2025-12-01@17:42:37 GMT
إجمالي نتائج البحث: 12114

«Jaridar Leadership»:

    Daga Shamsuddeen Mannir Atiku  Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta karɓi daftarin kasafin kuɗin shekarar 2026 da ya zarce naira miliyan dubu dari tara da tamanin da biyar daga bangaren zartarwa jihar. Da yake gabatar da kasafin kudin a  zauren majalisar, Gwamna Malam Uba Sani ya bayyana kasafin a matsayin na sauye-sauye da ci-gaba wanda aka...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismael Baqaei ya bayyana cewa Amurka ce Babbar barazana ga zaman lafiya da tsaro a duniya, saboda ganin abinda take yi a halin yanzu a kasar Venezuela da kuma wasu kasashen Afirka. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalyo kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar yana fadar haka...
    Paparoma Leo 14 wanda yake ziyarar aiki na kwanaki uku a kasar Lebanon ya gana da shugaban kasar Lebanon Josept Aun da kuma manya-manyan malamai da shuwagabannin kungiyoyin yan siyasa a kasar Lebanon. A jawabin da ya gabatar a gaban wadannan shuwagabannin kasar Lebanon Lio na 14 ya bukaci, su rungumi zaman tare da kuma...
    Anicen Ekane dan adawa na jam’iyyar African Movement for New Independence yana daga cikin fitattun yan  siyasa a kasar Kamaru, kuma yana goyon bayan Issa Chiroma a zaben shugaba kasa wanda aka gudanar a kasar a cikin watan Octoban da ya gabata. Issa Chiroma dai ya shelanta cewa shi ya lashe zaben shugaban kasa wanda...
    Tawagar kungiyar raya tattalin arziki na kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta bar bar birnin Bissau da sauri bayanda shugaban kasa Umaro Sissoco yayi barazanar zai fiddasu daga kasar ida sun kara jinkirin fita. A cikin watan da ya gabata ne kungiyar ta aiki tawagar zuwa kasar ta Gunea Bissai saboda gabatar da shawarorin kan yadda...
    Hukumar kididdiga ta HKI ta basa sanarwan cewa yawan yahudawa da suke ficewa daga haramtacciyar kasar . Tashar talabijin ta Almayadeen na kasar Lebanon ta nakalto hukumar na bada labarin cewa a shekara ta 2010 yawan masana wadanda suke da shahadar Jami’a ya karu ha rya kai kashi 46% sannan wannan adadin ya cilla sama...
    Shugaban Ƙungiyar Iyaye na Jami’ar MAAUN, Alhaji Mustapha Balarabe, ya ƙaryata rahotannin da ke cewa jami’ar ta yanke wasu kuɗi masu yawa domin yaye ɗalibai. A wata sanarwa da ya fitar tare da sakataren ƙungiyar, Hajiya Habiba Sarki, ya ce koken da aka kai wa PCACC da kuma rahotannin da aka wallafa ba su da...
    Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III, ya shawarci gwamnonin jihohin Arewa 19 su riƙa sauraron masu sukarsu tare da amfani da shawarwarin da ake ba su domin inganta salon mulkinsu. Ya bayar da wannan shawara ne a ranar Litinin, yayin taron haɗin gwiwar Gwamnonin Arewa da Sarakunan Gargajiya a Kaduna. ’Yan sanda sun gano zinaren N23m...
    ’Yan sanda sun gano tare da miƙa wa wata mata zinarenta da kuɗinsu ya kai Naira miliyan 23 da suna ɓace a lokacin wani harin Boko Haram shekara 13 da suka gabata a Jihar Borno. Jami’an tsaro da ke sintiri a kan iyakar Jihar Borno da Nijar ne suka gano kayan zinaren da suka ɓace...
    ’Yan sanda sun gano tare da miƙa wa wata mata zinarenta da kuɗinwu ta kai Naira miliyan 23 da suna ɓace a lokacin wani harin Boko Haram shekara 12 da suka gabata a Jihar Borno. Jami’an tsaro da ke sintiri a kan iyakar Jihar Borno da Nijar ne suka gano kayan zinaren waɗanda suka haɗa...
    Daga Bello Wakili  Najeriya ta ƙarfafa ƙoƙarinta na kawar da cutar HIV nan da shekarar 2030, inda Uwargidar Shugaban Kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira ga ’yan Najeriya, shugabanni da jami’an lafiya su haɗa hannu wajen cimma wannan manufa. Yayin jawabi a bikin ranar Yaki da Cutar AIDS ta Duniya ta 2025 da aka...
    Daga Ali Muhammad Rabi’u  ’Yan bindiga kimanin guda huɗu dauke da makamai sun kai hari a garin Eruku da ke ƙaramar hukumar Ekiti a jihar Kwara, inda suka sace wani manomi mai suna Mista Aasaru. Rediyon Najeriya ya ruwaito  cewa wannan hari shi ne na biyu da aka kai wa garin Eruku cikin wata guda,...
    Hukumomi a Gaza sun ce akalla Falasdinawa 357 ne sukayi shahada yayin da wasu 903 suka jikkata a hare-haren Isra’ila tun bayan da yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki a ranar 10 ga Oktoba. Yawancin wadanda abin ya shafa mata ne da yara, in ji ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza a cikin wata sanarwa....
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta bayyana cewa Isra’ila na jinkirta aiwatar da mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma. Mai magana da yawun Hamas, ya bayyana cewa duk da cewa kungiyar ta na girmama yarjejeniyar tsagaita wuta sosai, gwamnatin mamayar Isra’ila na jinkirta aiwatar da mataki na biyu na yarjejeniyar, wanda...
    Daga Abdullahi Jalaluddeen  Gwamnatin Jihar Kano ta sha alwashin daukar mataki kan masu yin haya da  babura a fadin jihar. Mai bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Sufuri, Alhaji Danladi Idris Karfi, ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a Kano. Ya ce gwamnatin ta lura da yadda aka cigaba da yin haya...
    Jamhuriyar Nijar ta sanar da cewa za ta sanyar da sinadarin uranium dinta a kasuwar duniya ga wanda ta ga dama bayan da gwamnatin kasar ta mayar da hakar uranium ga kamfanin kasar a watan Yuni. Hakar ma’adinan uranium a Nijar na daga cikin batutuwan da suka fi daukar hankali tsakanin gwamnatin soji data kwace...
    Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) za ta aika da wata babbar tawaga zuwa Bissau a wannan Litinin. Tawagar, wacce shugaban ECOWAS na yanzu ke jagoranta, Shugaban Saliyo Julius Maada Bio, ta hada da shugabannin kasashen Senegal, Cape Verde, da Togo, ko wakilansu don ganawa da sabbin hukumomi, da manyan ‘yan siyasa da...
    ’Yan bindiga sun yi garkuwa da wani fasto da matarsa da mabiyansa a yayin da suke tsaka da ibada a coci da ke a  Jihar Kogi. Wani ganau da ke cikin cocin a lokacin da aka kai harin, Adegboyega Ogun, ya ce misalin ƙarfe 9.30 na safe ’yan bindigar suka kai harin suna bude wuta....
    Ana ci gaba da ta ƙaddama kan Naira dubu ɗari bakwai da hamsin da Jami’ar Amurka ta Maryam Abacha  (MAAUN) da ke Jihar Kano ta wajabta wa ɗalibanta da suka kammala karatu biya a matsayin kuɗin bikin yaye ɗalibai. Jami’ar MAAUN ta sanya wa kowane ɗalibin da ya kammala karatu biyan Naira dubu ɗari bakwai...
    Rahotanni sun bayyana cewa ministan harkokin wajen kasar Turkiya ya iso birnin Tehran a jiya lahadi kuma  ya samu kyakkyawar tarba daga takwaransa na kasar iran Abbas Araqchi. Ziyarar tasa ana saran za ta kara fadada dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, ganin cewa dukkan kasashen biyu suna taka rawa a batutun da suka shafi yanki...
    Pars Today – Shugaban Iran, a wata ganawa da Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, ya ce a lokacin da maƙiyan ƙasashen Musulmi ke neman ƙara matsin lamba, ana sa ran ƙasashen Musulunci za su sauƙaƙa wa junansu yanayi da kuma guje wa matsaloli masu sarkakiya. Masoud Pezeshkian, Shugaban Iran, a ranar Lahadi da yamma a ganawarsa...
    Nicolas Maduro shugaban kasar Venzuwela yayi tir da barazanar da Washington ke ta nanatawa na yin amfani da karfin soji kan karakas, kuma yayi gargadi game da shirin Amurka na kwace ikon kila da rijiyoyin mai na kasar a hanyar amfani da karfin soji. Maduro yayi wannan bayanin ne a cikin wata wasika da ya...
    Fira ministan HKI Benjamin natanyaho ya bukaci yafiyar shugaban kasa game da shari’a da aka dade ana yi kan zargin da ake masa na cin hancin da rashawa da mutane da sauran yan siyasa ke Allah wadarai da shi. Mazu zanga zanga sun mamaye gidan shugaban gwamnatin isra’ila Isaac Herzog inda suka yi tir da...
    A wani bangare na huldar duplomasiya tsakanin iran da saudiya , mataimakin ministan harkokin wajen kasar saudiya Saud bin mohammad Al-sati ya gana da ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi a nan birnin tehran inda suka tattauna kan batutuwan da suka shafin alakokin dake tsakani da kuma ci gaban yankin. Ganawar wani bangare ne...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A mafi yawan ƙasashen duniya, ana ɗaukar jakadu a matsayin fuskar ƙasa kuma ginshiƙan hulɗar diflomasiyya. Saboda haka, akwai muhimman halaye da suke tilas jakadan ƙwarai ya mallaka domin ya wakilci ƙasarsa cikin mutunci, da nagarta da kwarewa.   Tun bayan da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya...
    A daidai lokacin ziyarar Paparoma Leo na XIV  shugaban Katolika na duniya a kasar Lebanon, kungiyar Hezbollah ta fitar da wata sanarwa a hukumance da aka aike masa. Kungiyar ta yi maraba da ziyarar Paparoma, ta kuma jaddada muhimmancin Lebanon a matsayin kasa mai bambance-bambance na addini da kabilu da akidu, wadda al’ummominta suke bukatar...
    Daga Usman Muhammad Zaria  Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce ya zuwa yanzu ta mayar da sama da naira miliyan 50 ga maniyyatan jihar na shekarar 2026, biyo bayan rage kudin kujerar aikin Hajji da Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta sanar. Daraktan Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya...
    Sojojin Rundunar Operation Hadin Kai (OPHK), sun samu nasarar ceto ’yan mata 12 da ’yan ta’addan ISWAP suka sace a gundumar Mussa da ke Ƙaramar Hukumar Askira/Uba a Jihar Borno. An sace su ne ranar 23 ga watan Nuwamba 2025, yayin da suke girbe amfanin gonakin iyayensu. Yaran ’yan shekaru 15 zuwa 20 ne. Wannan...
    A birnin Dublin na kasar Ireland an cire sunan tsohon sugaban “Isra’ila” Chaim Herzog,daga wata lambu na shakatawa a unguwar Ratgar, tare da maye gurbinsa da sunan Shahida Hind Rajab. Jaridar “Vadiot-Ahranot” ta ‘yan sahayoniya ta buga labarin cewa, hukumar birnin Dublin a Ireland ta amince da a sauya sunan shugaban “Isra’ila” ta shida Chaim...
    Ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinu a Gaza ta sanar da cewa; An sami shahidai 3 da aka kai su asibitin a cikin sa’o’i 24 da su ka gabata.  Shi kuwa ofishin gwamnati dake Gaza ya sanar da cewa, daga tsagaita wutar yaki zuwa wannan lokacin, sau 591 Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta keta wutar yaki. Ofishin...
    Jaridar Washington Post ta buga rahoto akan Shirin Donald Trump na aikewa da sojoji zuwa Gaza, tare da cewa tana fuskantar matsala, domin har yanzu ana Magana akan yadda za a raba ‘yan gwgawarmaya da makamansu. Jaridar ta ci gaba da cewa; Da akwai damuwa a cikin manyan biranen kasashen duniya danagne da yiyuwar a...
    Hukumar Agaji ta MDD ta sanar da cewa, kasar Somaliya ta shiga cikin wani mawuyacin yanaki saboda fari, da yanki mai yawa na kasar ya bushe bayan da aka dauki shekaru hudu a jere babu ruwan sama. Hukumar ta MDD ta kuma ce, da akwai miliyoyin mutanen kasar da suke fuskantar yunwa mai tsanani, yayin...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya gana da takwaransa na Turkiya Hakan Fidan da safiyar Lahadi a nan birnin Tehran. Ministan harkokin wajen na Turkiya ya kawo ziyarar Iran ne domin tattauna hanyoyin bunkasa alaka a tsakanin kasashen biyu da kuma tattauna halin da ake ciki a wannan yankin na yammacin Asiya. Share 0...
    ’Yan bindiga sun shiga garin Chaco da ke Ƙaramar Hukumar Wurno a Jihar Sakkwato, inda suka sace amarya da ƙawayenta guda 14. Yayin da mutane ke tsaka shagalin bikin auren, sai ’yan bindigar suka afka musu tare da tarwatsa komai. Mutum 6 sun jikkata a rikici manoma da makiyaya a Jigawa Sojoji sun ceto mutum...
    Aƙalla mutum shida ne suka jikkata bayan da wani rikici ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a ƙauyen Kangire da ke Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu a Jihar Jigawa. Ishak Ibrahim Fanini, mai taimaka wa shugaban Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu, Muhammad Uba, ya tabbatar da faruwar lamarin a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na...
    Dakarun Sojin Najeriya, sun ceto wasu mutum bakwai da ’yan bindiga suka sace a Ƙaramar Hukumar Tsanyawa da ke Jihar Kano. Wannan zuwa ne bayan mazauna Yankamaye Cikin Gari suka sanar da jami’an tsaro cewa ’yan bindiga sun shiga ƙauyensu a daren ranar Juma’a. ’Yan bindiga sun kashe tsohuwa, sun sace mutum 3 a Kano...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana halin da Falasdinu ke ciki da rauni mafi muni da aka aikata kan bil adama a doron kasa. A yayin bikin Ranar Falasdinu ta Duniya, Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta sake nanata goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke bai wa Falasdinawa, tana mai bayyana halin da suke ciki...
    An yi gangami a fadin duniya domin nuna goyan baya ga al’ummar Falasdinu a daidai lokacin da aka gudanar da bikin ranar Falasdinu a ranar 29 ga watan Nuwamba da MDD ta kebe. A faransa a gudanar da irin wannan gangamin, inda suka yi Allah wadai da mamayar da gwamnatin Isra’ila ta yi wa Gaza...
    Cinikin kasashen waje na kasar Iran a cikin watanni takwas na farko na bana ya kai tan 131,540, wanda darajarsa ta kai dala biliyan 76.5. kwatankwacin tagomashi na kashi 1.53% idan aka kwatanta da bara warhaka. Bayanin da aka samu daga hukumar kwastam ta Iran ya ce: “A wannan lokacin, an fitar da tan 105,231,000...
    Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kubutar da wasu yan mata 12 da mayakan ISWAP suka sace a gundumar Mussa da ke yankin karamar hukumar Askira/Uba da ke jihar Borno. Cikin wata sanarwa da sojojin suka fitar da maraicen ranar Asabar, sun ce yanzu haka yan matan na wani sansanin soji mai tsaro domin kula...
    A Jamhuriyar Kamaru, an sake zabar Samuel Eto’o a matsayin Shugaban Hukumar kwallon kafa ta kasar (Fecafoot) Duk da kin amincewa da Ma’aikatar Wasannin kasar ta yi. An sake zabar Eto’o ne wanda shi ne Tsohon kyaftin din kungiyar Indomitable Lions ne a wani wa’adi na tsawon shekaru hudu a kasa da shekaru hudu bayan...
    Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Najeriya (NARD) ta dakatar da yajin aikin da ta shafe kwanaki 29 tana yi, bayan wani taron gaggawa da Majalisar Koli ta ƙungiyar ta gudanar a ranar Asabar. Shugaban NARD, Muhammad Suleiman, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya wallafa, inda ya bayyana cewa an dakatar da...
    Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa ya koma jam’iyyar ADC ne saboda ita kaɗai yake gani za ta iya ceto Najeriya daga matsalolin tsaro da na tattalin arziki da take fama da su. Yayin ƙaddamar da ofishin jam’iyyar a Jihar Taraba ranar Asabar, Atiku duk da a baya ya kasance a jam’iyyar...
    Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasar najeriya Bola Ahmad tunubu ya mika sunayen mutane 32 ciki har da tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa mahamud yakubu da tsohon ministan sufurin jiragen sama femi kayode ga majalisar dokokin kasar domin a tantancesu kwanaki bayan tura sunayen mutane 3 a fara da su. Mai magana da yawun...
    Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar hizbullah ta kasar Labanon ta yi kira ga shugaban cocin katolika na duniya pope leo na 14 da zai kai ziyara kasar labanon da yayi tir da hare hare da rashin adalcin da isra’ila ke yi kan kasar labanon duk da yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma a...
    Rahotanni sun bayyana cewa iran ta yi tir da sanarwar da shugaban Amurka ta fitar na rufe sararin samaniyar kasar venuzuwela kuma ta bayyana shi a matsayin keta dokokin kasa da kasa, da kuma dokokin kula da zirga –zirgar jiragen sama. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Isma’ila Baghae ne ya fitar da wannan sanarwa...
    A ranar nuna goyon baya ga alummar falasdinu shugaban kasar Pakistan Asif Ali zardari ya jinjinawa Alummar falasdinu game da juriya da tsayin Dakar da suka nuna, yace jarumtar da suka nuna ta bude sabon shafin tarihi, don haka gudanar da bincike kan laifukan yaki da HKI ta tafka yana da muhimmanci sosai. Kasar Pakistan...
    Antonio Guterres babban sakataren majalisar dinkin duniya yayi kira da a kawo karshen mamayar yankunan falasdinawa da isra’ila ke yi da ya sabama doka, kuma yace babu ja da baya game da kudurin kafa kasashe biyu masu cin gashin kai Sakataren ya sake yin kira ne saboda ya nuna irin bukatar da ake da ita...
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya sake aike wa Majalisar Dattawa ƙarin sunayen mutum 32 domin tantance su a matsayin jakadu. Sunayen sun haɗa da manyan mutane kamar tsohon shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Femi Fani-Kayode, da Reno Omokri. Muna buƙatar taimakon ƙasashen waje kan tsaro a Najeriya — Obasanjo Yadda aka horar da mata 100 sana’o’in...
    Babban kwamandan sojojin kasa na JMI Manjo Janar Amir Hatami ya bayyana cewa sojojin JMI a shirye suke su maida martani ko kuma kai hari kan makiya a duk lokacinda suka takali kasar. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Hatami  yana fadar haka a bikin kaddamar da jiragen ruwan yaki masu suna...