Kano Pillars Ta Koma Ta 4 A Teburin Firimiyar Nijeriya
Published: 3rd, March 2025 GMT
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars wacce ake wa laƙabi da Masu Gida ta doke abokiyar karawarta Enugu Rangers da ci 2-1 a filin wasa na Sani Abacha dake Kano.
Wasan wanda aka fara da karfe 4 na yammacin ranar Lahadi, ya na daga cikin manyan wasanni masu zafi da ke ɗaukar hankalin masu sha’awar ƙwallon ƙafa a Nijeriya.
Rabiu Ali da Jerry Alex ne su ka jefa wa Pillars ƙwallayensu biyu a wasan, da wannan sakamakon Sai Masu Gida su ka koma matsayi na 4 akan teburin gasar Firimiyar Nijeriya.
Ƙungiyar ta Kano ta dakatar da kocinta Usman Abdallah, inda mataimakinsa Ahmed Garba Yaro Yaro ya jagorance ta a wasanni uku na baya bayan nan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Enugu Rangers Kano Pillars
এছাড়াও পড়ুন:
An gano gawawwakin mata uku ’yan Kamaru da aka sace a Anambra
Rundunar ’yan sandan Jihar Anambra ta gano gawar wasu mata uku ’yan ƙasar Kamaru da ake zargin waɗanda suka yi garkuwa da su domin neman kuɗin fansa sun kashe su.
Haka kuma, rundunar ta ce ta kama wasu mutum biyu da ake zargi da hannu a lamarin, Nonso Augustine Akpeh da Kingsley Akpeh, waɗanda ake zargin suna cikin gungun masu garkuwar da suka sace matan.
Wata mata ta kashe ’yar shekara 7 a Ribas El-Rufai ya koma jami’yyar haɗaka ta ADCTun dai a ranar Litinin, 10 ga watan Nuwamban nan ne aka sace matan a garin Anam da ke Jihar Anambra, inda suka saba zuwa sayen kayayyakin kasuwanci.
Jami’an rundunar na sashen yaki da masu garkuwa da mutane da ke Awkuzu ne suka kai wani farmaki, inda aka yi musayar wuta tsakaninsu da masu garkuwar.
A yayin bincike, an gano makamai iri-iri, ciki har da bindiga mai sarrafa kanta da bindigogi ƙirar hannu da kuma harsasai.
Kakakin rundunar, SP Tochukwu Ikenga, ya shaida wa Aminiya cewa dangin matan ne suka kai rahoton bacewar su tun a ranar 13 ga Nuwamba, bayan sun gaza komawa gida daga kasuwar Anam, inda suka saba zuwa.
SP Ikenga ya ce masu garkuwa sun fara neman kuɗin fansa har Naira miliyan 50, amma bayan an yi ciniki suka amince a biya Naira miliyan 2.9.
Sai dai a cewar SP Ikenga, masu garkuwar sun kashe matan duk da ’yan uwan waɗanda abin ya shafa sun biya kuɗin fansar.
A cewar SP Ikenga, wani cikin waɗanda ake zargin ne ya jagoranci jami’an ’yan sanda zuwa dajin da ake ɓoye waɗanda aka sace, inda a can ne aka gano wurin da ake jefar da gawawwakin nasu.
A yayin binciken ne ɗaya daga cikin ababen zargin ya yi yunƙurin tserewa, amma jami’an suka sake cafke shi.
Mazauna yankin da ke kusa da dajin sun tabbatar wa ’yan sanda cewa wurin ya shahara wajen jefar da gawar mutanen da masu garkuwa da mutane ke kashewa.
Rundunar ’yan sandan ta ce bincike zai ci gaba da gudana, kuma za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala.