Kasar Sin Ta Yi Kiran Samar Da Ci Gaba Da Tsaro Bai-daya A Fannin Fasahar AI.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

An ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su a Kebbi

Rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi ta ce ta ceto wasu mutane uku da aka yi garkuwa da su, bayan sun yi artabu da wasu da ake zargin sun yi garkuwa da su a wani mummunan musayar wuta da aka yi a tsaunin Shanga.

Waɗanda aka yi garkuwan da su sun haɗa da: Muhammad Nasamu Namata mai shekara 25, da Gide Namata mai shekara 20 da Hamidu Alhaji Namani mai shekara 35.

INEC za ta fara rajistar ƙuri’a a ranar 18 ga Agusta Rundunar sojin ruwa za ta kafa sansaninta a Kebbi

An  yin garkuwa da su ne a safiyar ranar 27 ga watan Yuli, 2025, lokacin da masu garkuwa da mutane ɗauke da makamai suka mamaye ƙauyen Sangara da ke Ƙaramar hukumar Shanga.

A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, CSP Nafiu Abubakar ya fitar a ranar Juma’a, ya bayyana cewa wannan ceton ya biyo bayan ɗaukar matakin gaggawa da jami’an ’yan sanda na yankin Shanga suka ɗauka, wanda ya haɗa tawagar jami’an tsaro da suka haɗa da jami’an sojojin Najeriya, jami’an tsaro na Civil Defence da ’yan banga na yankin da mafarauta.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Rundunar ta bi sahun masu garkuwa da mutanen ne zuwa tsaunin Shanga, inda aka yi musayar wuta a tsakaninsu, musayar wutar ta sa jami’an tsaro suka yi nasara kan masu garkuwar.

Daga nan masu garkuwan suka tsere zuwa cikin daji da raunukan harbin bindiga.

“An kuɓutar da waɗanda aka yi garkuwa da su ne ba tare da wani rauni ba, a ranar Alhamis, 31 ga Yuli, 2025 da misalin ƙarfe 3:30 na rana kuma a halin yanzu suna samun kulawar likita kafin su sake haɗuwa da iyalansu.”

Ya ce, Kwamishinan ’yan sanda, CP Bello M. Sani ya yaba wa jarumtaka da ƙwarewa na rundunar, inda ya buƙaci dukkan hukumomin tsaro su ci gaba da haɗa kai. Ya nanata ƙudirin rundunar na kare rayuka da dukiyoyi a Jihar Kebbi.

Kwamishinan ya kuma yi kira ga al’ummar yankin da su sanya ido tare da kai rahoto ga jami’an tsaro mafi kusa domin ɗaukar matakin gaggawa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su a Kebbi
  • GORON JUMA’A 01-07-2025
  • An Zaɓi Saidu Yahya A Matsayin Shugaban Hukumar Yaƙi Da Cin Hanci Ta Kano
  • Habasha Ta Kaddamar Da Shirin Shuka Bishiyoyi Miliyan 700 A Rana Daya
  • Matsayar Bai Daya Da Sin Da Amurka Suka Cimma Ta Fuskar Haraji Na Da Babbar Ma’ana
  • Gwamna Zulum Ya Sauke Kwamishinoni Biyu Tare Da Maye Gurbinsu Da Wasu
  • Gwamnatin Jigawa ta horas da malamai 20,000 fasahar sadarwar zamani
  • Samar da makamashi mai tsafta na zamani shi ne fatanmu — Guterres
  • ZAMFARA: APC Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Kawo Dauki Don Matsalar Tsaro Na Kara Tsananta
  • An Yaba Da Kwazon Shugaba Bola Ahmad Tinubu