Najeriya ta yi hasashen samun karuwar kashi 4.6 cikin dari na GDP a 2025
Published: 12th, March 2025 GMT
Gwamnatin Najeriya a ranar Talata ta bayyana fatanta na ganin tattalin arzikin kasar zai karu da a kalla kashi 4.6 cikin dari a shekarar 2025, daga kashi 3.19 a shekarar 2024.
Da yake kaddamar da wani cikakken tsarin tattalin arziki na samun ci gaba mai dorewa a babban birnin tarayyar Abuja, ministan kudi kuma mai kula da harkokin tattalin arzikin kasar, Wale Edun, ya ce har yanzu daidaita sassan tattalin arzikin kasa shi ne abin da aka fi sa a gaba, tare da samun daidaito a darajar musayar kudi, da rarar cinikayya, da karuwar samar da man fetur da ke sanya kasar a matsayin kasa mai karfi a duniya.
A sa’i daya kuma, hukumar kididdiga ta kasa a baya ta bayar da rahoton cewa, jimillar darajar kayayyakin cikin gida wato (GDP) ya karu da kashi 3.84 cikin dari a rubu’i na hudu na shekarar 2024, idan aka kwatanta da makamancin lokaci a 2023, inda jimillar ta karu daga kashi 3.46 a rubu’i na baya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kamfanonin Sin Sun Kera Tare Da Sayar Da Motoci Sama Da Miliyan 31 Tsakanin Janairu Zuwa Nuwamban Bana
Masana’antun kirar motoci na kasar Sin, sun samar tare da sayar da motocin da suka haura miliyan 31 cikin watanni 11 na farkon shekarar bana, wanda hakan ke shaida irin ci gaban da suka samu ta fuskar fitar da hajoji.
A cewar wasu alkaluma daga kungiyar kamfanonin kirar motoci na kasar Sin, tsakanin watan Janairu zuwa Nuwamban bana, adadin kirar motoci a Sin ya karu da kaso 11.9 bisa dari kan mizanin shekara, zuwa sama da motoci miliyan 31.23, yayin da alkaluman sayar da su ya karu zuwa kusan miliyan 31.13, wanda ya shaida karuwar kaso 11.4 bisa dari kan mizanin shekara.
Kazalika, alkaluman na watanni 11, sun shaida yadda yawan kirar motoci masu aiki da sabbin makamashi a kasar ya karu zuwa miliyan 14.907, karuwar da ta kai ta kaso 31.4 bisa dari, yayin da alkaluman sayar da su ya kai miliyan 14.78, wato karuwar kaso 31.2 bisa dari kan mizanin shekara. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
ADVERTISEMENT ShareTweetSendShare MASU ALAKA