Yadda za a samu rufin asiri da sana’ar ɗinki — Muhammad
Published: 10th, March 2025 GMT
Wani matashi mai sana’ar ɗinki, Malam Muhammad Sani Tela ya bayyana cewar, ya shafe fiye da shekara 30 ya na ɗinki.
Ya ce wannan sana’a ta zama tamkar jini da tsoka a gare shi sakamakon yadda ya riƙe ta da hannu bibbiyu.
Ko dai Gwamna Fubara ya yi murabus ko a tsige shi — APC An cafke mutum uku kan satar wayoyin lantarki a AdamawaYa ƙara da cewar, wannan sana’a ta ɗinki sana’a ce da ke da matuƙar albarka idan ka sa juriya a ciki domin kuwa ba sana’a ce da za ka tara kuɗi akai-akai ba nan take.
“Sai dai kuma muddin ka tsayar da gaskiya tare da cika alƙawari to lalle za ka samu babban rufin asirin da baya misaltuwa domin kuwa a kullum in ka fito to kuwa za ka samu abin da za ka yi cefanen gidan ka da sauran buƙatu.
A cewarsa, ya samu fa’ida sosai a wannan sana’a ta ɗinki, domin a cikin ta ya yi aure har ma da ‘ya’ya da sauran kadarori.
“Alhamdulillah, kuma babu abin da ya taimaka min na cimma nasara fiye da jajircewa a kanta.
“Kamar kowace sana’a ita ma sana’ar ɗinki t na da nata irin ƙalubalen domin kamar a shekarar da ta shude sakamakon matsalar rayuwa da al’umma suka samu kansu ciki sai da ta kai ga wannan sana’a ta mu ta samu tasgaro na rashin samun ɗinki.
“Domin lokacin ba ta kayan sawa ake yi ba, jama’a na fafutukar abin da za a ci ne ba’a batun ɗinka sutura.
“Amma a bana lamarin sai godiya domin ya kasance muna ɗinkin sosai idan an kwatanta da shekarun baya.
“Saboda yadda ake samun ɗinki tuni mun rufe karɓar ɗinkin sallah sakamakon al’umma sun fara dawowa hayyacin su saboda sauƙin rayuwa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: wannan sana a ta
এছাড়াও পড়ুন:
Kwamishinan Abba ya yi murabus bayan watanni 7 da naɗinsa
Manjo-Janar Muhammad Inuwa Idris mai ritaya, Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Ayyuka na Musamman na Jihar Kano, ya yi murabus.
Wannan dai na zuwa ne bayan shafe watanni bakwai kacal da karɓar muƙamin.
Sakataren Labarai na Fadar Gwamnatin Kano, Mustapha Muhammad ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Larabar.
Sanarwar ta ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da murabus ɗin Kwamishinan yana kuma yaba masa kan ƙwazon da ya yi wajen sauke nauyin da aka ɗora masa.
Kazalika, gwamnan yana yi wa Manjo-Janar Idris fatan samun nutsuwa da kwanciyar hankali a ritayar da ya yi.
Aminiya ta ruwaito cewa tun a ranar 16 ga watan Agustan bara ne aka rantsar da Manjo-Janar Muhammad Inuwa a matsayin kwamshinan, amma sai kimanin watanni biyar da suka gabata ne aka ƙirƙiro sabuwar ma’aikatar wacce aka danƙa ragamarta a hannunsa.