NAHCON Za Ta Fara Jigilar Alhazai Ranar 5 Ga Watan Mayun 2025
Published: 12th, March 2025 GMT
Hukumar Alhazai ta Kasa NAHCON ta fitar da sunayen kamfanonin jiragen sama da za su yi jigilar Alhazan bana.
Bayanin ya ƙunshi sunayen jiragen da kuma adadin mahajjatan da aka ware wa kowannensu.
Kamfanin Fly Nas zai yi jigilar Alhazai 22,893, kashi 32.12 bisa dari kenan na maniyyatan Najeriya a bana, yayin da Kamfanin Air peace ya sami Alhazai 9,145 , kashi 12.
Sauran su ne Max Air Ltd da aka warewa Alhazai 23,343, kashin 32.75 kenan bisa dari, sai kamfanin Umza Air Ltd an ware da ya sami 15,893 wato kashi 22.30 bisa 100, wanda ya kawo adadin maniyyata 71,274 da ake sa ran za su sauke farali a bana.
Hukumar ta NAHCON ta ce za a fara jigilar maniyyatan ne a ranar 5 ga Mayun 2025.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigilar Maniyyata
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan sanda sun gano zinaren N23m bayan shekara 12 da ɓacewarsu a Borno
’Yan sanda sun gano tare da miƙa wa wata mata zinarenta da kuɗinwu ta kai Naira miliyan 23 da suna ɓace a lokacin wani harin Boko Haram shekara 12 da suka gabata a Jihar Borno.
Jami’an tsaro da ke sintiri a kan iyakar Jihar Borno da Nijar ne suka gano kayan zinaren waɗanda suka haɗa da sarƙoƙi da sulallan zinariya a yankin Ƙaramar Hukumar Abadam.
Jami’an Ƙaramar Hukumar ne suka sanar a ranar Asabar a Malam Fatori cewa tsabar zinaren da aka gano, darajarsu ta kai Naira miliyan 23, mallakin wata uwa ce mai ’ya’ya shida.
Matar, wacce ke zaune a gaɓar Tafkin Chadi, ta ce, “A yau ina cike da farin ciki game da gano tsabar zinare na masu daraja da suka ɓace tun 2012, lokacin da ’yan Boko Haram suka ƙona gidaje da shaguna da yawa a cikin al’ummarmu.”
Ta jaddada cewa, “babu daga cikin zinare da aka samu ya ɓace ko ya lalace a lokacin mamayar Malam Fatori da ’yan ta’adda suka yi fiye da nawa.”
Wani babban jami’in Majalisar Ƙaramar Hukumar Abadam da ya sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, ya yaba wa ’yan sandan da aka tura don kare rayukan mutane da kadarorinsu a yankin Tafkin Chadi.
Bayan gano tsabar zinare na naira miliyan 23, jami’in ya lura cewa martanin ’yan sanda a ayyukan yaƙi da ta’addanci da ake ci gaba da yi wani abin karfafa gwiwa ne ga sojoji da sauran hukumomin tsaro a yankin Tafkin Chadi, wanda ya ƙunshi qananan hukumomi takwas da ke yankin.