2025-09-18@19:03:52 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2201
«Murja Ibrahim Kunya»:
Gwamnatin tarayya ta ce tace a shirin ta sauya wuraren dake bushe a sassan arewacin Nijeriyaza a raba naira miliyan miliyan 3.4 kuma akasarin wadanda zasu amfana da wannan za su kasance mata ta hanyar Shirin ACReSAL. Da yake jawabi a wajen bude taron kwanaki 10 na masu ruwa da tsaki kan tsarin kula...
Tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ba wa ɗalibar nan ’yar shekara 17 daga Jihar Yobe da ta lashe Gasar Turanci ta Duniya, Nafisa Abdullah Aminu, kyautar tsabar kuɗi Dala 100,000 da gida da kuma lambar girmamawa ta OON. Ya buƙaci a gayyato Nafisa da malamanta na harshen Turanci...
Wata yarinya ’yar shekara 17, Nafisa Abdullah, daga Jihar Yobe, ta lashe Babbar Gasar Harshen Turanci ta Duniya ta ‘TeenEagle’ ta shekarar 2025 da aka gudanar a birnin Landan, fadar gwamnatin ƙasar Birtaniya. Nafisa ta zama Gwarzuwar Shekarar 2025 ce baya da ta fafata ne da sama da mahalarta gasar 20,000 daga ƙasashe kusan 69...
Gwamnatin Kano ta karɓi rahoton kwamitin bincike da ta kafa domin gano haƙiƙanin gaskiya kan zargin da ake yi wa Kwamishinan Sufuri na jihar, Ibrahim Ali Namadi da shiga sha’anin belin wani da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi. Shugaban kwamitin, Barista Aminu Hussain, ne ya miƙa rahoton ga Sakataren Gwamnatin Kano, Alhaji Umar Farouk...
Gwamnatin Kano ta bayyana shirin mayar da tsohon gidan yarin nan na Kurmawa, wanda aka gina fiye da shekara 100 da suka gabata, zuwa gidan adana abubuwan tarihi. Gidan yarin Kurmawa mai ɗaukar fursunoni 690 kacal, wanda aka gina a shekarar 1910 tun a zamanin Turawan mulkin mallaka a kusa da fadar mai martaba Sarkin...
Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya amince da ware Naira Biliyan 20 a karin kasafin kudin da aka yi domin ci gaba da gyaran gine-ginen makarantu a fadin jihar. A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ilimi na jihar, Dr. Lawal Olohungbebe, ya fitar, ya ce wannan sabon tsarin zai kara karfi wajen cigaban gyaran makarantun...
Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni ya tuhumi sabon Sarkin Gudi, Alhaji Ismaila Ahmed Gadaka da ya jagoranci zaman lafiya, hadin kai, da ci gaban al’ummar masarautar sa, jiha da kasa baki daya. Gwamna Buni ya yi wannan kiran ne a ranar Litinin yayin gabatar da takardar nadin sarauta ga basaraken a hukumance a...
Shugaban kungiyar malaman addinin musulunci ko –Council Of Ulema-na Tafawa Balewa a jihar Bauchi na tarayyar Najeriya Sheikh Dan’azuki Musa tafawa balewa, yayi kira ga kasashen musulmi da kuma sauran kasashen duniya da su dauki darasi a jajircewar JMI da turjiyarta ga HKI, a kuma matsayin hanya tilo ta kawo karshen HKI. Kamfanin dillancin labaran...
Majalisar zartaswar jihar Sokoto a karkashin jagorancin Gwamna Ahmed Aliyu ta amince da kashe kudade wajen ayyuka a sassa daban daban nufin tabbatar da amana da aka dora wa gwamnati. Da yake karin haske ga manema labarai yayin taron da ya saba gudanarwa, kwamishinan yada labarai Alh. Sambo Bello Danchadi ya ce majalisar ta...
Amincewar Gwamnatin Tarayya da kashe Naira biliyan 712 biliyan don gyaran Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Legas ya haifar da ce-ce-ku-ce a faɗin Najeriya. Wannan gagarumin kashe kuɗi, da Majalisar Zartarwa ta Kasa ta amince da shi a ranar Alhamis da ta gabata, ya sanya masana harkar jiragen sama, ’yan adawa, da...
ADC ta ce, duk da cewa an tsara filin jirgin ne don karbar fasinjoji miliyan 14 a cikin shekara guda, amma rahotannin da ake da su sun nuna cewa, filin jirgin ya karbi fasinjoji miliyan 6.5 ne kawai a shekarar 2024, kasa da rabin karfinsa. Don haka, ADC ta yi kira ga daukacin ‘yan...
Gwamnatin Najeriya ta ce tana sa ran samun kimanin Naira biliyan 300 a duk shekara daga noman dabino a ƙasar. Ta ce tana fatan samun wannan kuɗaɗen shiga ne daga rabon irin dabino guda miliyan biyar da ta samar ga manoma a wannan shekara ta 2025. Darakta-Janar na Hukumar Yaƙi da Kwararowar Hamada (NAGGW), Alhaji...
Auwalu Labarina, wanda ke cikin matasa jarumai da tauraruwarsu ke haskawa a Masana’antar Kannywood, ya fito a manyan fina-finai da dama da suka hada da darasi, Kwana Casa’in, Gidan Sarauta da kuma shirin nan na Labarina, ya kuma samu kyautuka da dama da suka danganci wannan sana’a tasa ta fim a lokuta daban-daban. Kazalika, ya...
Ministan harkokin wajen kasar Aran Abbas Aragchi ya bayyana cewa JMI da kuma kasar Japan suna iya jagorantar kasashen duniya zuwa ga rabata daga makaman kare dangi. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Ministan yana fadar haka a wani rubutu da yayi, wanda kuma aka buga a jaridar Asahi Shimbun ta kasar...
Ƙungiyar Hamas ta sake jadadda matakinta na cewa ba za ta taɓa ajiye makami ba, har sai lokacin da duniya ta amince da samar da ’yantacciyar ƙasar Falasɗinu a yankin Gabas ta Tsakiya, wani abu da zai sake mayar da yarjejeniyar zaman lafiya da ake ƙoƙarin ƙullawa baya. A halin da ake ciki yanzu haka...
Rundunar sojin Jamus ta fara gudanar da aikin jefa kayayyakin gaji da suka hada da abinci da magunguna ta sama a Zirin Gaza. Ma’aikatar Tsaron Jamus da ke Berlin, fadar gwamnatin kasar, ce ta tabbatar da hakan, inda ta ce jiragen rundunar sojin sama sun ajiye kunshin tallafi 34 dauki da tan 14 na...
Ya danganta mutuwar ta ƙanana da matsakaitan sana’oi a ƙasar, kan rashin samun rancen kudaɗen da za su ci gaba da ka kasuwancin su da rashin kayan aiki, da rashin kasuwa da ba a samu sosai da kuma rashin gudanar da ingantaccen shiri, kafin su fara gudanar da kasuwancinsu. Ya sanar da cewa, ya zama...
Wani mutum ya rasu, yayin da wasu biyu suka jikkata sakamakon rikici da ya ɓarke tsakanin mazauna ƙauyen Kuchibiyi da jami’an ’yan sanda a Ƙaramar Hukumar Bwari da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja. Wani mazaunin ƙauyen, Samuel Dangana, ya shaida wa wakilinmu ta waya cewa rikicin ya samo asali ne yayin da wasu da ake...
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce gwamnatinsa na shirin mayar da mutum 5,000 gida daga sansanin ‘yan gudun hijira kafin wucewar damina domin su samu damar yin noma. Mutanen za su fito ne daga garuruwan Goniri, Bula Kuriye, Mayanti, Abbaram, da Darajamal. Ma’aikatan jinya sun dakatar da yajin aiki a faɗin Najeriya Rufe...
A’isha ƴar shekara uku da suke zaune a ƙarƙashin inuwar bishiyar ɗogoyaro a wani ƙauye mai nisa a yankin Arewa maso Gabas (sansanin gudun hijira). Babu takalmi a ƙafarta, ta yi shiru, saboda radaɗi da take ji. ƙafafuwanta sirara sun yi rauni, cikinta ya dan kumbura saboda yunwa, idanunta sun fito tana cikin halin da...
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Suna fatan haɓakar musayar kasuwanci tsakanin Iran da Pakistan ta haura dala biliyan 10 Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bar birnin Tehran a wannan ranar Asabar din zuwa Islamabad na Pakistan a wata ziyarar aiki a kasar bisa gayyatar da fira ministan Pakistan Shehbaz Sharif ya yi masa....
Ƙungiyar Ma’aikatan Jinya ta Najeriya (NANNM), ta dakatar da yajin aikin gargaɗi na kwanaki bakwai da ta fara a faɗin ƙasar nan. Ƙungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata takarda da shugabanta ƙasa, Haruna Mamman, da sakatarenta, T.A. Shettima, suka sanya wa hannu. Rufe gidan rediyo ya haifar da cece-ku-ce a Neja Jami’ar Umaru Yar’adua...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban kasar Iran Masuod Pezeshkiya ya yi juyayin shahadar Isma’ila Haniyya marigayi shugaban kungiyar Hamasa a nan Tehran shekara guda kenen. Ya kuma jaddada cewa JMI ba za ta taba manta da shi ba. Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto shugaban yana bayyana wannan juyayin a ranar da Haniya yake cika shekara guda da shahada,...
Kungiyar wasan Taekwondo ta JMI kuma guragu, sun zama zakara a wasan taekwondo gurago sun lashe gasar ta Asia karo na 10 a jere. Kanfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto cewa an gudanar da gasar ne a kasar Malasiya, kuma yan wasa 107 ne daga kasashe 18 suka sami damar halattar gasar...
An yi jana’izar Marigayi Sarkin Gudi da ke Jihar Yobe, Alhaji Isa Bunuwa Madugu Ibn Khaji, ranar Juma’a a Abuja, inda ya rasu a wani asibiti bayan fama da jinya. Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni ya ranar Juma’a ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar wajen hakartar taron. Sanarwar da Mamman Mohammad daraktan yada labarai na gwamna...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila na da burin kawo cikas ga harkokin tsaro a yankin, yana mai kira ga daukacin kasashen yankin da su yi taka tsantsan wajen tunkarar irin wannan makirci. Araghchi ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da mataimakin firaministan Hadaddiyar Daular...
Yayin da yakin kisan kare dangi na “Isra’ila” ya shiga cikin wata na 22 a Gaza, wani babban wakilin shugaban kasar Amurka Donald Trump, Steve Witkoff, ya zagaya wuraren raba abinci da Amurka ke da da’awar cewa ta kafa domin taiamakawa wajen ayyukan jin kai, duk da cewa sojojin Isra’ila na ci gaba da kai...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Matukar dai Trump ya bukaci dakatar da inganta sinadarin Uranium gaba daya a Iran, to ba za a cimma wata yarjejeniya ba Ministan harkokin wajen Iran Sayyid Abbas Araqchi ya jaddada a wata hira da jaridar Financial Times cewa: Iran na neman a biya ta diyya kan...
Rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi ta ce ta ceto wasu mutane uku da aka yi garkuwa da su, bayan sun yi artabu da wasu da ake zargin sun yi garkuwa da su a wani mummunan musayar wuta da aka yi a tsaunin Shanga. Waɗanda aka yi garkuwan da su sun haɗa da: Muhammad Nasamu Namata...
Rundunar sojin ruwan Najeriya ta bayyana aniyar kafa sansaninta a Ƙaramar Hukumar Yauri ta Jihar Kebbi a wani mataki don bunƙasa harkokin tsaron iyakokin ruwa. Hakan na zuwa ne bayan da wata tawagar manyan jami’an sojojin ruwan suka kai ziyara gidan gwamnatin Jihar Kebbi. Ɗaliban da aka sace a Binuwai sun kuɓuta ’Yan Najeriya miliyan...
“Kiyasin ƴan Nijeriya miliyan 20 ke rayuwa da cutar hanta, kuma mutum miliyan 18.2 sun kamu ne da cutar rukunin B, sannan wasu mutum miliyan 2.5 sun kamu da cutar rukunin C. Abin takaici, ƴan Nijeriya 4,252 ne ke mutuwa a duk shekara sakamakon ciwon hanta da aka kasa maganceta ke haifarwa,” ya shaida. A...
Tarihin dan’adam ya nuna yadda ƙabilu daban-daban, ke nuna ƙin amincewa da auratayya ta haɗin gambiza a tsakanin ƴaƴansu da wasu ƴan ƙabilar da ba tasu ba. Hatta a cikin ƙabila daya ana samun wannan nuna wariya, tsakanin dangi, ko masu hali da talakawa. Hatta a tsakanin addini daya, bambancin aƙida ko fahimta na sa...
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana naɗin Saidu Yahya a matsayin sabon Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafen Jama’a da yaƙi da cin hanci da rashawa (PCACC), bayan ƙarewar wa’adin tsohon shugaban, Barrister Muhuyi Magaji Rimin Gado, a watan Yuni. Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ta...
A cewar Adelabu, har yanzu dai wutar lantarki ne ƙashin bayan kamfanoni a Nijeriya da kuma tattalin arziki, ya nemi haɗin kan dukkanin wadanda lamarin ya shafa domin sake farfaɗo da sashin wutar lantarki yadda ya kamata. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
Kamfanin sadarwa na MTN ya sanar da cin ribar Naira biliyan 414 a watanni shida na farkon shekarar 2025 a Najeriya. Kamfanin ya bayyana hakan ne a rahotonsa na karshen wata shidan da ya gabatar a gaban Hukumar da ke Kula da Kasuwar Hannun Jari ta Najeriya a ranar Alhamis. Za a kashe biliyan 712.26...
Majalisar Zartarwa ta Kasa ta amince da kashe Naira biliyan 712.26 don yi wa wani sashe na filin jirgin saman a Murtala Muhammad da ke Legas garambawul. Hakan dai ya biyo bayan zaman majalisar wanda Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta a Abuja ranar Laraba. NAJERIYA A YAU: Me dokar kasa ta ce kan...
Yayin da yajin aikin gargadi na kasa baki daya da kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta kasa (NANNM) ta kira ya shiga rana ta biyu, iyalai sun fara kwashe ‘yan uwansu daga asibitocin gwamnati zuwa masu zaman kansu a jihar Filato. A Asibitin Kwararru na Jihar Filato, dogon layin masu amsar katin asibiti don neman...
Allah Ya yi wa Mai Martaba, Sarkin Gudi Alhaji Isa Bunuwo Ibn Khaji rasuwa a asibitin Nizameye da ke Abuja ranar Alhamis. Mai martaba Sarkin wanda ke garin Gadaka a Ƙaramar hukumar Fika cikin Jihar Yobe ya rasu ne bayan ya yi fama da jinya. Gwamnatin Jigawa ta horas da malamai 20,000 fasahar sadarwar zamani Peter...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta horas da Malaman makarantun sakandare kimanin dubu 20 ilimin fasahar sadarwar zamani (digital). Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi ne ya bayyana hakan a lokacin da ya karɓi baƙuncin tawaga daga Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta ƙasa (NITDA) da Cibiyar Zaman Lafiya ƙarƙashin jagorancin Farfesa Hauwa Ibrahim da take Amurka, a...
Melaye wanda shi ne dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a zaben jihar Kogi a 2023, har yanzu bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba a nan gaba. Sai dai rahotanni na nuni da cewa, yana iya sauyawa zuwa jam’iyyar ADC – wata gamayyar jam’iyyar adawa da a baya-bayan nan ta jawo hankalin wasu jiga-jigan...
Tawagar kananan yan wasan damben gargajiya na kasar Iran sun zama zakara a wasannin da aka gudanar a na wannan shekara ta 2025 tare da Zinari guda, azurfa guda da kuma Tagullah 4. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jami’an gasar wasan na damben gargajiya na kasar Iaran suna fadar haka a...

Sin Na Ci Gaba Da Kyautata Rayuwar Al’umma Ta Amfani Da Hidimomin Dijital Da Na Kirkirarriyar Basira
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tsohon ɗan wasan tsakiyar Barcelona, Carles Perez, yana kwance a asibiti a ƙasar Girka bayan da wani kare ya cije shi a al’aurarsa yayin da yake yawo da nasa karen a Thermi, a wata unguwa a Thessaloniki, ranar Talata. Perez, mai shekaru 27, yana ƙoƙarin raba karensa da wani da suke fada lokacin da ya...
Sama da mutum 5,000 ne suka tsere daga gidajensu a Jihar Katsina, sakamakon sabbin hare-haren da ’yan bindiga suka kai a Ƙananan Hukumomin Bakori da Faskari. Mutane daga ƙauyuka sama da 10 sun nemi mafaka a garin Bakori, inda da dama ke zaune wajen ’yan uwansu, yayin da wasu ke kwana a waje ba tare...
Tawagar Iran ta fice daga taron majalisun dokokin kasashen duniya kafin fara jawabin jami’in gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a zaman taron A wata gagarumar nuna rashin amincewa da tushen zaluncin da ya addabi duniya, tawagogin kasashen Iran, Yemen, da Falasdinu sun fice daga zaman taron Majalisar Dinkin Duniya a Geneva, bayan da shugaban majalisar dokokin...
Da alama tallafin da matar Shugaban Kasa, Sanata Remi Tinubu ta ba wadanda hare-haren jihar Binuwai ya raba da muhallansu na Naira biliyan daya ya bar baya da kura. Kwana daya da bayar da tallafin, ’yan gudun hijirar sun fito suna zanga-zangar yunwa, amma kakakin hukumar bayar da agaji ta jihar (SEMA), Terna Ager, ya...
Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da shirin tallafi guda biyu da suka kai fiye da naira miliyan 392, ga membobin kungiyar direbobi ta NURTW da kuma ƴan kungiyar mahauta a jihar Jigawa. Wannan tallafi wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatinsa na inganta rayuwar masu sana’o’in da ke taka muhimmiyar rawa a rayuwar yau da kullum....
“Muna kira ga gwamnatin jiharmu da ta kawo mana agaji da gaggawa domin da yawa daga cikin kaburburan da ke makabartar, sun rufta bayan ruwan saman, wannan aikin ya fi karfin mu.” In ji shi. A halin da ake ciki dai, rundunar ‘yansandan jihar Borno ta gaggauta gudanar da tantancewa a wurin tare da...
Kwamitin da Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umari Radda, ya kafa domin binciken ayyukan makarantun gaba da sakanadare masu zaman kansu na jihar, ya tabbatar da cewa, 37 cikin 39 ba su da rajista da gwamnati. Shugaban kwamitin, Farfesa Ahmed Muhammad Bakori, ne ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar...