2025-06-21@02:42:07 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2417
«tsiraici»:
A cikin takardar, ƙungiyar ta bayyana cewa ta yanke shawarar kafa sabuwar jam’iyya maimakon haɗaka da wasu. Sun bayyana cewa sun zaɓi suna All Democratic Alliance (ADA) kuma taken jam’iyyar shi ne “Justice for All” wato “Adalci ga Kowa.” Sun kuma haɗa da adireshin babban ofishin jam’iyyar a cikin takardar. Sun gabatar da wasu muhimman...
Jagororin jam’iyyun adawa na Najeriya a ƙarƙashin ƙungiyar hadaƙa ta Nigeria National Coalition Group (NNCG) na neman yin rajistar All Democratic Alliance (ADA) domin ta zama sabuwar jam’iyyar da za su yi amfani da ita don tunkarar Jam’iyyar APC a zaɓen 2027. NNCG ta riga ta miƙa takardar neman rajistar jam’iyya ga Hukumar Zaɓe mai...

Jakadan Sin Dake Amurka Ya Yi Jawabi A Gun Liyafar Da Kwamitin Kasa Mai Lura Da Kasuwancin Amurka Da Sin Ya Shirya
Kwamitin kasa mai lura da kasuwancin Amurka da Sin ko USCBC, ya gudanar da liyafar murna ta shekarar 2025, a ranar Laraba 18 ga wata a birnin Washington na Amurka, liyafar da jakadan kasar Sin a Amurka Xie Feng ya halarta tare da gabatar da jawabi. Cikin jawabin nasa jakada Xie ya ce cimma moriya...
Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta yanke wa wani mai suna Olukoye Olalekan hukuncin daurin shekaru 76 a kukuku saboda yada hotunan tsiraicin yara kanana da kuma aikata damfara. Alkalin kotun, Mai Shari’a Alexander Owoeye, ne ya yanke hukuncin ranar Alhamis, bayan ya samu mutumin da aikata laifukan da aka zarge shi da su....
Barcelona ta amince da yarjejeniyar ɗaukar ɗan wasan gaba na ƙungiyar Athletic Bilbao Nico Williams, amma kuma har yanzu akwai ƙalubalen da zasu fuskanta kafin ɗan wasan ya samu damar rattaba hannu a ƙungiyar ta Catalonia, ɗan wasan na ƙasar Sifaniya Williams, wanda ya zura ƙwallaye 31 a wasanni 167 da ya buga wa Bilbao,...
Sanarwar ta ce: “Ma’aikatar Harkokin Waje na sanar da jama’a cewa, sakamakon rikicin da ke kara kamari tsakanin Isra’ila da Iran, Gwamnatin Tarayya tana shirin karshe na kwaso ‘yan Nijeriya da suka maƙale a wadannan kasashe. “Saboda haka, ana shawartar dukkanin ‘yan Nijeriya da abin ya shafa da su kiyaye matakan tsaro da kuma tuntubar...
Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ce ta bayyana hakan a rahoton ayyukan ta’addanci na watanni 12. Rahoton ya bayyana ayyukan ta’addanci miliyan 51.89 da suka shafi iyalai, satar waya ce mafi yawa a ciki da kaso 13.8 da rahoton satar waya miliyan 25. Rahoton ya nuna akwai layukan waya da ke aiki a wayoyin hannu...
Shugaban Isra’ila, Isaac Herzog, ya bayyana cewa ƙasarsa za ta iya samun nasara a yaƙin da take yi da Iran ko da kuwa Amurka ba ta shigar mata ba. Sai dai Herzog ya shaida wa ABC News cewa kawar da barazanar nukiliyar Iran yana da muhimmanci ga “duniya mai ’yanci”, ciki har da Amurka. Nan...
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce sai nan da mako biyu zai yanke shawara kan ko zai shigar wa Isra’ila yaƙin da take yi da Iran ko kuma akasin haka. A wata sanarwa da sakatariyar yaɗa labaran fadar gwamnatin Amurka, Karoline Leavitt ta karanto, Trump ya ce akwai yiwuwar a zauna a teburin sulhu. Waadin...
A ranar 27 ga Mayu, 2025, Indomie Arewa ta ƙara ɗanɗano da armashi a cikin tasowar yara. Babban kamfanin abincin tana alfaharin ƙaddamar da Indomie AI Career Generator, wata dandalin zamani irinsa na farkon da aka ƙirƙira don nuna irin baiwar da yara ke da ita ta hanyar ba su damar ganin makomarsu ta wata sabuwar...
Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya buƙaci Donald Trump kada ya ɗauki matakin soji kan Iran, yana mai kiran da a biyo wa lamarin ta hanyar lalama. Mista Starmer ya ce akwai “mummunan hatsarin bazuwar” yaƙin, inda ya yi kira ga duka ɓangarorin sun rungumi sulhu. Ba zai yiwu mu bar Khamenei a raye ba —...
Ministan Tsaron Isra’ila, Israel Katz ya ce ba zai yiwu su bar jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei a raye ba. Israel Katz ya yi barazana ga Ayatollah yana mai cewa ya zama tilas ya ɗauki alhakin hare-hare da makamai masu linzami da Iran ta yi a kan wata cibiyar lafiya da ke kusa da...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta tabbatar da aniyarta na dawo da dukkan Alhazan Najeriya da ke Saudiyya zuwa ranar 28 ga watan Yunin, 2025. Rahotanni daga Hukumar NAHCON da ke birnin Makkah na cewa, alhazan Najeriya 6,528 ne suka dawo Najeriya, yayin da Kamfanin Max Air ya kammala jigilar Alhazai jirgi na 16 a...
Wata kotun shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu a Jihar Kano, ta yanke wa wasu mutum bakwai hukuncin ɗauri, bayan da suka ji wa wani ɗan sanda rauni yayin da ake ƙoƙarin cafke su. Al’ummar unguwannin Tudun Maliki da Sheka ne suka kai rahoton mutanen, inda suka zarge su da sayar da miyagun ƙwayoyi. ’Yan...
Ayatollah ya yi gargaɗi cewa, idan Amurka ta shiga cikin rikicin kai-tsaye don taimaka wa Isra’ila, wannan zai jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin matsala babba. Rikicin da ke tsakanin Iran da Isra’ila ya shafe kwanaki shida yanzu, inda mutane da dama suka mutu a ɓangarori biyun, baya ga asarar dukiyoyi da gine-gine. Daga...
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan kada a kuskura a shiga tsakanin yaƙin da Iran da Isra’ila ke fafatawa ta hanyar amfani da ƙarfin soji. Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya yi gargadi kan duk wani “shiga tsakani na soji”, a yankin Gabas ta Tsakiya, inda manyan abokan gaba Isra’ila da Iran ke musayar...
An cimma jerin yarjejeniyoyin hadin gwiwa a taron koli na biyu na kasar Sin da tsakiyar Asiya da aka gudanar a birnin Astana na kasar Kazakhstan a ranar 17 ga watan nan agogon kasar. Shugabannin kasashen biyar na tsakiyar Asiya sun yaba wa kasar Sin a matsayin babbar abokiyar hadin gwiwa kuma kawa ta gaskiya...
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya kai ziyara Jihar Benuwe domin jajanta wa mutanen jihar bisa hare-haren da suka faru a wasu ƙauyuka kwanan nan. Ya je ne domin nuna alhininsa ga waɗanda abin ya shafa da kuma tattaunawa da shugabanni don nemo mafita mai ɗorewa. Mun shirya yin sulhu da ’yan bindiga — Gwamnatin Sakkwato...
A ci gaba da yakin da suke yi da ’yan ta’adda, sojojin Najeriya sun samu nasarar jikkata jagoran kungiyar ISWAP, Abu Moussab Albarnawi a dajin Sambisa. Bayanai sun nuna sojoji sun sami nasarar ce bayan wani gagarumin harin da suka kai ta sama a wani sabon sansani na ’yan ta’addan da ke dajin Baikee a...
Masana sun yi gargadin cewa yakin da ake gwabzawa a tsakanin Isra’ila da Iran zai iya shafar farashin man fetur a duniya kuma hakan zai iya yin illa ga tattalin arzikin Najeriya. Masanan na cibiyar Commercio Partners da ke Legas sun bayyana fargabar ce a cikin wani rahoto da cibiyar ta fitar mai taken: “Farashin kayayyaki...
Sanarwar ta ƙara da cewa ana aiki tare da hukumomin cikin gida da na ƙasa da ƙasa domin ganin an gudanar da aikin kwasar cikin tsaro. Sanarwar ta ce: “Ma’aikatar Harkokin Waje na sanar da jama’a cewa, sakamakon rikicin da ke ƙara ƙamari tsakanin Isra’ila da Iran, Gwamnatin Tarayya tana shirin ƙarshe na kwaso ‘yan...
Majalisar Dokoki ta kasa ta ce ta aike wa Shugaban Kasa Bola Tinubu kudurorin dokar harajin da ta amince da su a hukumance domin ya rattaba musu hannu su zama doka. Shugaban Kwamitin Yada Labarai na Majalisar Dattawa, Sanata Yemi Adaramodu (APC, Ekiti) ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai ranar Talata a...

Majalisar Wakilai Ta Fara Binciken Yadda Aka Raba Naira Tiriliyan 1.12 Kan Shirin Lamuni Ga Manoma Da Masana’antu
Kwamitin Majalisar wakilai mai kula da samar da abinci mai gina jiki da tattalinsa ya fara bincike kan yadda aka kashe Naira Tiriliyan 1.12 na shirin Ba da Lamuni na Anchors. Har ila yau, binciken ya shafi yadda cibiyar NIRSAL’s ta raba Naira biliyan 215 na ayyukan noma da kuma yadda Bankin Masana’antu (BOI) shi...
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa ya san inda jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei yake “boye”, kuma ya yi gargadi cewa Washington na iya halaka shi, amma za su dakata a halin yanzu. Wannan na zuwa ne yayin da Trump din ya gargadi Iran kan da kada ta kai harin makamai masu...
Kafofin yaɗa labarai na cikin gida a Iran sun yi iƙirarin cewa ƙasar ta kai hari kan hedikwatar hukumar leƙen asiri ta ƙasar Isra’ila (Mossad). Kamfanin dillancin labaran Iran (TASNIM) ya ruwaito cewa rundumar juyin juya hali na Iran (IRGC) ce ta kai harin a hedikwatar Mossad da ke Herzliya. Kamfanin ya wallafa wasu jerin...
Akalla mutane 20 sun mutu yayin da wasu 16 suka jikkata a wani rikicin ƙabilanci da ya auku a wani lardi na gabashin kasar Chadi. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar sadarwa ta ƙasar ta fitar, ta ce fadan ya barke ne daga ranar 10 zuwa 14 ga watan Yuni a yankin Molou na lardin...
Isra’ila ta tabbatar cewa an garzaya da ’yan ƙasarta aƙalla 154 asibiti bayan sabbin hare-haren ramuwar gayya da Iran ta kawo mata. Ma’aikatar lafiyar Isra’ila ta ce aƙalla mutum huɗu daga cikin waɗanda aka kai asibitin suna cikin halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai, wasu biyar kuma na samun kulawa ta musamman saboda tsananin tashin hankali. Alkaluman da ma’aikatar...
Tankokin yaƙin Isra’ila sun i kashe kimanin mutun 51 a yankin Khan Younis da ke Zirin Gaza, a yayin da mutanen suke tsaka da karbar abincin tallafi. Jami’ain lafiya sun sun ce mutum 51 sun mutu, wasu 200 sun samu raunuka — 20 daga cikinsu suna cikin halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai — bayan harin. Sun bayyana harin...
Hukumomin Isra’ila na ci gaba da bincike tare da ɗaukar matakan gaggawa domin daƙile tasirin harin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga...
Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump ya ce yana neman ganin an kawo karshen rikicin nukiliyar ƙasar Iran gaba ɗaya, a yayin da aka shiga kwana na biyar a yaƙin da ya ɓarke tsakanin Iran da Isra’ila. Trump ya bayyana shirinsa na tura manyan jami’an ƙasarsa zuwa birnin Tehran domin tattaunawa da hukumomin Iran a game...
Hukumar gudanarwar matatar man ƙasar Isra’ila da ke yankin Haifa ta sanar cewa matatar ta dakatar da ayyukanta ɗungurungum bayan harin da Iran ta kai mata. Kamfanin Bazan Group da ke kula da matatar ya ce harin na Iran ya tilasta musu tsayar da gaba ɗaya — a yayin da sabon rikicin na yankin Gabas...
Ƴansandan jihar Kogi sun tabbatar da sace wani basarake mai suna Samuel Ajayi Bello yayin da yake aikin gona a gidan gonarsa na Ponyan da ke kan titin Ponyan-Irele, a ƙaramar hukumar Yagba ta Gabas. Mai magana da yawun ‘yansandan jihar, SP William Aya, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da ƙarfe 10 na...
Wani yaro mai kimanin shekaru goma a duniya ya harbe mahaifinsa wanda jami’in ɗan sanda ne mai mukamin sufeto a Jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Nijeriya. Haka kuma, wakilinmu ya ruwaito cewa yaron ya harbi wani yayansa da bindigar mahaifin nasa ta aiki kirar AK-47. Kashe jagoran addini na Iran zai kawo ƙarshen...
Wani yaro mai kimanin shekaru goma a duniya ya harbe mahaifinsa wanda jami’in ɗan sanda ne mai mukamin sufeto a Jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Nijeriya. Haka kuma, wakilinmu ya ruwaito cewa yaron ya harbi wani yayansa da bindigar mahaifin nasa ta aiki kirar AK-47. Kashe jagoran addini na Iran zai kawo ƙarshen...
Ƴansandan jihar Kogi sun tabbatar da sace wani basarake mai suna Samuel Ajayi Bello yayin da yake aikin gona a gidan gonarsa na Ponyan da ke kan titin Ponyan-Irele, a ƙaramar hukumar Yagba ta Gabas. Mai magana da yawun ‘yansandan jihar, SP William Aya, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da ƙarfe 10 na...
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce duk wani shiri na kashe jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei ba zai rura wutar rikicin da ake yi yanzu ba, hasali zai ma kawo ƙarshen rikicin ne. A wata hira ta tsawon minti 20 da tashar talabijin ta ABC ta Amurka ta yi da shi, Netanyahu ya...
Za a gudanar da taron jin ra’ayin jama’a a lokacin ziyarar shugaban ƙasa. Tun da farko, Tinubu ya yi Allah-wadai da rikicin da ke faruwa a Benuwe, inda ya yi kira da a zauna lafiya. Haka kuma, ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu da dukiyoyinsu a sanadin rikicin. Tinubu ya shirya kai...
Yau Litinin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Guo Jiakun ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum. Game da halin da ake ciki yanzu a yankin Gabas ta Tsakiya, Guo Jiakun ya ce, ministan wajen Sin Wang Yi ya riga ya tattauna ta waya tare da takwarorinsa na Iran da Isra’ila, inda ya...
Iran ta ce ta aiwatar da hukuncin kisa ta hanyar rataya ga mutumin da aka kama yana yi wa Isra’ila leƙen asiri. Mahukunta a bangaren shari’ar sun ce an kama Esmail Fekri a shekarar 2023 yana ƙoƙarin miƙa wa Isra’ila bayanan sirri ne don samun kuɗi. KADSEMA da IOM sun fara tantance ɓarnar da ambaliya...
FCCPC ta lura cewa, waɗannan sassan dokar suna kare ‘yan Nijeriya daga “rashin adalci, rashin sanin ya kamata, daga kwastomominsu.” A wata wasika mai ɗauke da kwanan watan 13 ga watan Yuni 2025, FCCPC ta yi amfani da sashe na 32 da na 33 na FCCPA, inda ta bukaci kamfanin da ya gurfana a...

Shugabannin Duniya Za Su Gudanar Da Taron Sanya Hannun Jarin Bunƙasa Ƙudurorin Muradun Ƙarni A Sifaniya
Shirin dai zai kunshi abubuwa masu mahimmanci guda uku; Na farko, Taron Sevilla zai taimaka wajen zaburar da shigowar tallafi zuwa ga kasashen da suka fi bukatarsa. Na biyu, dole ne kasashe su kasance a kan kujerar tattara albarkatun cikin gida ta hanyar karfafa samar da kudaden shiga da magance rashin biyan haraji, hadin gwiwar...
Dan wasan mai shekaru 27 ya zura kwallaye 20 sannan ya taimaka wajen zura bakwai daga wasanni 40 da ya buga a duk wasannin da ya buga a kakar wasan data gabata, Lookman ya ci kwallaye 17 kuma ya taimaka wajen zura 10 a kakar wasanni ta shekarar 2023/24. Daga kanmu, magana ta...
Dakarun kare juyin juya halin Musulunci sun kai hare-hare har sau uku kan cibiyoyin leken asirin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Ma’aikatar hulda da jama’a ta dakarun kare juyin juya halin musulunci ta Iran ta fitar da sanarwa inda ta bayyana harin da aka kai kan cibiyoyin leken asirin haramtacciyar kasar Isra’ila a mataki na uku...

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Sojojin Isra’ila Sun Kashe Kananan Yara Masu Yawa A Iran
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Yahudawan sahayoniyya sun kashe adadi mai yawa na yaran Iran a cikin ta’addancin da suke yi Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya bayyana cewa: Gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta kashe kananan yara masu yawa na Iran a cikin wannan ta’asa da take gudanarwa kan Jamhuriyar...
Iran ta zartar da hukuncin kisa kan jami’an leken asirin Hukumar leken asirin yahudawan sahayoniyya “Mossad” a safiyar yau Litinin A wani gagarumin farmaki da aka kai kan cibiyar leken asirin yahudawan sahayoniyya a cikin kasar Iran, an kama wani mutum tare da yi masa shari’a bisa zargin hadin kai da hukumar leken asirin ‘yan...
Jami’an tsaron kan iyakokin Iran sun harbo jiragen saman yaki marasa matuki ciki guda 44 a cikin sa’o’i 48 da suka gabata Kwamandan rundunar tsaron kan iyakokin kasar Iran Birgediya Janar Ahmad Ali Goudarzi ya bayyana cewa: An harbo jiragen sama marasa matuka ciki guda 44 da kananan jiragen saman yakin gwamnatin ‘yan sahayoniyya tare...
Gwamnatin Amurka ta rufe Ofishin Jakadancinta da ke haramtacciyar kasar Isra’ila Jakadan Amurka a haramtacciyar kasar Isra’ila Mike Huckabee ya sanar a yau Litinin cewa: Wani makami mai linzami na Iran ya fado kusa da ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Tel Aviv, wanda ya yi barna kadan amma ba a samu rauni a tsakanin...
Matatar mai ta Dangote ta sanar da fara dakon man fetur da dizal a fadin kasar daga ranar 15 ga Agusta, 2025. A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, matatar ta bayyana cewa shirin zai hada da ‘yan kasuwa, masu gidajen mai, masana’antun, kamfanonin sadarwa, kamfanonin jiragen sama, da sauran manyan masu...
Isra’ila ta ce mutum takwas sun mutu a daren ranar Litinin sakamakon sabon harin da Iran ta kai a biranen Tel Aviv da Haifa da wasu sassa na ƙasar. Wannan na zuwa ne a matsayin ci gaba daga jerin hare-hare da Iran ke kai wa tun bayan da Isra’ila ta fara kai mata hari makonnin...