Kwamnadan Rundunar Sojin Ruwan IRGC Ya Ce: Suna Iya Rufe Mashigar Hormuz Amma Ba Za Yi Hakan Ba Yanzu
Published: 10th, February 2025 GMT
Kwamandan rundunar sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa: Za su iya rufe mashigar Hormuz, amma ba za yi hakan a yanzu ba
Kwamandan rundunar sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Ali Reza Tangsiri ya yi bayani kan irin fitattun abubuwan da jirgin ruwan da Iran ta kera mai suna Shahid Bahman Baqiri, inda ya ce; Wannan jirgi shi ne nau’i daya tilo saboda babu wata kasa a yankin yammacin Asiya da ke da makamancinsa.
Birgediya Janar Tangsiri ya bayyana a cikin shirin ”Labarin juyin juya hali” a tashar Al-Alam cewa: Bayan sanarwar da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya fitar dangane da alhakin da ya rataya a wuyan al’ummar Iran na gina rundunar sojojin ruwa ta tafi-da-gidanka a matakin juyin juya halin Musulunci. Domin samun damar tabbatar da tsaro ga magudanan ruwa na kasa da kasa da magudanar jiragen ruwa na Jamhuriyar Musulunci da kuma samun damar yin musanyar kayayyaki da na duniya, haka nan ma jiragen ruwa na duniya ma suna iya amfani da wannan hanya, to lallai ne dakarun kare juyin juya halin Musulunci su kasance a cikin teku. Domin kasancewa a cikin teku suna buƙatar manyan jiragen ruwa waɗanda za su iya kasancewa a can har abada kuma suna da wuraren da suka dace don gudanar da wannan aikin.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: juyin juya halin Musulunci
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Sanda A Kano Sun Kama Kasurgumin Dan Fashin Nan Barga Da Wasu Mutum 14
Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Kano ta samu nasarar kama mutane 15 da ake zargi da laifuka daban-daban, ciki har da wani kasurgumin dan fashi da makami mai suna Mu’azu Barga, a wani samame da aka lakaba wa suna “Operation Kukan Kura”.
Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano.
Ya ce samamen, wanda dakaru na musamman suka gudanar a unguwannin Sheka, Ja’oji, da Kurna a ranar 26 ga Yulin 2025, na da nufin gano da kuma hana aikata laifuka, bisa umarnin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, IGP Kayode Adeolu Egbetokun.
Kiyawa ya bayyana cewa, wadanda aka kama ‘yan tsakanin shekaru 14 ne zuwa 28, kuma an same su da wayoyin salula guda hudu da suka sace daga hannun mutane daban-daban.
“Wadanda ake zargin sun amsa laifin aikata sata da fashi, musamman satar wayoyin salula,” In ji shi.
“Mu’azu Barga, wanda ake zargi da kasancewa barawo a lokuta da dama, yana daga cikin wadanda aka kama. Ana danganta shi da laifukan fashi da makami, da kuma. jagorantar hare-hare masu tayar da hankali da fada tsakanin kungiyoyin daba a cikin birnin Kano.”
Kiyawa ya kara da cewa, Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ayyana yaki da duk wani nau’in laifi na daba, tare da jaddada kudurin rundunar na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.
Ya bayyana godiyar rundunar bisa goyon bayan jama’a, tare da yin kira da su ci gaba da bayar da rahoton duk wani motsi ko mutum da suke zargi da aikata laifi, a ofishin ‘yan sanda mafi kusa.
Abdullahi Jalaluddeen