Masar Za Ta Karbi Bakuncin Taron Gaggawa Na Larabawa Kan Batun Falasdinu
Published: 10th, February 2025 GMT
Ma’aikatar harkokin wajen Masar ta sanar cewa, kasar za ta karbi bakuncin taron gaggawa na kasashen Larabawa a ranar 27 ga watan Fabrairun nan, domin tunkarar al’amura na baya-bayan nan da suka shafi batun Falasdinu da zirin Gaza.
Sanarwar ta ce, an yanke shawarar gudanar da taron ne bayan muhimman shawarwarin da Masar ta yi da kasashen Larabawa, ciki har da Falasdinu da ta bukaci gudanar da taron, tare da hadin gwiwar Bahrain.
A wani labarin kuma, kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ta yi kakkausar suka kan munanan kalamai da kuma rashin da’a da firaministan Isra’ila ya yi na yin kira da a kafa kasar Falasdinu a kasar Saudiyya.
A ranar Alhamis, ne Netanyahu ya ba da shawara yayin wata hira da tashar 14 ta Isra’ila cewa “Saudiyya za ta iya kafa kasar Falasdinu a Saudiyya, suna da kasa mai girma.”
Kungiyar ta OIC ta dauki wannan a matsayin tsokana ga Saudiyya, kuma cin zarafi ne ga ’yancin kai, tsaron kasa da kuma yankinta, da kuma keta dokokin kasa da kasa da kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya.
A yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa a birnin Washington da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ne a ranar Talata, shugaban Amurka Donald Trump ya ce Amurka na shirin “karbe ikon zirin Gaza,” da tura Falasdinawa zuwa kasashe makwabta, da kuma sake raya yankunan gabar tekun, kalaman na Trump da Netanyahu sun haifar da cece-kuce a yankin da ma duniya baki daya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST November 6, 2025
Daga Birnin Sin Baje Kolin CIIE Ya Bayar Da Tabbaci Ga Duniya November 6, 2025
Daga Birnin Sin Manufofin Sin Na Yaki Da Sauyin Yanayi: Gani Ya Kori Ji November 6, 2025