HausaTv:
2025-09-17@23:26:41 GMT

Araghchi : Iran Ba Za Ta Shiga Tattaunawa Da Amurka Bisa Matsin Lamba

Published: 26th, February 2025 GMT

Iran ta bayyana cewa ba zata shiga wata tattaunawa da Amurka ba kan shirinta na nukiliya bisa matsin lamba.

Ministan harkokin wajen Iran ne Abbas Araghchi ya bayyana hakan, inda yake cewa muddin fadar White House ba ta janye matsin lamba wa kasar ba, babu wata tattaunawa.

“A kan tattaunawar nukiliya, matsayin Iran a bayyane yake: ba za mu yi shawarwari cikin matsin lamba, barazana, da takunkumi ba.

“Saboda haka,” in ji ministan harkokin wajen Iran, “babu yuwuwar yin shawarwari kai tsaye tsakaninmu da Amurka kan batun nukiliya matukar dai ana ci gaba da yin amfani da mafi girman matsin lamba a yadda take a halin yanzu.”

Misra Araghchi ya bayyana hakan ne a yayin  wani taron manema labarai da takwaransa na Rasha, Sergey Lavrov da ke ziyara a Tehran.

Ministan harkokin wajen kasar ya ce Iran za ta magance batun nukiliyar tare da hadin gwiwa da kawayenta – Rasha da China.

A nasa bangare da yake bayyani game da shirin nukiliyar Iran, Lavrov ya ba da fifiko kan hanyar diflomasiyya.

“Mun yi imanin cewa har yanzu akwai karfin diplomasiyya don warware batun nukiliyar Iran, kuma muna fatan za a iya samun mafita. Ba Iran ce ta haifar da wannan rikicin ba.” Inji shi.

Iran dai ta dade tana fuskantar takunkumin da kasashen yamma suka kakaba mata kan ayyukanta na nukiliya, da batun kare hakkin bil’adama, da dai sauransu, saidai zuwan Donald Trump, ya kara dagula al’amuran inda ya sha alwashin matsin lamba kan kasar ta Iran, domin ta mika wuya.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

‘Yansanda Sun Kama Mutane 6 Kan Zargin Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Neja

 

A yayin samamen, kakakin ‘yansandan Neja ya ce an kama mutane shida a wurin da ake hakar ma’adinan yayin da wasu kuma suka tsere.

 

Abiodun ya bayyana sunayen wadanda ake cafken da Aliyu Rabiu, Samaila Ibrahim, Sadiku Auwal, Ibrahim Babangida, Musa Adamu da Sani Hassan.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘Yansanda Sun Kama Mutane 6 Kan Zargin Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Neja
  • Har Kullum Burin Sin Shi Ne Wanzar Da Daidaito Da Cimma Moriya Tare Da Amurka
  • ALGON ta karrama Gwamna Buni da lambar yabo kan kawo ci gaba a Yobe
  • Iran Ta Gabatar Da Sabbin Kayayyaki Guda 5 A Wajen Taron Kolin kere-kere .
  • Baqa’i: Kowace Kasa A Duniya Tana Da Hakkin Mallakar Makamashin Nukiliya Na Zaman Lafiya
  • Jonathan Zai Jagoranci Taron Tattaunawa Kan Dimokuraɗiyya A Ghana
  • Ministan Tsaron Kasar venezuela Ya Gargadi Amurka Dangane Da Kokarin Juyin Mulki A Kasar
  • Tawagogin Sin Da Na Amurka Sun Sake Tattaunawa Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya A Rana Ta Biyu
  • Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Dakatar Da Shuka Kiyayya Da Tashin-Tashina A Tekun Kudancin Sin
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Qatar, Turkiyya, Pakistan Da Labanon A Doha