Tsohon Mataimakin Gwamnan Kogi Patrick Adaba ya rasu
Published: 10th, March 2025 GMT
Tsohon Mataimakin Gwamnan Kogi, Cif Patrick Adaba ya riga mu gidan gaskiya.
An ruwaito cewa Cif Adaba wanda ya shafe shekaru 78 a doron ƙasa ya rasu ne bayan ya yi fama da jinya a Abuja.
Abba ya ƙaddamar da bincike kan zaftare albashin ma’aikatan Kano Blatter da Platini sun sake gurfana a kotu kan zargin cin hanciWata majiya daga iyalansa ta ce tsohon Mataimakin Gwamnan ya rasu ne cikin daren ranar Lahadi.
Cif Patrick Adaba shi ne ya yi wa Prince Abubakar Audu mataimakin gwamna bayan samun nasara a Zaɓen 1999.
Tsohon Mataimakin Gwamnan wanda ya fito daga Ƙaramar Hukumar Adavi da ke Jihar Kogin, ƙani ne ga tsohon Darekta Janar na Hukumar Kula da Kafofin Watsa Labarai (NBC), marigayi Tom Adaba wanda ya rasu a watan jiya na Fabarairu.
Majiyar ta ce za a binne gawar marigayi Patrick Adaba a Abuja, inda aka binne yayan nasa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Hukumar NBC Jihar Kogi mataimakin gwamna Mataimakin Gwamnan
এছাড়াও পড়ুন:
Zargi: ’Yan sanda sun musanta sace tsohon Kwamishinan El-Rufai
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta ƙaryata zargin da Tsohon Gwamna Nasir El-Rufai ya yi cewa jami’an tsaro sun sace tsohon Kwamishinansa, Jafaru Sani.
El-Rufai ya yi wannan iƙirari ne a shafinsa na sada zumunta cewa an ɗauke tsohon Kwamishinan kamar fursuna ba tare da bin ƙa’idojin doka ba.
Direba ya murƙushe yarinya ta mutu a artabu da jami’an tsaro a Edo Cutar sanƙarau ta kashe sama da mutum 50 a Sakkwato da KebbiYa yi zargin cewa wata “ƙungiyar masu garkuwa da mutane” da ke da alaƙa da Gwamna Uba Sani ce ke da alhakin ɗauke tsohon Kwamishinan.
Da yake mayar da martani, kakakin ’yan sandan jihar, DSP Mansir Hassan, ya bayyana zargin a matsayin ƙarya.
“Babu wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane a cikin Rundunar ’Yan Sandan Najeriya.
“Mu hukuma ce da ke aiki bisa kundin tsarin mulki don tabbatar da doka da oda,” in ji shi.
Ya buƙaci ’yan siyasa su guji yaɗa labaran da ba su da tushe.
“Yi wa jami’an tsaro ƙarya na iya haifar da ruɗani da kuma rage martabarsu. Idan mutum yana da ƙorafi, ya bi hanyar shari’a maimakon yaɗa kalaman da za su tayar da fitina,” a cewarsa.