Mutane Da Dama Ne Ake Jin Tsoron Sun Rasa Rayukansu A Lokacinda Motar Daukar Gas Ta Yi Bindiga A Kan Gadar Karu A Birnin Abuja
Published: 20th, March 2025 GMT
Asbitoci a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya wadanda suka hada da Asbitin kasa da kuma na Asokoro duk a ciki suke da wadanda suka ji rauni, ko sun mutu bayan da wata motar daukar gas ta yi hatsari a kan gadar Karu a tsakiyar birnin Abuja a jiya Laraba da misalign karfe 7:14 na yamma.
Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta bayyana cewa wasu majiyoyi sun tabbatar da mutuwar muta ne 6 sannan wasu da dama sun ji rauni sanadiyyar hatsarin.
Labarin ya nakalto Mr Mark Nyam mai kula da al-amuran gaggawa na hukumar NEMA ta kasa ya bayyana cewa hatsarin ya auku ne a lokacinda direban motar daukar gas ya burma cikin wasu ababen hawa a kan gadar Karu wanda ya kai ga feshewar tankar gas da yake dauke da shi. Sannan nan da nan wutan ta watsu zuwa wurare da dama kusa da wurin.
Mark ya kara da cewa a halin yanzu dai jami’an tsaro da na ceto daban daban suna aikin tallafawa wadanda abin yashafa da kuma duk wanda yake bukatar taimako a wurin.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kenya: Zanga-zanga Ta Tsayar Da Kai Komo A Birnin Nairobi
Rahotanni da suke fitowa daga kasar ta Kenya sun ce tun safiyar yau Litinin ne ‘yan sanda su ka rufe muhimman hanyoyin da su ka nufi tsakiyar babban birnin kasar Nairobi da kuma muhimman cibiyoyin kasuwanci.
Kafafen watsa labarun kasar ta Kenya sun ce da akwai jami’an ‘yansanda masu yawa da aka girke su a cikin muhimman wurare da shatale-tale a cikin birnin da kuma hanyoyin da suka nufi fadar gwamnati.
Dubban mutane ne su ka fito titunan birnin Nairobi domin nuna kin amincewarsu da salon Mulki William Ruto wanda suke zargi da cin hanci da rashawa da kuma kama karya.
Zanga-zangar ta yau dai ana ba ta sunan; 7/7, wacce ta samo asali a 1990 da al’ummar kasar su ka yi Zanga-zangar gamagari ta yin kira da a gudanar da zabe cikin ‘yanci, da a karshe gwamnati ta amince da bukatar hakan.
A watan da ya shude na Yuni masu Zanga-zanga sun kutsa cikin ginin majalisar dokokin kasar da hakan ya tilastawa gwamanti ta janye dokar da ta yi akan harkokin kudade da haraji.