Jami’ar Ahmadu Bello Ta Yaye Dalibai Fiye Da Dubu 20 a Bana
Published: 27th, January 2025 GMT
Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Farfesa Kabiru Bala ya roki Majalisar Dokoki ta kasa da ta yi gyare-gyaren doka don ware cibiyoyin ilimi daga zama hukumomi masu samarda kudaden shiga.
Ya yi wannan roko ne a wajen bikin yaya=e dalibai karo na 44 da aka gudanar a dandalin Mamman Kontagora da ke Samaru a Zariya.
Shugaban jami’ar ya ce idan haka ta faru, jami’o’in za su mayar da hankali ne a matsayin manyan cibiyoyin kawo ci gaban kasa.
Ya yi nuni da cewa Jami’ar Ahmadu Bello kamar yadda jami’o’in Najeriya da dama ke fuskantar kalubalen kudi don tallafa wa manufofinta na ci gaba da zamanantar da ayyukanta.
Farfesa Bala ya yi magana ne game da umarnin kotun masana’antu ta kasa na a rufe asusun ajiyar jami’ar dake a babban bankin Najeriya ajiya wanda ke cike da kudi naira miliyan dubu biyu da miliyan dari biyar da tamanin da biyar.
Ya yi nuni rashin jin dadin ganin c ewa wannan asusun jami’ar da abin ya shafa ya kunshi wasu kudade na sassan daban daban kamar tallafin bincike na gida da na waje, kudade na sassan jami’ar da ke da alaka da bincike bincike.
Ya bayyana cewa, a sakamakon wannan odar, dukkan ayyukan da suka shafi kashe kudi kamar su tsaftar muhalli, wutar lantarki da sauran kayayyakin masarufi na fuskantar cikas.
Tun da farko a nasa jawabin, shugaban jami’ar kuma shugaban majalisar gudanarwar jami’ar, Alhaji Mahmood Yayale Ahmed ya ce tsarin jami’o’in Najeriya na fuskantar kalubale da suka hada da kudade, mulki da gudanarwa.
Don haka ya ba da shawarar samun ‘yancin kai na kuɗi don tabbatar da cewa jami’o’i sun kasance matattarar masana da kwararri da tunani da sabbin abubuwa.
Shima a nasa jawabin, Uban jami’ar, Obi na Onitsha, Nnaemeka Alfred Achebe, ya dorawa daliban da suka yaye aikin yin amfani da wannan karni na 21 a matsayin shekarun juyin zamani.
Bikin karo na 44, an yaye dalibai 21,952 da suka kammala karatun digiri na 2023/2024, daga cikinsu 5,756 sun sami digiri na biyu yayin da 16,196 suka sami digiri na farko.
COV/HALIRU HAMZA/Wababe
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Ta’addanci: Ana Fuskantar Ƙarancin Man Fetur A Mali Sakamakon Datse Hanyoyin Shiga Bamako
Gidajen mai da dam aka rufe, yayin da wadanda suka kasance da dan sauran mai kuma, layuka ne marasa iyaka suka makare su, lamarin da ta kai har kwana mutane ke yi a gidajen man.
A kan titunan babban birnin kasar, bayanai sun ce ba kasafai ake ganin motoci suna kai komo ba, ko kuma mutane na tura babura, bisa alama dai mutane sun ajiye ababen hawansu a gida.
Sai dai duk da wannan karancin man da ake fama da shi, farashinsa ya ci gaba da kasancewa a yanda yake, domin kuwa farashin lita na mai CFA 775 yayin da dizal yake akan CFA 725.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA