2025-11-25@22:21:32 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4770
«Yabi»:
Daga Bello Wakili Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bayyana farin cikinsa bisa dawowar ’yan mata 24 da ’yan ta’adda suka sace a Maga, Jihar Kebbi. ’Yan ta’addan sun kai hari makarantar ranar 17 ga wantan Nuwamban 2026, inda suka yi awon gaba da ’yan matan, jim kaɗan bayan wata rundunar soji ta bar harabar makarantar....
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya gabatar da kasafin kuɗi na shekarar 2026 na sama da naira biliyan 900 ga Majalisar Dokokin jihar. Yayin gabatar da kasafin da aka lakaba wa suna “Kasafin Kirkire-kirkire da Sauyi Don Cigaban Jigawa II,” Gwamna Namadi ya ce za a ware sama da naira...
’Yan Majalisar Tarayya daga yankin Kudu sun yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi wa jagoran ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, afuwa bayan da kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai. Kungiyar ’Yan Majalisar Wakilai daga yankin Kudu maso Gabas ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya yi amfani...
Rahotanni na cewa ’yan bindiga sun sace wasu mutum takwas a garin Biresawa da ke Karamar Hukumar Tsanyawa ta Jihar Kano a daren jiya na Litinin. Wata majiyar da ta tabbatar da lamarin ta shaida wa Aminiya cewa maharan sun shiga garin tsakanin 11 na dare zuwa 12 na tsakar dare, inda suka yi awon...
’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 11, ciki har da wat mai juna biyu da ƙananan yara Jihar Kwara. Maharan sun kai farmaki tare da sace mutanen ne a yankin Eruku da ke Ƙaramar Hukumar Ekiti da ke jihar. Ƙarin bayani na tafe…
Gwamnatin kasar ta Gambia ta sanar da bai wa jagoran ‘yan hamayyar kasar ta Kamaru Isa Chiroma mafaka bisa dalilai na “‘yan adamtaka”. A wani bayani da ma’aikatar harkokin waje ta kasar Gambia ta fitar, ta bayyana cewa; Chiroma dan shekaru 76 ya isa babban birnin kasar Panjul a ranar 27 ga watan Febrairu a...
A jiya Litinin ne dai mahukuntan kasar ta China su ka yi Allawadai da yadda kasar Japan din ta girke makamai masu linzami a wani tsibirinta da yake kusa da yankin Taiwan, tare da bayyana hakan a matsayin kokarin tayar da hargitsi a cikin yankin. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar China Máo...
Abbas Arakci Ya Yi Gargadi Akan Abin Zai Biyo Bayan Keta Dokokin Duniya Da “Isra’ila” Take Yi A Cikin Wannan Yankin
Ministan harkokin wajen na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci wanda yake ziyarar aiki a kasar Oman ya gana da manzon musamman na MDD a kasar Yemen Hans Grundberg a jiya Litinin ya yi tir da yadda Haramtacciyar Kasar Isra’ila take keta dokoki tana kai wa kasashen wannan yankin hare-hare. Haka nan kuma ministan harkokin...
’Yan Majalisar Wakilai daga yankin Kudu sun yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi wa jagoran ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, afuwa bayan da kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai. Kungiyar ’Yan Majalisar Wakilai daga yankin Kudu maso Gabas ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya yi amfani...
Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Gombe ta ƙaddamar da sabbin matakan ƙarfafa tsaro a makarantu bayan wani taron tattaunawa da aka gudanar tsakanin Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, Bello Yahaya, da shugabannin Ƙungiyar Malaman Sakandare reshen jihar. An gudanar da taron ne a Hedikwatar Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Gombe, bisa umarnin Sufeton ’Yan Sanda...
Shugaban kasar Sudan kuma babban kwamandan sojojin kasar Janar Abdulfattah Alburhan, ya yi watsi da shawarar Amurka ta kawo karshen yaki a kasarsa wanda ya lakume rayukan mutane da dama, ya kuma raba kasar gida biyu a cikin watanni kimani 30 da suka gabata. Shafin yanar gizo na labarai ‘AfricaNews’ ya nakalto Burhan yana fadar...
Shugaban kasar Sudan kuma babban kwamandan sojojin kasar Janar Abdulfattah Alburhan, ya yi watsi da shawarar Amurka ta kawo karshen yaki a kasarsa wanda ya lakume rayukan mutane da dama, ya kuma raba kasar gida biyu a cikin watanni kimani 30 da suka gabata. Shafin yanar gizo na labarai ‘AfricaNews’ ya nakalto Burhan yana fadar...
Gwamnonin jihohin kudu maso yammacin Najeriya sun bada sanarwan cewa lokacin kafa yansandan jihohi ya yi, har’ila yau dakuma karfafa kula da dazuzzukan kasar saboda magance matsalolin tsaro da suka addabi kasar. Jaridar Daily Trust ta nakalto gwamnonin na fadar haka a jiya Litinin bayan taron gwamnonin shiyar kudu maso yammacin kasar da suka gudanar...
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya kaddamar da titi mai tsawon kilomita 13 da rabi, da ya tashi daga Sada zuwa Danakari zuwa Unguwar Malam Kuda, zuwa Magina, a Karamar Hukumar Yankwashi ta jihar. A jawabinsa wajen bikin kaddamarwar, Namadi ya bayyana kudirin gwamnatinsa na ci gaba da samar da muhimman...
Manzon musamman na majalisar dinkin duniya kan kasar Yamen yayi kira ga kasar iran ta ci gaba da nuna goyon bayan kokarin da duniya ke yi wajen ganin zaman lafiya ya ci gaba da wanzuwa a kasar Yamen Han Grungdbag wakilin majalisar dinkin duniya yayi wannan kira ne a lokacin ganawarsa da ministan harkokin wajen...
Rahotanni daga kasar Habasha sun ce dutsen na Hayli Gubbi ya fitar da kura da toka mai yawa da ta shiga kasashen Oman da Yemen. Masana ilimin kasa sun ce lokaci na karshe da dutsen ya yi aman wuta shi ne shekaru 10,000 da su ka gabata. Bugu da kari, masana ilimin kimiyya sun ce...
A yau Litinin tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, zai yankin kati domin shiga Jam’iyyar ADC a hukumance. Manyan hidiman Atiku sun shaida wa Aminiya cewa an kammala dukkan shirye-shirye domin yin rajistar Atiku a mazaɓarsa ta Jada 1 da ke Ƙaramar Hukumar Hada ta Jihar Adamawa. Atiku ya yi nuni da wannan mataki ne...
A dare na uku na makokin shahadar Fatiman Azzahra (s) diyar manzon All.. (s) shuwagabannin bangarorin gwamnati 3 a nan Iran sun sami halattan makakinta (s) a Husainiyyar Imam Khomanin(q) dake nan Tehran. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa, shugaban kasa Dr Masoud Pazeshkiya, Alkalin alkalai Hujjatul Islam Sheikh Ibrahim Ijeyi...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi da tokwaransa na kasar Omman Badr Al-Busaidi sun tattauna a birnin Muscat babban birnin kasar Omman a jiya Lahadi, inda bangarorin biyu suka tabo al-amura da suka shafi halin da ake ciki a yankin musamman HKI da kasashen yankin, da kuma dangane da kara dankon zumunci tsakanin kasashen...
Yayan kungiyar yan ta’adda ta ‘the Islamic State West African Province (ISWAP) ta bada sanarwan kamawa da tsare yan mata 13 a karamar hukumar Askira-Uba na jihar Borno a jiya Lahadi. Jaridar Daily Trust ta Nageriya ta nakalto Abdullahi Askira dan majalisar dokokin jihar Borno mai wakiltan Askira yana tabbatar da labarin ya kuma kara...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A shekarar 2014, bayan tashin hankalin da ya biyo bayan sace ɗaliban Chibok da kuma yawaitar hare-hare kan makarantun yankin Arewa maso Gabas, gwamnatin tarayya tare da haɗin gwiwar ƙasashen duniya ta ƙaddamar da wani muhimmin shiri mai suna Safe School Initiative. Manufar wannan shiri ita ce...
Shugaban kasan Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin janye jami’an ƴansanda dake gadi ko rakiyar manyan mutane domin mayar da su aikin tsaro. Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar ya fitar Mr Bayo Onanuga, da yammacin wannan Lahadi, ya ce daga yanzu za’a rika tura jami’an ƴansanda ne gudanar...
Ana zargin wasu ’yan bindiga da kashe wani fitaccen ɗan kasuwa, Alhaji Muhammad Bakoshi, lokacin da suka kai hari garin Zalau da ke Ƙaramar Hukumar Toro a Jihar Bauchi. Bayan kai hari, sun sace ɗaya daga cikin matansa, Hannatu Muhammad. Tinubu ya dakatar da ’yan sanda daga tsaron manyan mutane a Najeriya An ceto mutum...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bai wa ’yan sanda umarnin daina tsaron manyan mutane a faɗin Najeriya. Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ne, ya bayyana hakan a ranar Lahadi. ’Yan sanda sun ƙaryata jita-jitar kai wa coci hari a Gombe ’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda 5 a Bauchi Onanuga, ya ce...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta ce labarin da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta na kai wa cocin ECWA da ke Kashere hari, ba gaskiya ba ne. Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi ne, ya bayyana haka, inda ya ce sun bincika tare da gano cewar jita-jita ce. Ya ce DPO na Pindiga da shugaban...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta tabbatar da mutuwar wasu jami’anta guda biyar a ƙauyen Sabon Sara da ke Ƙaramar Hukumar Darazo, sakamakon harin da wasu ’yan bindiga suka kai. Kakakin rundunar, CSP Ahmed Wakil ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranae Lahadi. An ceto mutum 38 da aka sace a cocin Kwara...
A Isra’ila Dubban masu zanga-zanga ne suka gudanar da wani babban gangami a Tel Aviv don neman a gudanar da bincike na gaskiya kan harin ba zata na ranar 7 ga Oktoba da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta kai. Masu zanga-zangar adawa da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu sun taru, a dandalin Habima da ke...
Babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya yi kira ga shugabannin kasashen duniya da suke taro a birnin Johannesburg na kasar Afirka Ta Kudu da su warware matsalar rashin daidaito a cikin harkokin kasuwanci a tsakanin kasashe. Babban magatakardar MDD wanda ya gabatar da jawabi a wurin taron na G 20 ya yi Ishara da gibin...
Zabebben magajin garin birnin NewYork na kasar Amurka Zohran Mamdani, a haduwarsa ta farko da shugaban kasar Amurka Donal Trump a birnin Washington ya bayyana cewa HKI tana aikata kissan kiyashi a gaza, sannan mutanen NewYork basa son ganin gwamnatin Amurka tana amfani da kudaden harajin da suke biyu wajen tallafawa gwamnati wacce take aikita...
Mai ba wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya gana da Sakataren Yakin Amurka, Pete Hegseth, a Washington, inda gwamnatin Trump ta nuna damuwarta kan karin hare-haren da ake kai wa mabiya addinin Kirista a Nijeriya. Hegseth ya tabbatar da ganawar a shafinsa na X, yana mai cewa bangarorin biyu sun tattauna...
Sojojin Isra’ila sun kashe wasu yara falasdinawa guda biyu a yankin gaza duk da yajejejeniyar dakatar da bude wuta da a sanya hannu akai, da ta fara aiki a farkon watan oktoba kamar yadda hukumar unicef tayi gargadi akai. Tun da aka rattaba hannun kan yarjejeniyar dakatar da bude wuta a ranar 11 ga watan...
Majalisar Dattijai ta nuna damuwa kan tabarbarewar yanayin tsaro a kasar sannan ta yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta amincewa da daukar akalla matasa 100,000 cikin rundunar sojoji domin karfafa tsarin tsaro na Nijeriya da yake fuskantar kalu bale. ‘Yan majalisar sun kuma yanke shawarar kafa kwamitin musamman domin bincikar yadda...
Daga Aminu Dalhatu Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Zamfara ta ce ta samu nasarar ceto mutune 25 da aka yi yunkurin sacewa, bayan wani hari da ’yan bindiga suka kai wa kauyen Kuraje da ke yankin Damba a Karamar Hukumar Gusau. Wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya fitar...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara, ta daƙile wani hari da ’yan bindiga suka kai wa al’ummar Kuraje da ke gefen birnin Gusau. Wasu gungun ’yan bindiga, ɗauke da makamai ne, suka kutsa cikin ƙauyen suna harbi, lamarin da ya jefa mazauna Kuraje da maƙotan ƙauyukan cikin tashin hankali. Gwamnatin Tarayya ta musanta jita-jitar rufe dukkanin...
A ranar Alhamis da dare ne janar Thiani wanda ya karare kasar ta Nijar a cikin motoci a wani ran gadi da shi ne irinsa na farko da wani shugaban kasar ya yi, ya sami kyakkyawar tarba a wurin mazauna babban birnin. Kafar wasta labaru ta “Afircanews” ta nakalto wani dan fafutuka mai suna Zakari...
Gwamnatin Tarayya ta bada umarnin rufe makarantu arba’in da daya saboda matsalolin tsaro. A wata takardar sanarwa da aka aikewa dukkan Shugabannin makarantu, wadda Daraktan Makarantu Manyan Sakandare na Ma’aikatar Ilimi ya sanya wa hannu, gwamnati ta bayyana cewa sakamakon ƙalubalen tsaro da ake fuskanta a wasu sassan ƙasar nan da kuma buƙatar kare duk...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyar mu a yau. Shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata wadanda suka shafi siyasa, tattalin, arziki, zamantakewa tsaro da sauransu, inda muke masu Karin bayani sannan daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane...
Kakakin majalisar dokokin kasar Iran mohammad Bhakir Qalibaf ya bayyana cewa makiya JMI sun sawya salon yakaar kasar kamar yadda suka saba, a halin yanzu sun fibada karfi kan takurawa tattalin arziki da rikita al-adu da kuma zamantakewa tsakaninmutanen kasar. Kamfanin dillancin labaran IP nakasar Iran ya nakalto Qalibaf yana fadar haka a jiya jumm’a...
Wani tsohon ma’aikacin hukumar leken asiri ta CIA ta kasar Amurka John Kiriakou ba ce a yakin kwanaki 12 tsakanin HKI da JMI, Isra’ila ta yi barazanar jefawa JMI makaman Nukliya idan har Amurka bata kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin Nukliya na kasar Iran ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran, ya nakalto Mr...
A ranar Alhamis da ta gabata ce karamin kwamiti mai kula da al-amuran nahiyar afirka a majalisar dokokin kasar Amurka ya bude tattaunawa dangane da zargin da shugaban kasar Donal Trump yake yin a cewa ana kashe kiristoci a tarayyar Najeriya fiye da duk wata kasa a duniya. Wanda hakan ya say a yi barazanar...
Shugaban kasar Ukrain Volodymyr Zelensky ya fito fili ya bayyana cewa bai amince da sabon shirin shugaban kasar Amurka Donal Trump na kawo karshen yaki a kasarsa. Ya kuma bayyana cewa kasar Ukraine tana cikin mafi munin hali a tarihin kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a...
Yan wasan kasar Iran sun kammala gasar wasannin sada zumunci na kasashen musulmi wanda aka kammala a birnin Riyad na kasar Saudiya tare da lambobin yabo har 81. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa wannan ya nuna cewa kasar Iran na daga cikin kasashen musulmi wadanda suke da kwarewa a wasannin...
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin Jihar Jigawa ta tabbatar da bada cikakken goyon bayanta ga Kwalejin Aikin Noma ta Gwamnatin Tarayya da ke Kirikasamma. Gwamna Umar Namadi ya bayar da wannan tabbaci ne lokacin da ya karɓi tawagar gudanarwar kwalejin ta farko, ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Dr. Muhammad Yusha’u Gwaram, yayin ziyarar girmamawa da suka kai...
Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) sun nuna damuwarsu kan sace malamai da ɗaliban makarantar St. Mary’s da ke Ƙaramar Hukumar Agwara, a Jihar Neja. Sun ce wannan lamari babban hatsari ne ga rayuwar yara da makomar ilimi a yankin Arewa baki ɗaya. DSS ta mayar da Nnamdi Kanu gidan yarin Sakkwato Sojoji sun bar makarantar Maga...
’Yan bindiga sun kai hari makarantar Katolika ta St. Mary da ke cikin yankin Papiri a ƙaramar hukumar Agwara ta Jihar Neja, sannan suka sace ɗalibai da malaman da ba a kai ga tabbatar da adadinsu ba. Har zuwa yanzu dai babu cikakkun bayanai a kan harin, amma majiyoyi sun shaida wa wakilinmu cewa an...
’Yan bindigar da suka yi garkuwa da masu ibada a cocin Christ Apostolic Church da ke Eruku, a jihar Kwara, sun nemi Naira miliyan 100 a matsayin kudin fansar kowanne mutum da suka kama. A cewar Faston cocin, Lawrence Bamidele, tsakanin mutane 30 zuwa 35 aka yi garkuwa da su a daren Talata lokacin da...
Daga Ali Muhammad Rabi’u ‘Yan bindigar da suka sace masu ibada 38 a Cocin Christ Apostolic Church (CAC), Eruku da ke ƙaramar hukumar Ekiti a Jihar Kwara sun nemi kudin fansa na Naira miliyan 100 kan kowane mutum daya da suka sace. Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa masu garkuwan sun fara kiran iyalan waɗanda aka...
Daga Bello Wakili Shugaba Bola Tinubu ya umurci Ministan Tsaro, Alhaji Bello Matawalle, da ya koma Jihar Kebbi biyo bayan sace dalibai ’yan mata 24 a jihar. An umurci Matawalle, wanda tsohon gwamnan Jihar Zamfara ne, da ya zauna a jihar domin sa ido kan ƙoƙarin da ake yi na kubutar da ɗaliban da aka...
Daga Usman Muhammad Zaria Daliban makarantu daga jihohin Arewa maso Yamma da suka hada da Kano, Jigawa da Katsina sun yi kira ga masu ruwa da tsaki da su samar musu da tsaro, ingantaccen kiwon lafiya, da taftataccen ruwan sha. Daliban sun yi wannan kiran ne yayin bikin Ranar Yara ta Duniya da aka gudanar...
Daga Abdullahi Shettima Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya karɓi Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda suka tattauna kan manyan muhimman abubuwan ci gaban jihar musamman a fannoni na noma, ababen more rayuwa da tsaro. A yayin ganawar, Gwamna Uba Sani ya bayyana godiyarsa ga Shugaban Ƙasa...