Iran ta soki matakin Amurka na hana shigar da wutar lantarki Iraki
Published: 11th, March 2025 GMT
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya soki matakin da sabuwar gwamnatin Amurka ta dauka na janye sassaucin da ta yi wa Iraki na shigo da wutar lantarki daga Iran.
Araghchi ya bayyana matakin da gwamnatin Trump ta dauka a matsayin “abin takaici.”
Ya kara da cewa gwamnatin Amurka ta na kokarin hana al’ummar iraki samun ababen more rayuwa kamar wutar lantarki, musamman gabanin watanni masu zafi na wannan shekara.
Babban jami’in diflomasiyyar Iran ya sake jaddada goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ga al’ummar Iraki.
Ya kara da cewa Iran ta tsaya tsayin daka kan kudurin ta ga gwamnatin Iraki na dakile ayyukan Amurka da suka sabawa doka.
Kalaman Araghchi sun zo ne bayan da Amurka ta sanar da janye sassaucin da ta yi wa Iran wanda ya bai wa Iraki damar shigo da wutar lantarki daga makociyarta ta gabas.
A martaninsa, shugaban kwamitin kudi na majalisar dokokin Iraki ya yi gargadin cewa duk wani mataki da Washington za ta dauka na takaita shigo da wutar lantarki daga Iran zai haifar da rugujewar wutar lantarki a Iraki.
A halin yanzu, kusan kashi 80 cikin 100 na makamashin da ake samu a Iraki ya dogara ne da iskar gas, wanda hakan ya sa kasar ta dogara sosai da Iran don ci gaba da samar da wutar lantarki.
A watan Yulin 2022, Iraki ta sanya hannu kan kwangilar shekaru biyar da Iran don samar da megawatt 400 na wutar lantarki.
A watan Maris din shekarar 2024, an cimma wata yarjejeniya ta kara yawan iskar gas din Iran zuwa mita cubic miliyan 50 a kowace rana, wanda darajarsa ta kai dala biliyan 6 a duk shekara.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: da wutar lantarki
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Shirya Fara Tantance ‘Yan Fansho
Hukumar Fensho ta Jihar Jigawa da Kananan Hukumomin jihar ta shirya fara aikin tantance ‘yan fansho da ke cikin tsarin.
Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, Alhaji Muhammad K. Dagaceri ne ya bayyana haka yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Gidan Fansho, inda shugabannin kungiyar ‘Yan Fansho ta Najeriya reshen Jigawa suka halarta.
A cewarsa, an shirya fara aikin tantancewar ne daga ranar Litinin, 5 ga Mayu, 2025.
Alhaji Dagaceri ya bayyana cewa, an shirya hakan ne da nufin sabunta tsarin biyan fansho tare da tabbatar da ingancin bayanai.
Ya ce, aikin tantancewar zai gyara wasu ‘yan kura-kurai da suka kunno kai a cikin shekaru uku da suka gabata, da kuma tabbatar da ingantattun bayanai a jadawalin biyan fansho.
Ya kara da cewa, wannan yunkuri ya yi daidai da kudirin jihar gwamnati na tabbatar da gaskiya da rikon amana a harkokin mulki, tare da bai wa ‘yan fansho dama su gyara duk wani bayanin da bai cika ba a takardunsu.
Shi ma da ya ke jawabi, Akanta Janar na Jihar, Alhaji Abdullahi S.G. Shehu, ya jaddada cewa aikin tantancewar zai bai wa ‘yan fansho damar sabunta bayanansu da suka bace ko suka canza a takardunsu.
Saboda haka, ya bukaci dukkan ‘yan fansho daga ma’aikatun gwamnati, sassan hukumomi, kananan hukumomi da kuma hukumomin ilimi na kananan hukumomi da su halarci tantancewar a ranar da aka tsara kamar yadda yake cikin jadawalin aikin.
A jawabinsa, Shugaban kungiyar kananan hukumomi ALGON ta Jihar Jigawa, Farfesa Salim Abdurrahman, ya tabbatar da cikakken goyon baya daga shugabannin kananan hukumomi 27 domin cimma burin aikin.
Shugaban na ALGON wanda shugaban karamar hukumar Malam Madori, Alhaji Salisu Sani ya wakilta, ya bukaci ‘yan fanshon da su ba da cikakken haɗin kai don samun nasarar shirin.
Shi ma Shugaban hukumar, Dr. Bilyaminu Shitu Aminu, ya bukaci ‘yan fansho daga sassa daban-daban da su ba da hadin kai domin cimma burin da aka sanya, tare da jaddada cewa su ziyarci sakatariyar kananan hukumominsu domin a tantance su.
Shugaban Kungiyar ‘Yan Fansho ta Najeriya reshen Jihar Jigawa, Alhaji Umar Sani Babura, ya yi alkawarin cewa kungiyar za ta bada cikakken goyon baya domin nasarar wannan shiri.
Dukkan ‘yan fansho daga Ma’aikatun Gwamnati, Kananan Hukumomi, da Hukumomin Ilimi na Kananan Hukumomi da ke cikin tsarin fanshon, ya zama wajibi su halarci wannan tantancewa a ranakun da aka tsara a jadawalin aikin.
Usman Muhammad Zaria