Sai dai kuma, bayan bayyana a taron da gwamnonin tafkin Chadi suka yi a Borno na cewa, tubabbun ‘yan ta’adda sama 5000 ne suka sake haduwa da iyalansu, Jabi ya ce; babu shakka wannan wani cin fuska ne ga fuskokin wadanda aka kashe da kuma jaruman sojojin da suka mutu.

Haka nan, ya kuma sake bayyana hadewar komawar tasu cikin al’umma a matsayin wani babban kuskure wajen aiwatar da manufofin da suka dace.

Ya kara da cewa, “Abin da ya kamata mu yi wa ‘yan ta’adda shi ne, mu tabbata sun girbi abin da suka shuka. Saboda haka, idan har da gaske muke wajen kawar da ta’addanci a fadin wannan kasa, ya kamata mu sanya ido yadda ya kamata. Bana goyon bayan wannan abu da ake kira; sake shigar da ‘yan ta’adda cikin al’umma da siyasa.

“Wannan ba daidai ba ne, kuskure ne. Wadannan mutane, babu wani ci gaba da za su kawo wa kasa ko al’ummar da ke cikinta, in ban da kara dagula al’amura da za su yi”, a cewarsa.

Jabi ya ci gaba da cewa, sakamakon ayyukan ‘yan ta’adda, manoman da ya kamata a ce suna samar wa al’umma abinci; suna can sansanonin ‘yan gudun hijira suna rayuwa cikin mawuyacin hali.

Wani dan asalin Jihar Yobe, wanda ba ya so a bayyana sunansa, saboda fargabar ramuwar gayya; ya nuna rashin jin dadinsa ga gwamnatin tarayya da na jihohi, dangane da shirin sake dawo da wadannan ‘yan ta’adda cikin al’umma.

Ya ce, kyautuwa ya yi gwamnatin tarayya a ce tuni ta kammala fatattakar wadannan ‘yan ta’adda, kafin ta kai ga fara aiwatar da wannan shi.

Shi ma a nasa vangaren, babban daraktan cibiyar kare hakkin al’umma (CISLAC), Auwal Musa Rafsanjani ya ce, mayar da ‘yan ta’addan da suka tuba, ba tare da sake tsugunar da wadanda ta’addacin ya shafa ba, abu ne da zai tava samun karvuwa ba.

Don haka, ya yi kira ga gwamnati da ta gurfanar da duk wadanda suka taka rawa wajen cin zarafin al’umma tare da tabbatar da adalci.

Sanusi Isa, daraktan kungiyar ‘Amnesty International’ ta kasa, shi ma ya yi magana makwatankwaciyar wannan, inda ya yi nuni da cewa, duk wadanda suka aikata laifuka; su fuskanci hukunci na gaskiya.

Sannan ya kara da cewa, dukkanin wadanda abin ya shafa da wadanda suka tsira da iyalansu, sun cancanci a yi musu adalci.

daya daga cikin Shugabannin al’ummar Chibok, Mutah Nkeki, ya bayyana ra’ayinsa a matsayin rashin adalci da gwamnati ta shirya a kan ‘yan asalin Chibok da sauran daukacin wadanda ta’addancin ya shafa.

Ya yi zargin cewa, ‘yan matan makarantar Chibok da Boko Haram suka sace a shekarar 2014, an hana su ganawa da shugabanni da kuma iyayensu, tun bayan da suka tsere daga hannunsu.

Har ila yau, ya kara da cewa, babban abin takaicin shi ne, faruwar lamarin ya jawo mutuwar iyaye dama, inda y ace wadanda ke raye; ba a bas u damar ganin ‘ya’yansu mata da suka kuvuta ko aka kuvutar da su ba.  

Da aka tuntuvi kwamishinan yada labarai da tsaron cikin gida na Jihar Borno, Farfesa Usman Tar; ya musanta dukkanin zarge-zargen.

Ya ce, savanin zargin da ake yi; gwamnati jihar ta bayar da makudan kudade, domin sake tsugunar da al’umma.

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Tsaro yan ta adda

এছাড়াও পড়ুন:

Pezeshkian: Bunkasa Masana’antar Makamashin Nukiliyar Iran Don Inganta Rayuwar Al’ummar Iran Ne

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Faɗaɗa masana’antar makamashin nukiliyar Iran don inganta rayuwar mutanen kasar ne, ba don makamai ba

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya gana da manyan jami’ai a masana’antar makamashin nukiliya ta ƙasar a lokacin ziyarar da ya kai Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran (AEOI).

Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Masoud Pezeshkian, ya ziyarci AEOI a ranar Asabar da yamma, inda ya gana da wasu manyan jami’ai a masana’antar makamashin nukiliyar.

A yayin taron, Shugaba Pezeshkian ya jaddada cewa: Abin takaici, farfagandar son zuciya ta sanya ra’ayin “Makamashin nukiliya” ya zama daidai da samar da makaman nukiliya. Ya ce, “Samar da bama-bamai na nukiliya ƙaramin ɓangare ne kawai na sakamakon da ba su dace ba da rashin tausayi na wannan fanni. Sauran wannan masana’antar tana da nufin biyan buƙatun ɗan adam na asali. Manufar Iran da nufin kasar na faɗaɗa wannan masana’antar ita ce biyan buƙatun mutane da inganta rayuwar ƙasar ne, ba don samar da makamai ba.”

Shugaban ya kuma jaddada cewa: “Suna ɗaukar amfani da bama-bamai na nukiliya haramun ne, bisa ga fatawar da Babban Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya bayar.” Ya ƙara da cewa: “Ilimin yana cikin tunanin masana kimiyyar Iran, kuma rushe gine-gine da masana’antu ba zai hana kasar ci gaba ba. Za ta  sake gina cibiyoyin makamashin nukiliyarta da ƙarfi sosai.”

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Araqchi: Da Hadin Bakin Amurka, Gwamnatin Isra’ila ta kaddamar Da Hari Kan Kasar Iran November 2, 2025 Larijani: Iran Ba Ta Tsoron Gudanar Da Tattaunawa, Amma Ta Zama Mai Amfani November 2, 2025 Gwamnatin Isra’ila Tana Ci Gaba Da Hana Masu Jinya Zuwa Kasashen Waje Neman Magani Daga Gaza November 2, 2025 Kasar Qatar Ta Ba Da Tallafin Gaggawa Ga Al’ummar Sudan Bayan Gumurzun El-Fasher November 2, 2025 IAEA : Babu wata shaida da ke nuna cewa Iran na kera makaman nukiliya November 2, 2025 Amurka : zamu dauki matakin soja idan Najeriya ta gaza kawo karshen kashe Kiristoci November 2, 2025 Hamas ta musanta zargin Amurka na cewa tana sace kayan agaji a Gaza November 2, 2025 Wasu Yan Ta’adda Sun Kashe Dakarun Sa Kai 2 A Kudu Maso Gabashin Iran November 2, 2025 Sojojin Amurka Na Kara Fuskantar Venezuwela Adaidai Lokacin da Trump Ke Musanta Batun Kai Hari November 2, 2025 Isra’ila Ta Kashe Mutane 4 Tare Da Jikkata Wasu Guda 3 A Kudancin Labanon November 2, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Pezeshkian: Bunkasa Masana’antar Makamashin Nukiliyar Iran Don Inganta Rayuwar Al’ummar Iran Ne
  • Muna shirin kai farmaki a Nijeriya — Ma’aikatar Yaƙin Amurka
  • Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya
  • Sharrin son auren Mai Wushirya aka yi min — Mansura Isa
  • Gwamnatin Jihar Kwara Ta Kafa Kwamitoci 2 Don Tantance Wadanda Suka Yi Ritaya
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
  • Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai
  • Sudan Ta Yi Kira Ga Kwamitin Tsaro Da Ya Ayyana RSF A Matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda
  • Allah Ya Kai Manzon Allah (SAW) Muƙami Na Babban Yabo A Cikin Komai
  • An sake kama shi a cikin ’yan fashi kwana 5 da fitowa daga kurkuku