar da shugaban Kamaru Paul Biya karo na 8 Heitinga, wanda ya sanya hannu kan kwantiragi na shekaru biyu a watan Mayu, ya gaza sauya akalar ƙungiyar, lamarin da Ajax ɗin ta tabbatar cewa ta kawo ƙarshen yarjejeniyar....
Cin zarafin da Babban Jami’an tsaro (CSO) na Gwamnan Yobe, CSP Yakubu Zakari Deba ya yi ga wakilin Talabijin NTA da ke Damaturu, Babagana Kolo a harabar Majalisar Dokokin Yobe da ke Damaturu a ranar Alhamis ya tada ƙura. Lamarin ya faru ne yayin da wasu ’yan jarida ke jiran a shigar da su cikin zauren domin su bayar da rahoto kan gabatar da kasafin kuɗin 2026 da Gwamna Mai Mala Buni ya yi a gaban Majalisar Dokokin. An rantsar da shugaban Kamaru Paul Biya karo na 8 Ƙungiyyar Ƙwallon yashi ta Kada BSC ta fatattaki Kebbi BSC Shaidu sun ce Babban Jami’in tsaro (CSO) na fadar gwamnatin Yobe, CSP Yakubu Zakari Deba, ya afka wa Kolo ya buge shi...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Harin Amurka ya bayyana karara kan Venezuela Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa: Barazanar da ake yi wa Venezuela ba ta dace da al’ummar duniya ba, yana mai jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kasance kuma za ta ci gaba da kasancewa cikin hadin kai da gwamnati da al’ummar Caracas. Da yake jawabi a bikin rantsar da ofishin wakilin Ma’aikatar Harkokin Waje a Lardin Hamadan, Araqchi ya bayyana cewa: Wannan ofishin zai taimaka wajen karfafa alakar tattalin arziki, kimiyya, da al’adu ta lardin, da kuma sauƙaƙe hulɗar jakadanci da gudanarwa ga ‘yan ƙasar. Ya lura cewa: Baba’i Ragheb, wani jami’in ma’aikatar da ya ƙware, zai jagoranci sabon...
Shugaban Majalisar Dokokin kasar Iran ya jaddada muhimmancin aiwatar da kuma kammala yarjejeniyoyin da aka cimma tsakanin Iran da Pakistan Shugaban Majalisar Dokokin Iran, Mohammad Baqir Qalibaf, ya jaddada muhimmancin matakin da ake dauka a yanzu na dangantakar da ke tsakanin Iran da Pakistan a dukkan fannoni na hadin gwiwa. Ya bayyana ziyararsa zuwa Pakistan a matsayin wani bangare na kokarin da ake yi na fadada dangantaka, musamman hadin gwiwar yankin tsakanin kasashen biyu. A cikin wata sanarwa da ya aike wa kamfanin dillacin labaran Iran ‘IRNA’ bayan ya isa birnin Islamabad, fadar mulkin kasar Pakistan, a safiyar Laraba, Qalibaf ya ce: “Iran da Pakistan, a matsayin kasashe makwabta, suna jin dadin hulda daban-daban a fannin tattalin arziki, siyasa, da...
Mutum guda ya yi shahada wasu uku kuma suka jikkata a harin da Yahudawan sahayoniyya suka kai kan yankin kudancin Lebanon An kashe mutum guda, wasu uku kuma sun ji rauni a hare-haren jiragen saman yakin gwamnatin mamayar Isra’ila da suka kai kan garin Tura da ke gundumar Taya na kasar Lebanon, a cewar wata sanarwa da Ma’aikatar Lafiyar Jama’a ta Lebanon ta fitar. Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Ma’aikatar Lafiyar Jama’a ta sanar a cikin wata sanarwa cewa: “Harin jiragen saman gwamnatin mamayar Isra’ila a kan garin Tura da ke gundumar Taya a yankin kudancin Lebanon ya haifar da mutuwar mutum ɗaya, wasu uku kuma sun ji rauni.” A wani hari na daban, wani jirgin saman yakin gwamnatin mamayar Isra’ila...
Muhimmin fadakarwa daga Sayyid Muqtada al-Sadr kwanaki kafin zaɓen kasar Iraki Malamin Tafarkin Shi’a na Iraki Muqtada al-Sadr ya umurci magoya bayansa a ranar Alhamis da su dakatar da duk wani zaman dirshan da zanga-zanga har zuwa lokacin zaben ‘yan majalisa dokokin kasar mai zuwa. A cikin wata sanarwa, ofishin al-Sadr ya ce ya yi nazari kan ayyukan da suka hada da tarurrukan kabilanci da na matasa da ke goyon bayan shawararsa ta kauracewa zaben kuma ya yi tsokaci, “Daga yanzu har zuwa ranar zabe, babu bukatar wani karin zanga-zanga.” Wannan shawarar ta ci gaba da tsarin al-Sadr na nisantar da kansa daga tsarin zaben tun bayan sanarwarsa a watan Yunin shekara ta 2022 na janye kansa gaba daya daga...
An rantsar da Paul Biya a matsayin shugaban ƙasar Kamaru karo na takwas mai shekaru 93 a majalisar dokokin ƙasar da ke Yaoundé. Paul Biya ya shafe shekaru 43 yana mulkin ƙasar, kuma yanzu zai fara wani wa’adi na tsawon shekara bakwai nan gaba. Ƙungiyyar Ƙwallon yashi ta Kada BSC ta fatattaki Kebbi BSC Kwalara ta kashe mutum 10 a Ƙaramar Hukumar Adamawa Biya wanda shine shugaban ƙasa mafi tsufa a duniya, ya sami kashi 54 na ƙuri’un zaɓe, yayin da abokin takararsa, Issa Tchiroma Bakary ya samu kashi 35%, a cewar sakamakon zaɓen hukumar ƙasa. Tchiroma Bakary dai ya yi iƙirarin cin nasara a zaɓen da aka yi yana kuma zargin cewa an yi maguɗin zabe, wanda hukumomi suka...
Wasu fusatattun matasa a ƙauyen Sokupkpan da ke karamar hukumar Edu a jihar Kwara, sun kashe Babban Limamin yankin, Mallam Abdullahi Audu, bisa zargin shi da alhaki kan mutuwar wani matashi, Ibrahim Gana ta hanyar maita. Shaidu sun ce lamarin da ya faru a ranar Laraba ya jefa al’ummar yankin cikin rudani da firgici. Gwamnatin Tarayya ta fara shirin sayar da matatun manta ga ’yan kasuwa Za a gudanar da wasannin ƙwallon yashi a Abuja An ce wannan farmakin ya samo asali ne daga zargin cewa limamin ya yi amfani da maita wajen cutar da mamacin. A cewar majiyoyi, kafin rasuwarsa, Gana ya dade yana fama da wata cuta da ba a bayyana ba, kuma ya sha faɗa cewa Babban...
Ministan Harkokin Wajen Iran ya yaba da juriyar da kasar ta nuna yayin hare-haren Amurka da Isra’ila, wanda ya tilasta musu rokon a tsagaita wuta ba tare da shiri ba. Da yake jawabi a yammacin ranar Laraba a taron Majalisar Gudanarwa ta Lardin Hamadan, Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa abokan gaba sun gaza a dukkan manufofinsu a lokacin yakin na kwanaki 12. Kalaffafen yakin na kwanaki 12 ya bamu babban darasi inji shi, saboda mun fi karfi da a ranar 13 ga watan Yuni. A karon farko, an yi amfani da makamai masu linzami na Iran a wani rikici na gaske, wanda hakan ya ba da damar gano ƙarfi da rauninsu. A yau, Iran tana...
Kasahen Iran, Rasha da kuma China sun gana a tsakaninsu a jajibirin taron Kwamitin Gwamnonin Hukumar kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA), Zaman ya hada jakadun kasashen uku a birini Vienna ranar Laraba don daidaita matsayinsu kan manyan batutuwan da suka shafi zaman na gwamnonin IAEA da ke tafe. Michael Ulyanov, jakadan Rasha kuma wakilin dindindin a kungiyoyin kasa da kasa a Vienna, ya wallafa a shafukan sada zumunta cewa kasashen uku sun yi “wani zagaye na shawarwari ” game da batun nukiliyar Iran. Ya kara da cewa wakilan sun daidaita matsayinsu don su shirya sosai don taron Kwamitin Gwamnonin da ke tafe. A cewar shirin da aka sanar, za a gudanar da zaman kwamitin na gaba daga ranar...
Osimhen, wanda ya koma Galatasaray daga Napoli, ya taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarorin ƙungiyar ta ƙasar Turkiyya, ciki har da lashe kofin ƙalubale. A yanzu haka, shi ne ɗan wasan da ya fi ci wa Galatasaray ƙwallaye a dukkanin da ta ke bugawa a bana, ya bar sauran fitattun ’yan wasa irin su Leroy Sane da Mauro Icardi a baya. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba November 2, 2025 Wasanni Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara November 2, 2025 Wasanni Shin Mene Ne Matsalar Liverpool A Wannan Kakar? November 2, 2025
Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya bukaci Amurka da Turai su nuna gaskiya idan suna son sake gina aminci da Iran. A wata tattaunawa ta wayar tarho tsakanin Shugaba Emmanuel Macron na Faransa, da takwaransa na Iran Mas’ud Pezeshkian, shugaban na Iran ya ce dole ne turai su mutunta ‘yancin Iran kuma su daina gabtar da bukatu da Iran ba za ta taba amincewa da su ba. Iran ta yi maraba da tattaunawa amma Pezeshkian ya sake nanata cewa, a yanzu ba Iran ce za ta tabbatar da gaskyarta ba, domin ta riga ta yi haka, ya rage kan kasashen turai ne su tabbatar wa duniya cewa da gaske suke yi a cikin abin da suke furtawa. Duk da haka, ya...
Mataimakin ministan harkokin wajen Iran kan harkokin ƙasa da ƙasa da shari’a ya jaddada muhimmancin kara karfafa dangantakar da ke tsakanin Tehran da Riyadh, yana mai cewa ci gaban kyakkyawar alaƙa tsakanin Tehran da Riyadh ba wai kawai yana da amfani ga ɓangarorin biyu ba ne, har ma zai kara karfafa zaman lafiya a yankin da ma a duniya. Kazem Gharibabadi ya yi wannan furuci ne bayan ziyarar da ya kai Saudiyya da nufin fadada haɗin gwiwa da haɗin kai tsakanin manyan ƙasashen biyu. Mataimakin ministan harkokin wajen ya jaddada cewa Iran da Saudiyya, waɗanda ke da alaƙa ta tarihi suna da kyakkyawan matsayi don yin hidima ga al’ummarsu da kuma taka domin ci gaban zaman lafiya a yanking abas...
“Wannan babban shiri ne da zai sake fasalin Zamfara, ya tabbatar da ci gaba mai ɗorewa tare da inganta rayuwar al’umma,” inji shi. Ya ƙara da cewa, a mafi yawan ƙananan hukumomin jihar ana gina sabbin hanyoyi na kilomita biyar a cikin birane, baya ga Gusau wadda ake gudanar da manyan ayyuka na musamman. Ya ce hakan zai rage cunkoso, ya haɗa al’umma, ya kuma farfaɗo da kasuwancin ƙauye da birane. A fannin lafiya, gwamnati ta ƙaddamar da gina sabon babban asibiti a Nasarawa Burkullu a ƙaramar hukumar Bukkuyum, tare da sabunta cibiyoyin kiwon lafiya da dama a yankunan karkara, domin sauƙaƙa samun ingantaccen magani. An kuma sanar da ci gaba da gyaran makarantu a dukkan...
Hukumar shirya gasar ƙwallon yashi ta ƙasa ta tabbatar da cewa za a gudanar da wasannin ƙarshe na bana a filin wasa na Jabi Lake Park, da ke babban birnin tarayya Abuja. Kodinetan hukumar a Najeriya, kuma shugaban hukumar a nahiyar Afirka, Mahmud Hadejia, ne ya tabbatar da hakan a lokacin da yake zantawa da Trust Radio a cikin shirin “Bakin Raga” da safiyar yau Laraba. An amince da hukuncin yi wa malamai ɗaurin shekara 14 kan lalata da ɗalibai Yara biyu sun mutu bayan faɗawa rijiya a Kano Shugaban ya bayyana cewa wannan ce gasa ta biyar da za a buga, kuma ta farko da za a fafata a Abuja. A cewarsa, za a fara buga wasannin ƙarshe daga...
Dantsoho ya bayyana cewa, a taron Tashoshin Jiragen Ruwa na Duniya da aka yi a Kobe, Kasar Japan, shugabannin tashoshin jiragen ruwa na Afirka sun yi alƙawarin haɓaka ci gaban Tashoshin yankin ta hanyar tsarin dabaru uku – aiwatar da manufofi, sabunta haɗin gwiwa, da sauƙaƙe ciniki, wanda wannan shi ne abin da NPA ta ƙuduri aniyar aiwatarwa. Shugaban na PMAWCA ya kuma yaba wa gwamnati da mutanen Jamhuriyar Congo saboda ɗaukar nauyin taron kuma ya yaba wa sakatariyar ƙungiyar bisa jajircewa wurin tabbatar da dandamalin tattaunawar tsakanin yankunan da kuma yadda ake samar da sabbin tsare-tsare a shugabancin kungiyar mai kula da teku. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Malam Triump: Ƙungiyoyin Ɗariƙun Sufaye Sun Maka Gwamnan Kano A...
Haka kuma, kaso 73.2 sun yi imanin cewa manyan kasashe ba sa sauke dukkan nauyin da ya rataya a wuyansu game da harkokin kasa da kasa, sannan kaso 81.9 sun yi kira ga MDD da ta kara mayar da hankali kan muradu da bukatun kasashe masu tasowa. (FMM) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou November 5, 2025 Daga Birnin Sin Firaministan Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Bikin Bude CIIE November 5, 2025 Daga Birnin Sin Sin Za Ta Gyara Matakan Haraji Kan Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Su Daga Amurka November 5, 2025
Kungiyoyin da suka yi hadin gwiwar shigar da karar sun hada da Interfaith Partners for Peace and Development, Fityanul Islam of Nigeria, Sairul Qalbi Foundation, Tijjaniyya Youth Enlightenment Initiative, Hablullahi Mateen Foundation, Dariqa Qadiriyya of Nigeria, Kadiriyya Youth Awareness, Kadiriyya Riyadul Janna Kofar Na’isa, Ashabul Kahfi Foundation, da Majmau Ashabul Yameen. LEADERSHIP ta ruwaito cewa, takaddamar da ta shafi Malam Lawan Triumph ta fara ne a watan Satumba bayan da wasu ƙungiyoyin addini suka ɗauki wasu wa’azozinsa a matsayin ɓatanci ga Annabi SAW, wanda ya haifar da cece-kuce da muhawara a faɗin jihar. Wannan lamari ya sa gwamnatin jihar ta shiga tsakani ta hannun Majalisar Shura ta Jiha, wadda aka ba da umarnin gudanar da bincike kan zarge-zargen. ...
Firaministan kasar Georgia Irakli Kobakhidze da firaministan kasar Serbia Duro Macu da shugaban majalisar wakilan kasar Najeriya Tajudeen Abbas, sun halarci taron bude bikin tare da ba da jawabai. Haka kuma wakilai kimanin 1500 daga sassan siyasa, kasuwanci da ilmi na kasashe da yankuna da kungiyoyin kasa da kasa 155 su ma sun halarci taron.(Tasallah Yuan) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Za Ta Gyara Matakan Haraji Kan Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Su Daga Amurka November 5, 2025 Daga Birnin Sin CIIE Na Sin Karin Tagomashi Ne Ga Kasashen Afrika November 5, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Kaddamar Da Kwas Din Horon Fasahar Gwaje-Gwaje A Cibiyar CDC Ta Afrika November 4, 2025
Ya lura cewa kasashe kamar China, Japan, da Indiya sun cimma gagarumin ci gaba a fannin kimiyya da fasaha ta hanyar amfani da harsunan asali don koyarwa a matakin ilimi na farko. A cewarsa, koyarwa a cikin harshen Hausa zai inganta fahimta tsakanin dalibai, rage yawan faduwa, da kuma rage yawan wadanda ake kora daga makaranta sakamakon faduwa a jarrabawa. Bayan tattaunawa, shugaban majalisar Jibrin Ismail Falgore, ya mika kudirin dokar ga kwamitin majalisar mai kula da harkokin ilimi domin ci gaba da bincike da neman shawarwari. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai ECOWAS Ta Ƙaryata Iƙirarin Trump Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya November 5, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana...
Haka kuma, daga ranar 10 ga watan Nuwamba, kasar Sin za ta soke matakin da ta dauka a kan wasu kamfanonin Amurka a cikin jerin kamfanoni marasa aminci da ta sanar a ranar 4 ga Maris na wannan shekara, kamar yadda wani mai magana da yawun ma’aikatar ya bayyana a cikin wata sanarwa. Mai magana da yawun ma’aikatar ya kara da cewa kamfanonin cikin gida za su iya gabatar da bukata da neman yin ciniki da kamfanonin Amurka da aka ambata a sama da zarar an amince da bukatunsu. (Amina/Abdulrazaq Yahuza Jere) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin CIIE Na Sin Karin Tagomashi Ne Ga Kasashen Afrika November 5, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Kaddamar...
Iran ta sanar da yi wa ‘yan faransa nan guda biyu da take tsare saki bisa sharadi a zarginsu da akeyia da yi wa tsaron kasar Iran zagon kasa. Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Esmail Baghai ya fitar da bayanin sakin yana mai cewa na yi shi ne “bisa umarnin alkali.” Ya kara da cewa za su ci gaba da kasancewa a karkashin kulawar shari’a har sai an ci gaba da shari’a. Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya tabbatar da labarin, inda ya bayyana mutanen biyu a matsayin Cécile Kohler da Jacques Paris, wadanda aka tsare a Iran bisa zargin leken asiri. A halin yanzu suna Ofishin Jakadancin Faransa da ke Tehran. A ranar 21 ga Oktoba, Mataimakin Ministan Harkokin Wajen...
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya bayyana “matukar damuwarsa” kan keta yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra’ila ke yi akai-akai a zirin Gaza. Da yake bayyana ga manema labarai a gefen taron koli na biyu na duniya kan ci gaban zamantakewa a Doha jiya Talata, Guterres ya ce: “Dole ne su dakatar da wadannan ayyuka, kuma dukkan bangarorin dole ne su mutunta sharuddan dake kunshe a matakin farko na yarjejeniyar zaman lafiya.” “Muna aiki tukuru don kara taimakawa mutanen yankin Gaza; muna goyon bayan mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma dawo da alaka tsakanin Gaza da Yammacin Kogin Jordan,” in ji Mista Guterres. Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ta shiga tsakani, hare-haren Isra’ila a Gaza...
Ya ƙara da cewa wannan mataki wani ɓangare ne na gyaran tattalin arziƙi da kuma dawo da amincewa ga tsarin kwangilolin gwamnati. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai ECOWAS Ta Ƙaryata Iƙirarin Trump Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya November 5, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru 86 November 5, 2025 Manyan Labarai Ɗan Majalisar Amurka Ya Zargi Kwankwaso Da Hannu A Kisan Kiristoci A Nijeriya November 5, 2025
Pars Today – Wakilin Iran na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana kalaman shugaban Amurka game da gwajin makaman nukiliya a matsayin abin tsoro. A cewar Pars Today, Amir Saeed Iravani, jakadan Iran kuma wakilin dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, ya rubuta a ranar Talata ga Shugaban Majalisar Tsaro da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya a matsayin martani ga kalaman Shugaban Amurka Donald Trump da barazanar nukiliya, yana mai kiran su “abin damuwa ne kwarai da gaske.” Iravani ya yi gargadin cewa irin wadannan kalamai suna wakiltar babbar barazana ga zaman lafiya da tsaro na duniya kuma suna nuna keta hakkokin Amurka a karkashin dokokin kasa da kasa. Shugaban Amurka ya sanar a ranar 29 ga Oktoba cewa...
Rahotanni sun nuna cewa shugaban kungiyar gwagwarmaya ta Hamas Musa abu marzuk ya shaidawa gidan talabijin din Aljazeera cewa sun yi watsi da batun tura dakarun tabbatar da zaman lafiya zuwa yankin Gaza wadanda zasu yi aiki a madadin sojojin mamayar Isra’ila Yace ba zamu taba amincewa da aikewa da sojojin da za su zama madadin sojojin Isra’ila a gaza ba, Wannan bayanin ya zo ne bayan da kasar Amurka ta fitar da wani daftarin kuduri a kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya dake bukatar kafa dakarun tababtar da zaman lafiya na wucin gadi a yankin Gaza, akalla na shekaru 2 adaidai lokacin da falasdinawa ke fargabar tsoma bakin kasashen waje a yankin, Rahotanni da aka fitar ya nuna cewa...
Gidan talabijin da radiyo na kasar iran ya rattaba hannu kan yarjeniyoyi guda biyar da kafar sadarwa ta kasar Pakistan kan harkokin sadarwa da aladu a wata ziyara da babbar tawagar kasar Iran ta kai birnin Islam abad na kasar Pakistan ,inda ya samu halartar ministan sadarwa da yada shirye shirye na kasar Attaullah Tarar. Wadannan yarjiniyoyin ya nuna irin babban matakin da aka taka a bangaren diblomasiya na sadarwa tsakanin Tehran da kuma Islam Abad, wanda zai kara bunkasa alakar alaadu da sadarwa yadda zaa yi aiki tare a fadin kudancin Asiya. Tawagar kasar iran da Ahmad Norouzi ya jagoranta shugaban bangaren gidajen radiyoyin kasashen waje na gidan talabijin da redio na kasar iran su ne suka jagorancin sanya...
Rahotanni sun nuna cewa shugaban kungiyar Ansarullah Abdul-malik al-houthi yayi gargadin cewa yankin yana gab da fuskantar gagarumin rikici da isra’ila da kasashen yamma a yanki, don haka yasha alwashin cewa tsayin dakar dakarun kasar yafi karfi fiye da baya kuma a shirye take ta kalubalanci duk wanda yayi mata shisshigi a nan gaba. Wadannan kalaman suna nuna irin yadda ake samun karuwar fadace-fadace a yammacin asiya yayinda kungiyoyin dake goyon bayan yan gwagwarmayar daga yaman da labanon ke ciin shirin ko ta kwana na yaki da isra’ila da kawayenta na kasashen turai, haka kuma jawabin ya jaddda irin dabarun yaki da kungiyoyin yan gwagwarmaya da isra’ila suka bi bayan yakin gaza da kuma sabunta kokarin sojojin Amurka a yankin...
Sin Na Goyon Bayan Najeriya Wajen Jagorantar Al’ummarta Zuwa Hawa Turbar Neman Ci Gaba Daidai Da Yanayin Kasar
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta yi tsokaci game da matakin Amurka na sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ake da damuwa a kansu, inda ta jaddada matsayin Sin na matukar goyon bayan gwamnatin Najeriya, wajen jagorantar al’ummarta zuwa turbar neman ci gaba bisa yanayin da kasar ke ciki. A ’yan kwanakin nan ne shugaban Amurka Donald Trump, ya sanar da sanya Najeriya cikin jerin kasashen da kasarsa ke kara mayar da hankali a kansu, bisa zargin barazanar da ya ce mabiya addinin Kirista na fuskanta a kasar. Trump ya kara da cewa, idan har gwamnatin Najeriyar ta gaza shawo kan kisan Kiristoci, to Amurka za ta hanzarta dakatar da dukkanin tallafin da take baiwa kasar, kana...
Sanata Ali Ndume ya ce jahiltar halin da Najeriya ke ciki ne ya sa Shugaban Amurka Donald Trump ya yi iƙirarin cewa ana kisan Kiristoci a ƙasar. Ndume, wanda ke wakiltar mazabar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise ranar Talata. Ousmane Dembele zai buga wasan PSG da Bayern Munich ’Yan kwangila sun hana zaman majalisa kan rashin biyan haƙƙoƙinsu Sanatan ya ce maganganun Trump sun nuna rashin cikakken fahimtar yadda matsalar tsaro take da sarƙaƙiya a Najeriya. Ya ce matsalar rashin tsaro a ƙasar ta shafi al’umma baki ɗaya ba tare da la’akari bambancin addini ba, yana mai cewa “mutane daban-daban ne ke...
Majalisar Wakilai ta dakatar da zamanta na tsawon mako guda, sakamakon zanga-zangar da wasu ’yan kwangila suka gudanar a ƙofar shiga ginin majalisar dokoki ta ƙasa da ke Abuja, saboda rashin biyan kuɗaɗen ayyukan da suka kammala tun shekarar 2024. Rahotanni sun ce ’yan kwangilar sun yi dandazo ne a ƙofar shiga majalisar a ranar Talata, domin nuna rashin jin daɗinsu kan yadda gwamnati ta gaza biyansu haƙƙoƙinsu duk da cewa sun kammala ayyukan da aka ba su. China ta yi martani kan barazanar Trump ta kai hari Najeriya Kotu ta sahale wa PDP gudanar da babban taronta a Ibadan Bayanai sun ce masu zanga-zangar sun rufe hanyoyin shiga da fita na majalisar, abin da ya tilasta shugaban majalisar da sauran...
Kakakin Dakarun Kare Juyin Juya Halin Mususluni na bayyana yaƙin kwanaki 12 kan Iran ya tabbatar da cewa ba za a taɓa amincewa da Amurka ba Kakakin Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC) ya tabbatar da cewa: Yakin kwanaki 12 da aka yi da Iran ya nuna rashin amana ga masu yanke shawara na Amurka, kuma al’ummar Iran sun san halin da ake ciki kuma sun haɗu wuri ɗaya, inda suka samar da garkuwar da ba za a iya ratsawa ba. Birgediya Janar Ali Mohammad Na’ini, kakakin Dakarun kare juyin juya halin Musulunci {IRGC}, ya yi jawabi ga mahalarta taron gangamin Ranar Yaƙi da Girman Kai na Duniya a Karaj, yana mai nuna godiyarsa ga kasancewar mutane masu aminci...
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei, ya bayyana cewa rikicin da ke tsakanin Tehran da Washington ya samo asali ne daga muradun jama’a, yana mai gargadin cewa duk wani hadin gwiwa da Amurka za a iya cimma shi ne kawai idan ta kawo karshen goyon bayan da take bai wa Isra’ila, ta kuma janye dukkan sansanonin sojinta daga yankin, sannan ta daina tsoma baki a harkokin Iran. Ayatollah Seyyed Ali Khamenei ya bayyana hakan yayin ganawa da wani rukunin dalibai na kasar a jajibirin Ranar Dalibai ta Kasa wacce kuma ta yi daidai da ranar kasa ta yaki da girman kai na duniya. Jagoran ya bayyana ranar a matsayin “ta tarihi” kuma wani muhimmin bangare...
Kasashen Musulmi bakwai, da suka yi taro a Istanbul a ranar Litinin don tattauna makomar Gaza, sun dage kan cewa Falasdinawa ne kawai ke da hakkin mulkin kansu, inda sukayi fatali da sabon tsarin kafa wata wani kwamitin gudanarwa na kasa da kasa a yankin bayan makonni biyu na tsagaita wutar da akayi wacce ke tangal-tangal. “Dole ne Falasdinawa su mallaki Falasdinawa, kuma Falasdinawa dole ne su tabbatar da tsaron kansu,” in ji Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan, ga manema labarai bayan ganawa da takwarorinsa daga Saudiyya, Qatar, Hadaddiyar Daular Larabawa, Jordan, Pakistan, da Indonesia. “Akwai bukatar sake gina Gaza, kuma mutanenta suna bukatar komawa gida inji shi. Ya bayyana fatansa na “sulhu tsakanin Falasdinawa” cikin sauri tsakanin Hamas...
A Tanzaniyaan rantsar da Shugabar kasar Samia Suluhu Hassan a wa’adinta na biyu bayan ta lashe zaben da ya haifar da mummunar zanga-zanga a fadin kasar. An ayyana Samia, wacce ta hau mulki a shekarar 2021 bayan mutuwar magabacinta, a matsayin wacce ta lashe zaben da aka gudanar a makon da ya gabata da kashi kusan 98.% na kuri’un da aka kada. Tayi rantsuwar kama aikin ne a sansanin sojoji da ke Dodoma, babban birnin kasar. Samia Hassan mai shekaru 65 ta fafata da ‘yan takara daga kananan jam’iyyu, yayin da manyan abokan hamayyarta daga manyan jam’iyyun adawa biyu aka haramta musu tsayawa takara. Babbar jam’iyyar adawa a kasar ta ce an kashe daruruwan mutane a zanga-zangar. Gwamnati ta yi...
A Iran dubban ‘yan kasar ne suka taru a Tehran da kuma birane sama da 900 a fadin kasar don tunawa da karbe ofishin jakadancin Amurka a 1979, bikin da ake wa lakabi da ‘’Ranar Yaki da Girman Kai ta Duniya’’ A kasar. Dalibai, matasa, malamai, da iyalai ne suka halarci tarurrukan na yau Talata suna masu Allah wadai da ayyukan Amurka da Isra’ila, gami da harin da suka kai wa Iran a watan Yuni. Mahalarta tarukan dauke da tutocin Iran da hotunan wadanda suka yi shahada a hare-haren Isra’ila da Amurka yayin da suke rera taken “Mutuwa ga Amurka” da “Mutuwa ga Isra’ila.” Jami’ai daga cibiyoyin gwamnati da na soji, iyalan shahidai, da tsoffin sojoji yakin da Irak na...
Sarakunan gargajiya, lauyoyi da jami’an gwamnati sun koka bisa yawaitar kananan ’yan mata da ke daukar ciki da kuma zubar da ciki ba bisa ƙa’ida ba, a sansanonin ’yan gudun hijira da ke Maiduguri, Jihar Borno. Lamarin ya fito fili ne a wani taron tattaunawa na kwanaki biyu da ƙungiyar Grassroots Researchers Association (GRA) ta shirya tare da tallafin We Are Not Weapons of War (WWoW) a karshen makon da ya gabata a Maiduguri. Taron ya haɗa mutane fiye da 500, ciki har da waɗanda suka tsira daga fyade da cin zarafi a lokacin rikici, sarakunan gargajiya, lauyoyi, jami’an gwamnati da abokan ci gaban ƙasa, domin tattauna hanyoyin magance wannan matsala. “’Yan mata kanana na sayar da jikinsu, suna kuma zubar...
Wata majiya ta hizbbulla ta fadawa gidan talabijin din al-hadatha cewa kungiyar tana nan kan bakanta na yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka sanyawa hannu tsakaninta da isra’ila musamman a yankunan kudancin kasar da kuma tekun litani Duk da yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma a watan decembar shekara ta 2024 amma akwai fargaba sosai a iyakokin labanon da Isra’ila , sai dai hizbullah ta fitar da sanarwa a baya bayan nan wanda ke nuna shirinta na mayar da martani mai tsanani idan israila ta tsokaneta, duk da kasashen yamma na kokarin ganin an kawar da makamai da kuma rage tasirinsu, adaidai lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan yiyuwar sake barkewar wani rikici Ministan...
Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Yayi Maraba Da Kalaman Da Hukumar IAEA Ta yi Kan Shirin Nukuliyarta
Ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa bayanan baya bayan nan da hukumar kula d makamashin nukiliya ta duniya da ministan harkokin wajen Oman suka fitar na cewa iran bata kokarin kera makamin nukiliya ya karyata ikirarin da Amurka da HKI ke yi kan shirin nata. Babban darakata janar na hukumar IAEA a baya bayan nan ya fayyace cewa iran bata kokarin kera makamin nukiliya da kuma kasar Oman babbar mai shiga tsakanin da aka amincewa tsakanin iran da Amurka, yace wadannan kalamai zasu iya bude kofar sake koma teburin tattaunawa tsakanin Iran da kuma kasashen duniya. Rafeal Grossi ya fitar da sanarwar cewa iran bata neman kera makamin nukiliya shi ma ministan harkokin wajen oman Al-busaidi...
Carlos Alcaraz da Jannik Sinner za su buga wasan baje koli a Koriya ta Kudu a watan Janairu, kwanaki takwas kacal kafin fara gasar Australian Open. ’Yan wasan biyu kuma za su hadu a babban wasan Hyundai Card Super Match a Incheon, a ranar 10 ga Janairu, yayin da za a fara babbar gasar Australian Open a Melbourne a ranar 18 ga Janairu. Barazanar kawo hari abin ɗaga hankali ne ga duk ’yan Nijeriya — Peter Obi Gidan rediyo ya ɗauki nauyin sanya yara 40 a makaranta a Kano Kafin hakan dai ’yan wasan biyu, wadanda suka hadu a wasanni uku daga cikin hudu na Grand Slam a shekarar 2025, sun lashe kofuna tara cikin manyan gasa 10 da suka...
Kakakin ma’aikatar kula da harkokin kasuwanci ta kasar Sin, He Yadong ya sanar da cewa, za a gudanar da taron CIIE karo na 8 a birnin Shanghai daga ranar 5 zuwa ta 10 ga watan Nuwamba. Kuma firayim ministan kasar Sin Li Qiang zai halarci bikin bude taron da sauran ayyukan tare da gabatar da wani jawabi. (Amina Xu) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan November 3, 2025 Daga Birnin Sin Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar November 2, 2025 Daga Birnin Sin Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta...
Daruruwan matafiya ne suke zaman dirshan a filin saukar jiragen sama na kasar Tanzania saboda rikicin da ya barke sanadiyyar rikicin zaben shugaban kasa, da Samia Suluhu Hassan ta lashe da kaso 97%,kamar yadda hukumar zaben kasar ta sanar. An soke dukkanin tafiye-tafiyen jiragen sama da hakan ya sa matafiya na kasashen waje da dama suka makale a filayen jiragen sama saboda yanke hanyar sadarwa ta “Internet.” Wani mtafiyi dan yawon bude ido Irvine Rene a filin suakar jiragen saman a Zanzibar ya fadawa manema labaru cewa: ” Muna kan hanyarmu ne daga nan Zanzibar zuwa Paris, amma an soke jirgin da zai kai mu zuwa Nairobin kasar Kanya, don haka mun makale a nan.” Kasashe da dama sun gargadi...
Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya ce; sabanin da yake a tsakanin Jamhuriyar musulunci da Amurka na tushe ne, ba wani abu ne na sama-sama ba. Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda ya gabatar da jawabi da dubban dalibai da iyalan shahidai a jajiberin ranar “Fada Da Masu Girman Kai Na Duniya” da shi ne gobe 13 ga watan Aban/1404= 4/11/2025, ya kara da cewa; Ya zama wajibi a ci gaba da raya wannan rana. Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya tabo ydda a ranar 4 ga watan Nuwamba 1979 daliban jami’o’in Iran su ka mamaye ofishin jakadancin Amurka dake birnin Tehran saboda ya zama cibiyar kitsa makirce-makirce akan jaririn juyin musulunci. Jagoran juyin musuluncin ya...
An rantsar da Samia Suluhu Hassan a wa’adin mulki na biyu a matsayin shugabar Tanzaniya, duk da tarzomar da ta ɓarke bayan zaɓen da aka gudanar a makon jiya. A wani ƙwarya-ƙwaryar biki da aka gudanar cikin matakan tsaro a Dodoma, babban birnin ƙasar, an rantsar da shugabar a wani wurin da ba a bai wa mutane da dama sun halarta ba. An kashe ’yan bindiga 19 yayin wani hari a Kano Komai zai iya faruwa a hare-haren da za mu kai Nijeriya — Trump Riƙe da Al-Qura’ni a hannu guda, Shugaba Hassan ta ce “na yi alƙawalin yi wa ’yan ƙasa aiki tuƙuru, zan yi biyayya ga dokoki na ƙasa da mutunta kundin tsarin mulki.” Baƙin da aka gayyata...
An rantsar da Samia Suluhu Hassan a wa’adin mullki na biyu a matsayin shugabar Tanzaniya, duk da tarzomar da ta ɓarke bayan zaɓen da aka gudanar a makon jiya. A wani ƙwarya-ƙwaryar biki da aka gudanar cikin matakan tsaro a Dodoma, babban birnin ƙasar, an rantsar da shugabar a wani wurin da ba a bai wa mutane da dama sun halarta ba. An kashe ’yan bindiga 19 yayin wani hari a Kano Komai zai iya faruwa a hare-haren da za mu kai Nijeriya — Trump Riƙe da Al-Qura’ni a hannu guda, Shugaba Hassan ta ce “na yi alƙawalin yi wa ’yan ƙasa aiki tuƙuru, zan yi biyayya ga dokoki na ƙasa da mutunta kundin tsarin mulki.” Baƙin da aka gayyata...
Zamfara Ta Tashi Daga Matsayi Na 36 Zuwa Na 17 A Shekara Biyu Ƙarƙashin Gwamna Lawal — Rahoton BudgIT
A shekarar 2023 lokacin da Gwamna Lawal ya hau mulki, Zamfara ta kasance a ƙasan jadawalin a matsayi na 36. Rahoton ya nuna cewa kuɗaɗen shiga na jihar sun ƙaru da kashi 182.34%, daga naira biliyan 87.44 a 2023 zuwa naira biliyan 246.88 a 2024. Haka kuma jimillar kuɗaɗen shiga gaba ɗaya ta ƙaru zuwa naira biliyan 315.53, ƙaruwar kusan kashi 118%. Haraji da jihar ta tara ya kai kusan kashi 10.31% na jimillar kuɗaɗen shiga a 2024. BudgIT ta bayyana cewa wannan ci gaban yana nuna Zamfara ta fara rage dogaro ga kuɗin kason asusun tarayya, kuma idan za a yi hasashe, jihar na da ƙarfin kai da kai idan za a kalle ta a matsayin ikon...
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce ƙasarsa na shirin ɗaukar matakan soja da ka iya haɗawa da hare-haren ƙasa da na sama a Nijeriya. Trump ya bayyana haka ne yayin da yake tattaunawa da manema labarai, inda yake amsa tambayar yanayin yadda hare-haren za su kasance ta sama ko ta ƙasa. NAJERIYA A YAU: Ko Kawo Dakarun Amurka Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya? Tsagin Damagum da Anyanwu sun shirya mamaye hedikwatar PDP a yau A cewarsa, “komai na iya faruwa, abubuwa da dama za su faru. Ina nufin abubuwa masu yawa,” in ji shi kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito. Shugaban ya ƙara da cewa, “Suna kashe Kiristoci, kuma suna kashe su da yawa. Ba...
Ofishin Yada Labarai na Gwamnatin Gaza Ismail al-Thawabteh y ace Rundunar sojin Isra’ila ta aikata laifuka 194 tun bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza wadda ta fara aiki a ranar 10 ga Oktoba. al-Thawabteh, darektan ofishin, ya shaida wa kamfanin dinalancin labarai na Anadolu cewa laifukan sun hada da hare-haren da Isra’ila ta kai hana shigar da kayayyakin lafiya, magunguna, tantuna. Jami’in na Hamas ya ce sojojin Isra’ila sun sha ketare “layin da aka shata musu”, suna aika motoci zuwa wuraren zama, suna kai hare-hare ta sama da rusa gidaje, wanda ya haifar da mutuwar fararen hula da raunuka. A cewar ofishin yada labarai, daga ranar 10 ga Oktoba zuwa karshen watan, manyan motoci 3,203 ne kawai suka shiga...
Har ila yau, majalisar ta amince da Naira biliyan 3.3 don ayyukan samar da ruwa da makamashi domin inganta samar da ruwa mai tsafta da aminci a cikin al’ummomin birane da karkara. Daga cikin ayyukan samar da ruwan, an amince da gina tashar tace ruwa ta zamani a Taliwaiwai da ke ƙaramar hukumar Rano, da kuma biyan bashin kuɗin wutar lantarki da man fetur da ake bin hukumar ruwa ta jihar don ci gaba da ayyuka. Wani ɓangare na kuɗaɗen zai kuma haɗa da biyan basussukan da kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano (KEDCO) ke bi, siyan dizal (AGO) da man fetur (PMS) don ayyukan tashoshin tace ruwa, da kuma kula da kayayyakin da tashoshin ke bukata don...
Wani magidanci, Malam Jibrin Rabi’u, ya bayyana yadda matarsa, Khadijat Ado, ta ɓace a gidansu da ke unguwar Life Camp a Abuja a ranar Alhamis da ta gabata, sannan kuma aka gano ta a Sakkwato washegari. Ya shaida wa wakilinmu da yammacin Lahadi, cewa ya dawo gida a ranar Alhamis, sai ya tarar da matarsa ba ta nan. Malam Jibril ya ce, ya kira wani abokinsa ɗan sanda, wanda ya sanar da ofishin ’yan sanda na Life Camp, Gwarinpa da sauran sassan yankin bayan bincike na farko ya gagara gano inda take. A cewarsa, na’urar CCTV da ke gidansu ta nuna yadda matarsa ta fita daga gidan cikin natsuwa, har sai da ta fita daga inda kyamarar ke iya ɗauka....
Kakakin hukumar kula da kanana yaran ta majalisar dinkin duniya tess ingram ta bayyana cewa yanayin da yara ke ciki a yankin gaza yayi muni sosai, inda sama da yara miliyan daya dake gaza suke bukatar taimakon gaggawa na ruwan sha da kuma abinci Ingram ta fadi a wata hira da aka yi da ita cewa dubban yara a falasdinu suna kwana da yunwa kusan kowanne dare, kuma akalla yara 650,000 ba su koma makaranta ba duk da yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimamma a baya –bayan nan tsakanin bangarori biyu, Har ila yau ta bayyana batun dakatar da bude wuta a matsayin labari mai kyau, da ya kawo karshen ci gaba da lugudan wuta da israila ke...
Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar gwagwarmaya ta Hamas tayi watsi da zargin da Amurka ta yi mata a baya bayan nan na cewa mayakanta sun wawushe kayayyakin agaji da wata mota take dauke da shi a yankin Gaza, ta bayyana zargin a matsayin karyace kawai mara tushe balle madafa, tace Amurka na wannan zargin ne domin fakewa da shi wajen takaita shigar da kayyakin agaji a yankin gaza, Wannan yana nuna karuwar takaddama tsakanin Amurka da sauran bangarorin falasdinawa kan batun samar da kayayyakin agaji da kuma daukar nauyin da ya rataya a wuyansu, gannin yadda tallafi yayi karance kuma kayayyakin more rayuwa sun tabarbare don haka irin wadannan zarge-zarge na iya kara tsananin rashin yarda da kuma kawo cikas...
A wata hira da kafar watsa labarai ta iran press ta yi da jagoran harkar musulunci a najeriya shaikh Ibrahim zakzaki yayi tir da ci gaba da kashe mutane da ake yi a kasar sudan inda kungiyar RSF ta kasashe sama da mutane 2000 a garin el-fishar, ya zargi kasar hadaddiyar daular larabawa da ruruta wutar yaki a madadin kasashen masu girma na duniya. Yakin basasar dake ci gaba da gudana a kasar sudan ya dauki mummunan yanayi yayin da kungiyoyin masu samun goyon bayan kasashen waje ke kara kai hare-hare kan fararen hula da basu ji ba basu gani ba, bayanan na shaikh zakzaki sun kara haskaka yanayin siyasar da ke mayar da kasashen afrika fagen yaki don rarrabasu,...
Kakakin gwamnatin kasar iran fateme muhajirani ta bayyana cewa ma’aikatar harkokin wajen kasar iran ta tabbar da karbar sakon da ya kunshi batun fara tattaunawar diplomasiya tsakaninsu da Amurka, sai dai za’a bayyana yadda za ta kasance da kuma abubuwa da ta kunsa a nan gaba. Wannana mataki ya nuna cewa ana iya ci gaba da kokarin ganin an koma teburin tattaunawa da ta tsaya cak ,sai dai duka da haka matsayin iran na kin amincewa da tattaunawa kai tsaye yana nan daram kuma yana nuna irin sarkakiyar diplomasiya da kuma bukatar masu shiga tsakani amintattu da za su jagoranci tattaunawar. Sanarwa ta fito ne a daidai lokacin da ake yayata batun ci gaba da tattaunawa ba kai tsaye ba...
Ministar Jin Dadin Jama’a ta Sudan, Salma Ishaq, ta bayyana cewa Mayakan (RSF) sun kashe mata kusan 300 tare da yi wa 25 fyade a El Fasher, babban birnin Jihar Darfur ta Arewa a yammacin Sudan, a matsayin wani bangare na ayyukan kisan kiyashin da suke aikatawa a yankin. A ranar 26 ga Oktoba, dakarun RSF sun kwace iko da El Fasher kuma sun yi kisan gilla ga fararen hula, a cewar kungiyoyin cikin gida da na kasa da kasa. A cikin sanarwar da ta fitar Salma Ishaq, Ishaq ta ce abin da ya faru a El Fasher “ya yi kama da abin da ya faru a El Jeneina a shekarar 2023, amma ba a bankado da kuma yada laifukan...
Daga Usman Mohammed Zaria Majalisar Ƙaramar Hukumar Babura ta Jihar Jigawa ta bayar da tallafin abinci ga fursunonin cibiyar gyaran hali ta Babura a matsayin wani ɓangare na ayyukan jin ƙai na majalisar. Yayin ziyarar, Alhaji Hamisu Muhammad Garu ya bayyana cewa, wannan taimako ya biyo bayan lura da bukatun fursunonin yayin da ya kai ziyara ta duba cibiyar a baya. A cewarsa, manufar bayar da tallafin ita ce don tallafa musu wajen kyautata rayuwarsu da kuma karfafa musu gwiwa su zama mutane nagari bayan sun fito daga gidan gyaran hali. A nasa jawabin, jami’in da ke kula da cibiyar gyaran hali ta Babura, ASP Muhammad Ali, ya gode wa shugaban ƙaramar hukumar bisa wannan karamci, yana mai cewa...
Wani fursuna mai suna Abba Hassan, wanda aka yanke wa hukuncin kisa, ya tsere daga gidan gyaran hali na Potiskum da ke Jihar Yobe. Rundunar ’yan sanda ta Jihar, ta tabbatar da wannan lamari a cikin wata sanarwa da kakakinta, DSP Dungus Abdulkarim, ya fitar a ranar Asabar. Tinubu ya yanke hulɗa da Amurka kawai — Sheikh Gumi Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka A cewar sanarwar, Abba Hassan, wanda asalinsa ɗa Jihar Borno ne, ya gudu daga gidan yarin a ranar 31 ga watan Oktoba, bayan kotu ta yanke masa hukuncin kisa. DSP Abdulkarim, ya roƙi jami’an tsaro, direbobi, sarakunan gargajiya, ’yan banga da al’ummomin Jihar Yobe da maƙwabtan jihohi da...
Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya shawarci Shugaba Bola Tinubu da ya ɗauki mataki mai tsauri a kan Shugaban Amurka, Donald Trump, game da barazanar da ya yi na amfani da ƙarfin soja a kan Najeriya. Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, malamin ya bayyana cewa irin wannan magana ta Trump cin mutunci ce ga ’yancin Najeriya. Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon barazana — Kwankwaso Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka Don haka malamin ya yi kira da a ɗauki matakin diflomasiyya cikin gaggawa. “Trump ya yi barazana ga ƙasa mai cin gashin kanta da harin soja, wannan girmamawa ne...
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana damuwarsa kan kalaman da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi game da Najeriya. Kwankwaso, ya yi wannan magana ne bayan Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin yaƙi game da zargin kisan kiyashi da ake yi wa Kiristoci. Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka Kisan Kiristoci: Lauyoyi sun nemi Gwamnatin Tarayya ta tattauna da Amurka A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso, ya ce Najeriya ƙasa ce mai cikakken ’yanci, wadda ke fama da matsalar tsaro daga miyagu a sassa daban-daban na ƙasar. “Matsalar tsaron da muke fuskanta ba ta bambanta tsakanin addini, ƙabila ko ra’ayin siyasa,” in ji...
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana damuwarsa kan kalaman da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi game da Najeriya. Kwankwaso, ya yi wannan magana ne bayan Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin yaƙi game da zargin kisan kiyashi da ake yi wa Kiristoci. Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka Kisan Kiristoci: Lauyoyi sun nemi Gwamnatin Tarayya ta tattauna da Amurka A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso, ya ce Najeriya ƙasa ce mai cikakken ’yanci, wadda ke fama da matsalar tsaro daga miyagu a sassa daban-daban na ƙasar. “Matsalar tsaron da muke fuskanta ba ta bambanta tsakanin addini, ƙabila ko ra’ayin siyasa,” in ji...
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Faɗaɗa masana’antar makamashin nukiliyar Iran don inganta rayuwar mutanen kasar ne, ba don makamai ba Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya gana da manyan jami’ai a masana’antar makamashin nukiliya ta ƙasar a lokacin ziyarar da ya kai Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran (AEOI). Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Masoud Pezeshkian, ya ziyarci AEOI a ranar Asabar da yamma, inda ya gana da wasu manyan jami’ai a masana’antar makamashin nukiliyar. A yayin taron, Shugaba Pezeshkian ya jaddada cewa: Abin takaici, farfagandar son zuciya ta sanya ra’ayin “Makamashin nukiliya” ya zama daidai da samar da makaman nukiliya. Ya ce, “Samar da bama-bamai na nukiliya ƙaramin ɓangare ne kawai na sakamakon da ba su dace ba da...
Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Isra’ila ba za ta kai hari kan Iran ba sai da goyon bayan Amurka Ministan harkokin wajen Iran Seyyed Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Gwamnatin ‘yan sahayoniyya ba za ta kaddamar da yaki kan Jamhuriyar Musulunci ba tare da samun wata kariya daga Amurka ba. Ya kara da cewa, Iran ta gudanar da yakin kwanaki goma sha biyu da wannan gwamnati mai wuce gona da iri, kuma ta hana ta ci gaba da mummunar manufarta ta mamaya a yankin. A wata hira da ya yi da gidan talabijin na Al- Jazeera, Araqchi ya yi nuni da cewa: Gwamnatin masu wuce gona da iri ta yi kokarin fadada yakin zuwa yankin ta hanyar kai...
Sakataren Majalisar Tsaron kasar Iran ya jaddada cewa: Ba suna cewa ba za su gudanar da tattaunawa ba ne, amma tattaunawar dole ta kasance ta gaskiya Sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran, Ali Larijani, ya tabbatar da cewa: Ba za a iya kwantar da hankalin makiya ta hanyar yin sassauci da rashin gindaya sharaɗi ba. Da yake jawabi a wani taron masana ilimin bil’adama a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran ‘yan kwanaki da suka gabata, Larijani ya bayyana cewa: “Hanya madaidaiciya ta gyara halayen makiyansu tana cikin ƙarfafa haɗin kan ƙasa, kuma tushenta shine gyare-gyaren tattalin arziki da dawo da kwanciyar hankali ga rayuwar mutane.” Sakataren Majalisar Tsaron kasar Iran ya jaddada cewa: Ba za a iya kwantar da...
Gwamnatin mamayar Isra’ila ta yanke hukuncin kisa kan masu fama da cutar kansa da kuma waɗanda suke fama da matsalar koda na mutuwa a Gaza domin hana fitar da su wata kasa don neman magani Cibiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Gaza ta bayyana matukar damuwarta game da tabarbarewar lafiyar marasa lafiya da ke fama da cutar kansa da kuma cutar koda a Zirin Gaza. Wadannan cututtuka sun kara ta’azzara ne sakamakon hare-haren sojojin mamayar Isra’ila kan Gaza da kuma ci gaba da killace yankin bayan tsagaita bude wuta, gami da hana shigar dq magunguna da kayayyakin ayyukan likitanci masu muhimmanci cikin yankin. Cibiyar ta kuma yi nuni da tsauraran matakan fitar da marasa lafiya zuwa ƙasashen waje don neman...
Babban dakaktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta Duniya ya tabbatar da cewa Iran ba ta kera makaman nukiliya ba, yana mai jaddada cewa tana ci gaba da kasancewa cikin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT). Rafael Grossi, ya shaida wa manema labarai a hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke New York cewa “Zan iya cewa babu wani shirin makamin nukiliya domin mun dade muna duba shi. Wannan ya zo ne yayin da Iran ta yi gargadin cewa aiwatar da abin da ake kira “snapback” da sake sanya takunkumin Majalisar Dinkin Duniya da kasashen Turai uku za su soke yarjejeniyar da ta yi da IAEA kan sake fara hadin gwiwa da aka sanya wa hannu a birnin Alkahira a ranar...