Kasar Sin Ta Mayar Da Martani Kan Kalaman Sakataren Baitul Malin Amurka
Published: 11th, March 2025 GMT
Sakataren baitul malin Amurka Scott Bessent ya sha nanata cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya dogara a kan kayayyakin da ake fitarwa zuwa kasashen ketare fiye da kima, kuma Amurka na neman yin ciniki bisa adalci da daidaito. Sai dai kuma, da yake mayar da martani a yau Litinin 10 ga watan Maris, yayin wani taron manema labaru na yau da kullum, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mao Ning ta yi nuni da cewa, maganar da ake yi a kullum kan “rasa madafa” da neman cikakken daidaiton cinikayya ta saba wa ilimin tattalin arziki na asali, da yin watsi da hukunci da muradun kamfanoni da masu sayayya na Amurka.
Mao Ning ta ce, halin da ake ciki na cinikayya a tsakanin Amurka da kasar Sin yanzu haka ya samo asali ne sakamakon rawar da kasuwanni ke takawa, kuma abubuwa da dama sun shafi tsarin tattalin arzikin kasashen biyu,da manufofin ciniki da kuma matsayin dalar Amurka.
Ta kara da cewa, kasar Sin ba ta taba neman cin bulus da gangan ba. Hasali ma, Amurka ce ta fi tsintar dami a kala daga cinikayyarta da Sin. Mao Ning ta jaddada cewa, ba a sauya wa tuwo suna, domin ko ta yaya Amurka ta sauya akalar abin, ba za ta iya boye yunkurinta na siyasantarwa da mayar da batutuwan tattalin arziki da cinikayya a matsayin makamin dakilewa da neman murkushe kasar Sin ba. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
AA Zaura Ya Yi Kira Ga ’Yan Nijeriya Su Marawa Sauye-sauyen Shugaba Tinubu Baya
Daya daga cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kuma ɗan kasuwa mai taimakon al’umma, Abdussalam Abdulkarim Zaura, wanda aka fi sani da AA Zaura, ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su ba da cikakken goyon bayansu ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai bayyana kwarin gwiwa cewa shugaban na da kwarewa da hangen nesa wajen farfado da tattalin arzikin ƙasar da inganta jin daɗin jama’a.
Zaura ya yi wannan kiran ne lokacin da wata tawaga daga Tinubu/Shettima Campaign Group ta kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa, inda ya jaddada cewa haɗin kan ’yan Nijeriya na da matuƙar muhimmanci domin samar da ci gaba mai ɗorewa da kuma tabbatar da matsayi irin na ƙasashen da ke da ƙarfafa tattalin arziki da ingantaccen rayuwa.
“Ina kira ga ’yan Nijeriya da su marawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya domin ya ja-goranci Nijeriya zuwa sahun ƙasashen da ke da ƙarfi a tattalin arziki da kuma sauƙin rayuwa a duniya,” in ji Zaura.
Jigon na APC, wanda ya shahara wajen ayyukan taimako da shirye-shiryen ƙarfafa matasa, ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin da Shugaba Tinubu ke aiwatarwa yanzu, duk da cewa suna da kalubale a farkon lokaci, suna da nufin gina tattalin arzikin ƙasar ne bisa tubalin ƙirƙira, gaskiya da ɗorewar ci gaba.
Ya ce matakan da gwamnati ta ɗauka, irin su cire tallafin man fetur da sake fasalin harkar musayar kuɗi (forex reform), muhimman matakai ne da za su taimaka wajen gyara matsalolin tsari da aka dade da fama da su, tare da shirya ƙasar don samun bunƙasar tattalin arziki a nan gaba.
“Duk wata babbar ƙasa ta fuskanci lokacin sauye-sauye kafin ta kai matsayin da ta samu kwanciyar hankali da ci gaba. Abin da ake buƙata a yanzu shi ne haƙuri, haɗin kai da amincewa da hangen nesan gwamnati,” in ji shi.
Zaura ya kuma shawarci shugabannin siyasa, kungiyoyin farar hula da masu zaman kansu da su haɗa kai da gwamnati wajen aiwatar da shirinta na ci gaba maimakon siyasantar da kalubalen da ke tattare da sauye-sauyen.
A cewarsa, gwamnatin Tinubu ta mayar da hankali ne wajen ƙirƙirar ayyukan yi, bunƙasa noma, ƙarfafa kirkire-kirkiren fasaha (digital innovation), da kuma zuba jari a fannin gine-gine da ababen more rayuwa, a matsayin dabarar rage talauci da ƙarfafa tattalin arzikin jama’a, musamman matasa da mata.
Ya ƙara da cewa ’yan Nijeriya su ci gaba da kasancewa masu ƙwarin guiwa da juriya, yana mai bayyana cewa shirin gwamnati na sake fasalin tattalin arziki zai fara haifar da sakamako mai gamsarwa nan ba da jimawa ba.
Zaura ya sake jaddada goyon bayansa ga gwamnatin APC, yana bayyana Shugaba Tinubu a matsayin jagora mai hangen nesa da ƙarfin gwiwa wajen ɗaukar matakan da za su dawo da ƙasar kan turbar ci gaba.
“Jagoranci ba na jin daɗi ba ne, amma na ƙarfin hali — ƙarfin hali na ɗaukar matakai masu wahala don amfanin jama’a na dogon lokaci. Ina da tabbacin Shugaba Tinubu yana da wannan ƙarfin hali, kuma da goyon bayanmu, Nijeriya za ta fi ƙarfafa,” in ji shi.
Ya kuma jaddada aniyar sa ta ci gaba da tallafawa ƙoƙarin gwamnati ta hanyar aikin sa na gidauniyar taimako, wadda ke aiwatar da shirye-shirye a fannin ilimi, kasuwancin zamani (digital entrepreneurship) da ƙarfafa matasa, wanda ya bayyana a matsayin ginshiƙi wajen gina ƙasa mai ɗorewa da dogaro da kai.
Zaura ya kuma yi kira ga ’yan Nijeriya daga kowane bangare da su fifita zaman lafiya, haɗin kan ƙasa da tattaunawa mai ma’ana wajen shawo kan matsalolin tattalin arziki da zamantakewa.
“Mu daina kallon bambance-bambance, mu haɗa kai don cigaban ƙasarmu mai albarka. Nijeriya tana da cikakken damar zama ƙasa mai girma, kuma ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu, wannan mafarki zai tabbata,” in ji Zaura.