Natasha ta yi ƙarar Akpabio a Majalisar Dinkin Duniya
Published: 12th, March 2025 GMT
Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya da aka dakatar, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta yi ƙarar Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Godswill Akpabio a Majalisar Ɗinkin Duniya.
Ta gabatar da kokenta a zaman taron mata da aka gudanar a hedikwatar Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) a birnin New York, inda ta nemi ƙungiyoyin kare dimokuraɗiyya na duniya su bi mata haƙƙinta.
Natasha, ta ce dakatar da ita daga Majalisar Dattawan Nijeriya da aka yi ba bisa ƙa’ida ba ne, kuma ta nuna damuwa kan cewa za a iya ƙoƙarin tsare ta saboda yin magana a fili.
Taƙaddamar da ke tsakanin Sanata Natasha da Sanata Akpabio ta ƙara tsanani bayan rigimar sauya mata wajen zama a zauren majalisa da ta faru a ranar 20 ga watan Fabrairu, 2025.
Ta zargi Akpabio da cin zarafinta da kuma amfani da muƙaminsa ta hanyar da ba ta dace ba, zarge-zargen da duk ya musanta.
Bayan lamarin ya yi ƙamari, Natasha ta maka Akpabio a kotu kan zargin ɓatanci, tana neman diyyar Naira biliyan 100.
A makon da ya gabata ne dai Majalisar Dattawan ta sanar da dakatar da Sanata Natasha Uduaghan tsawon watanni shida bayan kwamitin ladabtarwa na majalisar ya zarge ta da karya wasu daga cikin dokokinta.
Kwamitin ya yi zargin cewa Sanata Natasha ta yi magana ba tare da izini ba, kuma ta ƙi komawa sabon wurin zaman da aka sauya mata a zauren majalisar.
Har ila yau, an dakatar da albashinta da sauran haƙƙoƙinta na kuɗaɗe har tsawon lokacin dakatarwar, kuma an hana ta gabatar da kanta a matsayin Sanata.
Dambarwar Natasha da Akpabio na ci gaba da ɗaukar hankali a ciki da wajen Najeriya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: dakatarwa Ƙara Majalisar Dattawa Majalisar Ɗinkin Duniya a Majalisar
এছাড়াও পড়ুন:
Ronaldo Na Fuskantar Dakatarwar Wasanni Biyu Bayan Samun Jan Kati
Portugal ta shiga wasan ne da kwarin gwiwar cewa nasara za ta tabbatar mata da gurbin zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi a Amurka, Kanada da Mexico. Sai dai kwallaye biyu na Troy Parrott suka tarwatsa burinsu a Dublin. Duk da haka, Portugal har yanzu tana saman rukunin F da maki biyu a gaban Hungary, kuma za ta iya kammala tikitin shiga gasar idan ta doke Armenia a ranar Lahadi.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA