Ana nuna damuwa akan karancin kayan gwajin HIV a Taraba
Published: 14th, February 2025 GMT
Kungiyoyin farar hula masu yaki da zazzabin cizon sauro, rigakafi da abinci mai gina jiki (ACOMIN), reshen jihar Taraba, ta koka kan matsalar karancin kayan gwajin cutar kanjamau a jihar.
Shugaban kungiyar na jiha, Alhaji Muhammad Danburam ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyarar wayar da kan hukumar yaki da cutar kanjamau ta Taraba (TACA), ofishin kula da magunguna masu muhimmanci, da gidauniyar REDAID Nigeria Foundation.
Danburam ya bayyana cewa, wani bincike da aka yi kwanan nan a wasu cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko guda 18 a kananan hukumomin Ardo-kola, Bali, da Takum, ya nuna cewa kayan gwajin cutar kanjamau sun kare a cibiyoyin.
“Rashin kayan gwajin zai kawo cikas ga kokarin yaki da yaduwar cutar kanjamau a jihar,” in ji Danburam.
Ya yi kira ga gwamnatin jihar da masu ruwa da tsaki da su dauki matakin gaggawa don magance karancin.
A jawabinsa, Ko’odinetan Sashen Gudanar da Dabaru (LMCU) na Jiha, Pharm. Pinkai Bade, ya bukaci ‘yan kasar da su jajirce wajen tabbatar da samar da wadannan kayyakin tare da bayyana cewa tsarin samar da kayayyaki na da matukar kalubale sakamakon dakatar da tallafin da Amurka ke ba Najeriya.
Ya kuma yi nuni da cewa, Nijeriya ta himmatu wajen ganin an cike gibin da ke tattare da cutar kanjamau da kuma cimma nasarar rigakafin kamuwa da cutar daga uwa zuwa yara (PMTCT) nan da shekarar 2030.
Hukumar kula da fasaha ta REDAID ta Najeriya, Mista Stanley Nfor, da sakataren hukumar yaki da cutar kanjamau ta Taraba (TACA), Mista Bala Zugyeri, sun bayyana cewa, masu hannu da shuni kadai ba za su iya biyan bukatar kayayyakin gwaji da sauran muhimman kayayyaki ba, inda suka jaddada bukatar tallafin gwamnati.
Karshe/Jamila Abba/Wababe
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Taraba cutar kanjamau kayan gwajin
এছাড়াও পড়ুন:
Kungiyar ‘Yan Dako Ta Kasa Ta Nada Sabon Sakatare A Jigawa
Kungiyar ‘Yan Dako ta kasa reshen jihar Jigawa ta kaddamar da Malam Muhammad Tajudeen Maigatari a matsayin sakataren kungiyar na jihar.
Da yake jawabin a lokacin bikin kaddamawar a garin Maigatari, Shugaban kungiyar na jihar Malam Nasiru Idris Sara, ya bayyana shugabanci a matsayin rikon amana a maimakon hanyar tara dukiya da alfahari, a don haka akwai bukatar sakataren ya yi aiki tukuru dan kare martabar sana’ar dako da masu yin ta.
Yana mai cewar shugabancin kungiyar zai hada kai da shugabannin kananan hukumomi da masu rike da sarautu da jami’an tsaro a matsayin abokan kawo cigaba wajen daga likkafar sana’ar dako.
Nasiru Idris Sara ya kuma yi kira ga daukacin ‘yan dako a fadin jihar da su yi rijista da kungiyar domin kasacewa a karkashin inuwa daya ta yadda za su ci moriyar tanade tanaden ta, sannan su kasance masu mutunta shugabanci da kuma bin doka da oda domin inganta rayuwar su.
Ya ce yayin da kungiyar ta ke da ‘yan dako kimanin dubu 20 a karkashin ta, akwai bukatar duk ‘yan dakon da ba su da katin zabe su karbi sabo ko kuma su sabunta wanda ya bata ko ya lalace domin amfani da damar su wajen zaben shugabanni.
A sakon sa, Hakimin Maigatari Alhaji Sani Alhassan Muhammad wanda ya sami wakilcin Sarkin Kasuwar Maigatari Alhaji Muhammadu Sarkin Kasuwa, ya bukaci sabon sakataren kungiyar Malam Muhammad Tajudeen ya kasance mai nuna gaskiya da adalci wajen huldar sa da ‘yan dako da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin kasuwanci, inda ya bayyana murnar samun wannan mukamin.
Cikin wadanda suka halarci taron sun hada da Sarkin hatsin Maigatari, Malam Mu’azu Bako da Shugaban leburorin Dingas na Jamhuriyar Nijar Malam Lawwali Hassan.
Usman Mohammed Zaria