2025-11-20@07:56:10 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4093
«Sufeto Janar Na Yan Sanda»:
Wani magidanci tare da ɗaukacin iyalinsa huɗu sun rasu sakamakon wata gobara da ta tashi a sanadin kunna maganin sauro a layin Baba Impossible da ke Unguwar Kundila, da ke Ƙaramar Hukumar Tarauni a Jihar Kano. Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ta tabbatar da tashin wutar da misalin ƙarfe 4:13 na Asubar ranar Laraba....
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Mata da dama da aka yi garkuwa da su na shiga wani irin mawuyacin hali yayin da suke hannun wadanda suka sace su, suna fuskantar rayuwar kaskanci, da cin zarafi, da muzgunawa da wasu irin yanayi wanda sai ka tausaya musu. Irin wadannan mata a wasu lokutan basa...
Tauraron ɗan wasan Barcelona, Lamine Yamal, ya bayyana cewa ya shirya jagorantar ƙungiyar wajen kafa sabon tarihi a filin wasa na Camp Nou, wanda za su koma buga wasa a ƙarshen makon nan yayin karɓar baƙuncin Atletico Bilbao. Tun kusan kwanaki 900 da suka gabata ne aka rufe filin wasa na Camp Nou sakamakon wasu...
Matsayar da Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta dauka kan tattaunawa da Amurka Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ismail Baqa’i ya bayyana cewa: A halin yanzu babu wata tattaunawa da ake yi tsakanin Iran da Amurka. Ya yi nuni da cewa: Babu wata hujja mai ma’ana ta tattaunawa da wani bangare da ke neman ta tsara...
Darakta Janar na Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya {IAEA} ya bayyana cewa: Suna tuntubar Tehran kuma masu binciken hukumar sun koma kasar ta Iran Darakta Janar na Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA), Rafael Grossi, ya tabbatar da komawar masu binciken Hukumarsa ta IAEA zuwa Iran da kuma ci gaba da duba wasu wurare da...
An yanke wa abokan aikin ɗan tsohon shugaban kasar Gabon hukuncin ɗauri a gidan kurkuku Kotun Hukunta Laifuka ta Musamman da ke Gabon ta yanke hukuncin ɗauri a gidan kurkuku daga watanni 26 zuwa shekaru 15 ga tawagar abokan Nouruddine Bongo, ɗan tsohon shugaban ƙasa Ali Bongo, a shari’ar da aka fi sani da “Tawagar...
Rahotanni sun bayyana cewa Iran ta yi suke kudurin Amurka da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya amince da shi na tilasta aikewa da dakarun kasa da kasa zuwa yankin gaza domin tabbatar da zaman lafiya, ta yi gargadin kada ayi amfani da shi wajen take hakkokin alummar falasdinu na kafa kasarsu mai cin...
Amina Hassan, matar Yakubu Makuku, mai gadin makarantar ’yan mata ta GCGSS Maga da ke Ƙaramar Hukumar Danko Wasagu a Jihar Kebbi, wadda aka kai wa hari da safiyar Litinin, ta bayyana yadda aka kashe mijinta. Da take magana da ’yan jarida a wurin da lamarin ya faru, ta ce bayan da maharan suka kutsa...
Majalisar Wakilai ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya sake kawo sabuwar dabarar da za ta kawo karshen kashe-kashe, da sace-sace da sauran ayyukan ‘yan bindiga a Jihar Zamfara da ma kasa baki daya. Wannan ya biyo bayan amincewa da kudirin gaggawa na kula da muradun jama’a da dan majalisa mai wakiltar mazabar...
Iran: An Bayyana Taron Gundumomin Dake Gabar Ruwan ” Caspian” Da Cewa Yana Bunaksa Alakar Kasashen Yankin
Fira ministan jamhuriyar Kalmykia mai kwarya-kwaryar cin gashin kai a tarayyar Rasha, Utshir Janibinov ya fada wa manema labaru a wurin taron gwamnonin gundumomin dake gabar ruwan “Caspian” cewa; Taron da aka yi wanda shi ne irinsa na farko yana da tasiri mai kyau wajen bunkasa alaka a tsakanin gundumomin gabar ruwan “Caspian”. Taron na...
Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila suna ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta a Lebanon, da a yau Talata su ka kai wani hari a garin Bint-Jubail da ya yi sanadiyyar shahadar mutum daya da kuma jikkatar wani. Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya ambato ma’aikatar kiwon lafiya ta Lebanon tana cewa; Birnin na Bint...
Masu gangamin da adadinsu ya kai 100 sun tsaya a gaban babbar kofar shiga wurin taron kare muhalli na MDD da aka bude a garin Belem dake yankin Amazon na Brazil. Sojojin kasar Brazil sun bai wa masu gangamin kariya, tare da kaucewa yin taho mu gama saboda su sami damar isar da sakonsu akan...
Kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya amince da daftarin kuduri da kasar Amurka ta gabatar mata na kafa sansanin sojojin kasa da kasa a yankin Gaza. An amince da kudurin ne a jiya litinin inda aka amince da shirin na Donald Trump kan Gaza kuma ta bada umarnin kirkiro dakarun kasa da kasa na...
Ministan harkokin wajen kasar Afrika ta kudu Ronald lamola a jiya a joharnesbourg yayi gargadi game da kwaso falasdinawa da aka yi a baya bayan nan yana nuna irin yunkurin da ake yi na tilasta musu barin yankin gaza, inda ya bayyan shirin a matsayin wani bangare na shirin korar falasdinawa daga gidajensu. Pretoriya ta...
An ba wa hamata iska a Hedikwatar Jam’iyyar PDP da ke Abuja a tsakanin bangarorin da ke hamayya da juna. Fadan ya barke ne bayan bangarorin sun halarci ofishin domin gudanar da tarukansu daban-daban a safiyar Talata. Idan ba a manta ba, bangaren Ministan Abuja, Nyesom Wike, wadanda uwar jam’iyyar ta dakatar a yayin babban...
“Cikin hukuncin Allah, sojojin Daularmu sun kama ‘Kwamandan Runduna’… bayan ya gudu daga harin kwantan-ɓauna… Bayan mun yi masa tambayoyi, Mujahidai suka kashe shi.” An kuma wallafa wani hoto a kafafen sada zumunta da ya nuna Janar Uba a ɗaure. Har yanzu rundunar sojin Nijeriya ba ta fitar da wata sanarwa game da wannan lamari...
Gwamna Ahmed Idris na Jihar Kebbi ya ba da tabbacin cewa jami’an tsaro za su ƙwato ’yan matan da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Kwalejin ’Yan Mata ta GGCSS Maga da ke Ƙaramar Hukumar Danko Wasu ta jihar cikin ƙoshin lafiya. Gwamnan ya bayar da tabbacin ne a yayin ganawarsa da iyayen...
Alkaluman da suka fito daga kungiyar masu kera motoci ta kasar Sin sun nuna cewa, adadin motocin da kasar Sin ke fitarwa waje ya karu da kashi 15.7 bisa dari a cikin watanni 10 na farkon shekarar 2025 bisa na makamancin lokacin bara. Kasar ta fitar da motoci sama da miliyan 5.6 a tsakanin...
Firaministan kasar Sin Li Qiang ya isa birnin Moscow na kasar Rasha a yau Litinin domin halartar taro karo na 24 na majalisar shugabannin kasashe mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO). Bisa gayyatar da firaministan kasar Rasha Mikhail Mishustin ya yi masa, Li zai halarci taron na SCO a ranakun 17 da 18...
Ya bayyana cewa, zaman bitar ya yi daidai da umarnin Sufeto Janar na ‘Yansanda, IGP Kayode Egbetokun, musamman kan karfafawa jami’an rundunar. Don haka, CP Bakori ya umurci Kwamandojin da su zurfafa wayar da kan jama’a a yankunan karkara da birane domin sanar da su irin rawar da suke takawa wajen wanzar da zaman...
Na’ini: Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Da Kansa Ya Jagoranci Yaki Kwanaki 12 Da Aka Kaddamar Kan Iran
Jagoram juyin juya halin Musulunci da kan sa ya jagoranci yaki da harkokin al’umma a lokacin yakin wuce gona da iri na karshe kan Iran Kakakin Rundunar Tsaron kare Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC), Brigadier Janar Ali Mohammad Na’ini, ya tabbatar da cewa: Maƙiya ‘yan sahayoniyya ba su da yanayin sabon yaƙi, kuma abin da...
Wata sanarwa da gwamnati ta fitar a Gaza ta yi gargadin cewa: Akwai wani bala’i da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin jin kai Ofishin Yada Labarai na Gwamnati a Zirin Gaza ya fitar da Sanarwar Manema Labarai Mai Lamba (1021) a yau, Litinin, inda ya yi magana kan sabbin ci gaba da...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta kama ƙunshi 66 na ganyen tabar wiwi a wani samame da ta kai a garin Deba, bayan samun wasu sahihin bayanan leƙen asiri. Mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:30 na dare a ranar 16 ga Nuwamba,...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta kama ƙunshi 66 na ganyen tabar wiwi a wani samame da ta kai a garin Deba, bayan samun wasu sahihin bayanan leƙen asiri. Mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:30 na dare a ranar 16 ga Nuwamba,...
Ya kuma yi Allah wadai da kisan wani jigo na Jam’iyyar APC, Umar Moriki, da kuma sace-sacen jama’a da aka yi a Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara, inda aka sace iyalai baki daya, ciki har da mata da yara. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai MACBAN Ta Nemi Amurka Ta Cire Sunanta Daga Jerin Waɗanda...
Shugaba Bola Tinubu a ranar Litinin ya gargadi jami’an shari’a a fadin kasar cewa dole ne a tabbatar da adalci ga kowa – Talaka da mai kudi, ba tare da nuna wata wariya ba, ko karɓar cin hanci, “bai dace adalci ya zama na sayarwa ba.” Da yake jawabi a yayin bude taron alkalan Nijeriya...
Ma’aikatar raya al’adu da yawon bude ido ta kasar Sin ta fitar da sanarwa a jiya Lahadi, wadda ke kira ga al’ummunta da su yi taka-tsantsan a kwanakin nan wajen zuwa yawon bude ido kasar Japan. Game da hakan, masani a kwalejin bincike ta Nomura Takahide Kiuchi, ya bayyana a jiyan cewa, raguwar yawan Sinawa...
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Taraba, Rt Hon. Kizito Bonzena, tare da ’yan majalisar 15 sun sauya sheka daga jam’iyyarsu ta PDP zuwa APC. A saifyar Litinin ne Rt Hon. Kizito Bonzena ya gabatar da takardarsa ta ficewa daga PDP tare da sauran mambobin zuwa APC. Ya bayyana cewa da sauyin shekar tasu, yanzu APC ce...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƴan Bindiga Sun Sace Ɗalibai Ƴan Mata, Sun Kashe Mataimakin Shugaban Makaranta A Kebbi November 17, 2025 Manyan Labarai Mutane 42 Sun Mutu A Wani Hatsarin Tankar Dizal Da Motar Masu Umrah A Hanyar Makka November 17, 2025 Manyan Labarai Ba Mu Samu Labarin Kai Wa Laftanar...
Rahotanni da suka fito daga yankin falasdinu sun tabbatar da cewa sojojin Isra’ila sun kai hari a sansanin yan gudun hijira dake gabar yammacin kogin Jodan kuma sun kashe wasu matasa guda biyu,da suka hada da jadalla jihar jumaa dan shekara 15 dake sansanin yan gudun hijira na fara’a a yammacin garin Tubas. Hukumar bada...
Tawagar wasannin Wushu na kasar Iran ta nuna rawar gani sosai a gasar hadin kan kasashen musulmi da ake yi a kasar saudiya inda ta samu lambobin yabo guda 4 wato Azurfa 1 tagulla 1 da kuma zinariya 2 a ranar karshe na gasa a wannan bangaren. A bangaren mata kuma Sara shafi’I wacce ta...
Shugaban hukumar makamashin nukiliya ta kasar iran Mohammad Eslami ya bayyana cewa harin da Amurka da isra’ila suka kai kan tashohin nukiliyar ta a tsakiyar watan yuli ya nuna cewa Amurka da kawayenta ciki har da isra’ila suna harin naurorin kimiyya na jamhuriyar musulunci ta iran ne. Shugaban ya fadi hakan ne a wata hira...
Hamas Da Sauran Bangarorin Falasdinawa Sun yi Watsi Da Shirin Aikewa Da Dakarun Kasashen Waje A Yankin Gaza
Rahotanni sun bayyana cewa bangarorin falasdinawa sun yi watsi da kudurin da aka kaddamar ga kwamitin sulhu na majalsar dinkin duniya na shirin aikewa da sojojin ketare zuwa yankin Gaza sun yi kira ga kasar Aljeriya da sauran mambobin da ba na dindin ba a kwamitin sulhu da su kalubalance shi. Daftarin kudurin an tsara...
’Yan ta’adda sun harbe Mataimakin Firinsifal har lahira, sa’annan suka yi garkuwa da dalibai 25 a Makarantar ’Yan Mata ta Gwamnati (GGCSS) da ke yankin Maga a Karamar Hukumar Danko Wasagu ta jihar Kebbi. Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun bindige Malam Hassan Yakubu Makuku ne a yayin da yake kokarin kare daliban, a...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja November 16, 2025 Manyan Labarai Falana Ya Shawarci Waɗanda Suka Biya Kuɗin Fansa Su Kai Gwamnati Kotu Don Ta Biya Su November 16, 2025 Manyan Labarai Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara...
’Yan sanda sun yi nasarar kama wasu ’yan bindiga biyar tare da ƙwace tarin makamai a hannunsu a yankin Zuru–Tadurga da ke Jihar Kebbi. Rundunar ’yan sanda ta musamman da ta kama su, ta bayyana cewa, ’yan bindiga suna cikin waɗanda suka kai hare-hare a kan al’ummomin Zuru a kwanakin baya. Ta ƙara da cewa...
’Yan bindiga sun kashe mutum 3 tare da yin garkuwa da wasu 64 a ranar Asabar a Karamar Hukumar Tsafe ya Jihar Zamfara. Cikin waɗanda ’yan ta’addan suka kashe har da wani jigon jam’iyyar APC, Hon. Umaru Moriki wanda aka bindige a kan hanyar Gusau zuwa Tsafe, waɗanda aka yi garkuwa da su kuma har...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Matsayar doka ta zama babbar abun tattaunawa a Najeriya yayin da jam’iyyar PDP ta gudanar da taron ta na kasa duk da mabanbantan hukunce hukunce daga kotuna biyu. Umarnin kotu guda yana goyon bayan taron, ɗayan kuwa ya haramta shi gaba ɗaya. Wadannan hukunce hukunce ba baiwa...
Babban lauya kuma mai kare haƙƙin ɗan Adam, Femi Falana (SAN), ya bai wa ƴan Nijeriya shawara da su kai Gwamnatin Tarayya ƙara don neman a mayar musu da kuɗin fansar da suka biya yayin da aka yi garkuwa da ƴan uwansu. Ya ce gwamnatin ta kasa sauke babban nauyin da kundin tsarin mulki ya...
Babban jirgin ruwan yaki mai dakon sojojin kasa da sauran kayan yaki da ake amfani da su a kan-tudu samfurin 076 irinsa na farko a kasar Sin mai suna Sichuan, ya koma tashar jiragen ruwa da ke birnin Shanghai da misalin karfe 5 na yamma a yau Lahadi, bayan kammala gwajinsa na farko a teku....
Kungiyar kasa da kasa mai kula da ‘yan hijira ( IOM) tana yin kira ga shugabannin kasashen duniya da su bayar da kariya da kare hakkokin wadanda suke rayuwa a yankunan da suke fama da matsalar sauyin yanayi. A taron da ake yi a yanzu haka a garin Belem na kasar Brazil kungiyoyi masu zama...
Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya buƙaci al’umma su ƙara kula da tsaro tare da yin aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomin tsaro, yayin da ’yan bindiga suka fara kai hare-hare a ƙauyukan da ke iyaka da Jihar Katsina. Sarkin, ya yi wannan kira ne yayin ziyarar jaje da ya kai wa al’ummar...
Yanzu haka ana gudanar da taron bangarorin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar tinkarar sauyin yanayin duniya ta Majalisar Dinkin Duniya, karo na 30, wato “COP 30” a takaice, a birnin Belem na kasar Brazil, inda a ranar Juma’a 14 ga wata aka kira wani taro a gefe mai taken “Dabarun Kasar Sin Na Tinkarar...
Richard A falk Tsohon mai bincike kan laifukan yaki da HKI ta tafka kan alummar Gaza da majalisar dinkin duniya ta nada ya fuskanci matsalar a kasar kanada inda aka tsare shi tare da yi masa tambayoyi a wata tafiya da yayi don halartar taron dake da alaka da yankin Gaza. Falka dan shekara 92...
Rahotanni sun nuna cewa tsohon ministan harkokin wajen kasar iran mohammad Javad zarif yace isra’ila ce kawai gwamnatin dake ayyukan nukiliya ba bisa kaida ba a yammancin asiya, amma take sukar iran duk da cikakken hadinkai da take bayarwa ga dokokin hukumar nukiliya kuma wadda ke da tarihi mafi girma na binciken hukumar nukiliya ta...
Amfani da jami’an tsaro: Abu na farko dai dole ne kungiyoyi su yi aiki tare da yansanda, NSCDC, da jami’an tsaro na sirri wajen tsara tsare-tsaren tsaro a ranar da za su buga wasa, domin kuwa Bahaushe na cewa, “tun za a, ake shiri ba sai an dawo ba”, hakazalika yana da mahimmanci a...
Ɓangaren Shari’a a Nijeriya, yana da alhakin bayyana dokoki, kare kundin tsarin mulki, da kuma tabbatar da adalci. An tsara tsarin shari’a a karkashin jagorancin Kotun Ƙoli inda Alƙalin Alƙalan Nijeriya (CJN) ke kula da ita, sannan Kotun Ɗaukaka Ƙara da Manyan Kotuna a matakin jiha da tarayya. Daga cikin manyan haƙƙoƙin da...
Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN Sun Shaida Adawar Sassan Kasa da Kasa Da Burin Masu Tsattsauran Ra’ayi Na Japan Na Ruguza Odar Kasa Da Kasa Ta Bayan Yakin Duniya Na 2 Dangane Da Batun Taiwan
Kalaman tayar da husuma na firaministar Japan Sanae Takaichi, dangane da batun yankin Taiwan na kasar Sin, na ci gaba da shan suka da Allah wadai daga sassan kasa da kasa. Wani sakamakon kuri’un jin ra’ayin al’umma da kafar CGTN ta gabatar ya nuna yadda akasarin masu bayyana mahanga suka amince da cewa, matakin na...
Kamar ‘yan wasa da masu horarwa, an hana jami’an wasa shiga ayyukan yin caca bisa ga ka’idojin TFF, da kuma na FIFA da hukumar gudanarwa ta Turai (Uefa), masu gabatar da kara na Turkiyya sun bayar da umarnin tsare mutane 21 ciki har da alkalai 17 da shugabannin kungiyoyin kwallon kafa biyu a wani bangare...
Jaridar “ma’ariv’ ta buga labarin dake cewa Fira minista Netanyahu yana rayuwa cikin zullumi da tsoro mai tsanani akan hukuncin da kotu za ta yanke masa. Jaridar ta ‘yan sahayoniya ta kuma ce yadda ake yin matsin lamba daga waje domin ganin an yafe wa Netanyahu,yana nuni ne da yadda Fira ministan yake cikin tsoro...