Rasha ta shirya daftarin dakile Shirin turai na mayar da takunkumin MDD kan Iran
Published: 27th, August 2025 GMT
Rasha ta tabbatar da tsara wani daftarin kudiri a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da nufin hana duk wani yunkuri na dawo da takunkuman MDD kan Iran da ke da alaka da batun shirinta na nukiliya, da ake kira da “snapback”.
Mataimakin wakilin dindindin na kasar Rasha a Majalisar Dinkin Duniya, Dmitry Polyanski ne ya bayyana hakan ga manema labarai yayin wani taron ‘yan jaria a wannan Talata.
Kasashen Turai uku na Birtaniya, Faransa, da Jamus abokan kawancen Amurka a yarjejeniyar nukiliyar Iran ta 2015, sun yi ta kokarin ganin an dawo da matakan kakaba wa Iran takunkumai bisa hujjar cewa bata yi aiki da yarjejeniyar ba kamar yadda aka rattaba hannu a kanta.
Wakilin na Rasha ya ce, duk da haka “Rasha da Sin suna son ba da sarari domin yin amfani da hanyar diflomasiyya tare da samar da wasu damammaki don neman mafita ta hanyar siyasa kan wannan batu.”
Ya ce Moscow da Beijing suna yin hakan ne a matsayinsu na “mambobin da ke da alhakin aiwatar da shirin na hadin gwiwa ko kuma yarjejeniyar nukiliyar Iran da aka fi sani da (JCPOA).
A shekara ta 2018, Amurka ta fice daga yarjejeniyar a wani mataki da ya sabawa doka da ka’ida ta kasa da kasa, tare da mayar da wasu takunkumanta a kan kasar ta Iran.
A nasu bangaren Kasashe uku na Turai Birtaniya, Faransa, da Jamus ba wai kawai sun gaza cika alkawarin da suka dauka ba ne, har ma sun bi sahun Washington ne ta hanyar mayar da nasu takunkumin da kokarin kawo cikas da yin tarnaki ga duk wasu harkokin tattalin arziki da suka shafi kasar Iran.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka ECOWAS na Shirin hada rundunar dakaru 260,000 domin yaki da ta’addanci August 27, 2025 Trump ya yi barazanar korar Gwamnar Babban Bankin Amurka August 27, 2025 Syria: Adadin mutanen da suka mutu a harin Isra’ila a yankin Damascus ya kai 5 August 27, 2025 An Kammala Taron Iran Da E3 A Geneva August 26, 2025 Iran Ta ce Zata Rama Kan Korar Jakadanta Daga kasar Australia August 26, 2025 Najeriya: Jirgin Kasa tsakan Abuja da Kaduna Ya Sauka Kan Layin Dogo August 26, 2025 Iran A Shirye Take Ta Hada kai Da Pakistan Don Kawo Karshen Ayyukan Ta’addanci August 26, 2025 An Kashe Mutum Guda A Harin Isra’ila (HKI) A yankin Duddan Golan Na Siriya August 26, 2025 Jagora: Yahudawan Sahayoniyya Sune Mafi Kyamar Al’umma A Duniya Saboda Muggan Halayensu August 26, 2025 Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Tarihi Ba Zai Yafe Jinkirin Yin Allah Wadai Da Bala’in Gaza Ba August 26, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: a yarjejeniyar
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kasar Iran Ya Gana Da Sarkin Kasar Qatar A Birnin Doha
Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan wanda yake halartar taron brinin Doha, na kasashen musulmi da larabawa, ya gaba da sarkin Qatar Tamim Bin Hamad ali-Thani, inda su ka tattaunawa halin da ake ciki a wannan yankin na yammacin Asiya.
Taron na Doha ne na gaggawa ne wanda aka shriya shi, domin tattauna harin wuce gona da iri da HKI ta kai wa kasar Qatar a wani yunkurin yi wa shugabannin Falasdinawa kisan gilla.
A yayin wancan harin dai, ‘yan sahayoniyar sun harba makamai masu linzami fiye da 10 akan wani gini wanda jami’an kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas suke taro a ciki.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Dan Kasar Iran Mai Kirkira Ya Sami Kyautar Yabo A Kasar China September 15, 2025 Fizishkiyan: Wajibi Ne Musulmi Su Hada Kai Domin Dakatar Da Laifukan HKI September 15, 2025 Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Qatar, Turkiyya, Pakistan Da Labanon A Doha September 15, 2025 Kwamitin Kolin Tsron Kasar Iran Ya Amince Da Yarjejeniyar Da Aka Cimma Da Hukumar IAEA September 15, 2025 Jami’in Kasar Yemen Ya Aike Da Sako Ga Mahalarta Taron Birnin Doha Na Kasar Qatar September 15, 2025 Yawan Mutanen Da Suka Yi Shahada Sakamakon Kisan Kiyashin ‘Yan Sahayoniyya A Gaza Ya Kusaci 65,000 September 15, 2025 Gwamnatin Sudan Ta Ce: Babu Sulhu Da ‘Yan Tawayen Kasar Na Kungiyar Rapid Support Forces September 15, 2025 Kasashen Larabawa da na Musulmi na taron gaggawa kan harin Isra’ila a Qatar September 15, 2025 Hamas ta bukaci kasashen musulmi da na Larabawa su dauki mataki mai tsari kan Isra’ila September 15, 2025 Rabin Sojojin Isra’ila da suka ji rauni a yakin Gaza na fama da ciwon damuwa September 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci