2025-11-03@14:55:27 GMT
إجمالي نتائج البحث: 782
«Uwargidan Gwamnan Katsina»:
Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da aikin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a Kasuwar Dutse Ultra-Modern Market, inda ya cika alkawarin gwamnatinsa na samar da tsaftataccen makamashi ga ‘yan kasuwa a jihar Jigawa. Aikin wanda Hukumar Samar da Tattalin Arzikin Kasa da Samar da ayyukan yi ta Jihar Jigawa ta...
Ana fargabar mutuwar wasu mutane masu ababen hawa da wasu da ke hanya sakamakon faɗuwar wata tankar mai da ke ɗauke da mai a ranar Juma’a ta kuma tada gobara a hanyar Abeokuta zuwa Sagamu a Jihar Ogun. An samu rahoton cewa tankar ta faɗi ne ta gefenta sannan man da ke ciki ya zube...
Sabbin Gonakin Da Za A Magance Zaizayewar Kasa A Sin A Karshen Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar Na 14 Sun Kai Muraba’in Kilomita 340,000
Bisa labarin da ma’aikatar harkokin albarkatun ruwa ta kasar Sin ta bayar a kwanakin baya, ana sa ran cewa, fadin sabbin gonakin da za a shawo kan matsalar zaizayewar kasa a Sin a karshen shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 14 ya kai muraba’in kilomita dubu 340, fadin gonakin da aka tabbatar da...
Uwargidan Shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta ƙaddamar da sabon Asibitin Koyarwa na Tarayya (FMC) da aka gina a garin Kumo, Ƙaramar hukumar Akko ta Jihar Gombe An gudanar da bikin ƙaddamarwar ne tare da halartar Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya da kuma Ministan Kula da Lafiya da Walwalar Jama’a, Farfesa Ali Pate. NAFDAC...
Wata gobara da ta tashi a daren Alhamis ta lalata wani ɓangare na ɗakin kwanan dalibai mata a Jami’ar Jihar Gombe, tare da jikkata dalibai uku. Ana zargin gobarar ta tashi ne sakamakon fashewar gas ɗin girki a wani ɓangare na ɗakin kwanan da ke cikin harabar jami’ar. Da yake tabbatar da faruwar lamarin a...
Gwamnatin jihar Nasarawa ta ce ta ware naira biliyan biyu domin biyan kudaden tallafin karatu da alawus alawus na guraben karatu a jihar. Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana hakan ne a lokacin bikin kaddamar da biyan alawus-alawus na shekarar 2023/2024 da aka gudanar a Kwalejin Ilimi ta karamar hukumar Akwanga ta jihar. Gwamnan...
Gwamnatin jihar Kogi ta bayyana matuƙar alhininta kan mummunan hatsarin kwale-kwale da ya faru a kan Kogin Neja, inda aƙalla mutum 26 suka rasa rayukansu. Sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai da Sadarwa na jihar, Kingsley Femi Fanwo ya fitar a ranar Laraba ta ce wannan mummunan lamari ya rutsa da ‘yan kasuwa da suka taso daga ƙaramar hukumar Ibaji ta jihar...
Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya taya al’ummar Jihar Nasarawa murnar cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai da kuma Jihar Nasarawa da ta cika shekara 29 da samun ‘yancin kai. Wata sanarwa da ta sanyawa hannu kuma ta raba wa manema labarai, mashawarci na musamman ga gwamna kan harkokin yada labarai Malam...
Manyan garuruwan da suka shiga cikin wannan jerin sun haɗa da Mubi, Gusau da Azare. Ma’aikatar ta roƙi jami’an gwamnati a jihohi da sauran masu ruwa da tsaki da su sa ido sosai kan halin da ake ciki kuma su bayar da rahoto a kan lokaci. Haka kuma, ta shawarci jama’a da ke zaune kusa...
Shekara guda bayan shahadar Sayyed Hassan Nasrallah, yanayin siyasa da zamantakewar yankin ya sake yin tasiri da tunawa da shi. Nan da nan kuma shahadarsa ta zama wani muhimmin batu na samun hadin kai a tsakanin kungiyoyi masu adawa da mamaya da kuma sabunta himma ga manufofin tsayin daka. Sayyid Hassan Nasrallah, babban sakataren kungiyar...
Kungiyoyin gwgawarmaya na Hamas da Jihadul-Islami sun sanar da kai hari akan sojojin HKI da suke yin kutse a cikin yankin Gaza’ Rundunonin soja na “Al-Kassam” na Hamas da ‘Sarayal-Qudus” na Jihadul-Islami sun ce sun kai hare-haren ne akan sojojin mamayar da su ka shiga cikin yankunan Arewa da kudancin Gaza. A jiya Talata dakarun...
Sudan ta fitar da gargaɗin gaggawar samun ambaliyar ruwa a jihohi biyar bayan matakin ruwa a Kogin Nilu ya ƙaru kamar yadda rahoton gidan jaridar gwamnati Suna ya ruwaito. Rahotanni sun danganta ƙaruwar matakin ruwa da babban dam ɗin Ethiopia da aka buɗe a wannan watan. Ma’aikatar nomar rani ta Sudan ta sanar da gargadin...
Da yammacin yau Litinin ne ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya gudanar da taron nazari karo na 22, kan yadda za a sa kaimi ga mayar da addinan Sin zuwa addinan dake da salo na kasar. Yayin da ya jagoranci taron, babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya jaddada cewa, “Ya kamata mu...
Kwamitin harkokin waje da tsaron kasar Iran ya kammala dukkan shirye shirye na ficewar kasar daga yarjeniyar NPT ta hana yaduwar makaman nukliya ko na kissan kare dangi. Isma’il Riza’e shugaban kwamitin ya fadawa ya fadawa tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran kan cewa, kwamitinsa ya kammala shiri na dukkan takardu da tsare-tsaren da...
Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem ya tabbatar da cewa gwagarmaya ba za ta bari a kwance damarar ta ba, kuma za ta shiga fada irin na Karbala idan hakan ya kama, ya kara da cewa: “Za mu fuskanci duk wani aiki da zai yi wa Isra’ila hidima, ko da kuwa an mayar da...
Sau da yawa wasu mutane suna raina wanka da gyara jikinsu, Inda suka fi gane wanke jiki ko rashin amfani da turare, bayan kuma tsafta tana daga cikin imani. Abubuwan da ke kawo wari mai tashi ya addabi wadanda ke kusa; sun hada da rashin wanke jiki da lungu da sako a yayin wanka. Sannan...
An raba nakasun bakan baya ko tasgadewar kashin bayan zuwa mataki uku a ma’aunin kusurwa na “Cobb angle”: Mataki na farko: Mafi karancin nakasu (Cobb 10-25°) Mataki na biyu: Matsakaicin nakasu (Cobb 26-40°) Mataki na uku: Matsanancin nakasu (Cobb 50° zuwa sama). A Mataki na daya da na biyu, likitan fisiyo na taimakawa wajen shawo...
Mutum huɗu sun rasa rayukansu sakamakon ruftawar da ramin da suke hakar ma’adanan ya yi, a Unguwar Dura da ke Ƙaramar hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato. Mai taimaka wa gwamnan Filato Caleb Mutfwang kan harkokin ma’adanai, Solomon Dung ya bayyana cewa, “Daga abin da aka gaya min, wasu matasa maza suna aiki a...
Gabanin shekarar 2005 da gwamnatin Kano ta hana sana’ar haya da babur saboda matsalar tsaro da ta kunno kai jihar, jigilar fasinjoji ta ta’allaƙa ne da motocin haya na hayis, ko tasi, a kuma farashi mai sauƙi. Sai dai sannu a hankali, waɗannan motocin hayar suna neman zama tarihi musamman a birane saboda zuwan...
Fashewar abin damuwa ne Shugaban ya ziyarci Kaduna, “Kuma abu na gaba da muka ji shi ne an samu fashewar wani abu bayan tafiyarsa, don haka abin da ya fara zuwa a raina shi ne ko zagon kasa ne ko kuma barazana ce ta tsaro. “Na kuma damu da sanin ko an samu mace-mace, da...
Dangin wata yarinya ’yar shekara 14 a unguwar Gangare da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato, sun nemi a bi musu haƙƙi bisa zargin fyaɗen da wani mazaunin unguwar ya yi mata. Bayanai sun ce tun farko an cafke mutumin da ake zargi, Ibrahim Rawi, wanda da fi sani da Baban Siyama,...
Da safiyar yau Alhamis ne aka gudanar da gagarumin bikin murnar cika shekaru 70 na kafuwar yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kai, a babban zauren taron jama’a na Xinjiang. Kuma shugaban kasar Xi Jinping ya halarci bikin. Memba dindindin na ofishin siyasa ta kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta Sin JKS, kana shugaban majalisar...
Kuri’ar Jin Ra’ayoyi Ta CGTN: Guguwar Amincewa Da Kasar Falasdinu Ta Nuna Yadda Amurka Da Isra’ila Suka Zama Saniyar Waren Da Ba A Taba Gani Ba
Ya zuwa ranar 23 ga watan Satumba agogon Beijing, kasashe 152 cikin 193 na Majalisar Dinkin Duniya sun amince da Falasdinu a matsayin kasa. A cikin kasashe biyar masu kujerun dindindin a kwamitin sulhun MDD, Amurka ce kadai ba ta amince da kafuwar kasar Falasdinu ba. Wannan guguwar ta amincewa da kafuwar kasar Falasdinu ta...
Sojojin HKI sun amabci cewa sojoji biyu sun halaka a wani kwanton bauna da mayaka a Gaza su ka yi, daga ciki har da kwamandan rundunar “Folcan”. Kakakin sojan HKI ya bayyana cewa wanda aka kashe din shi ne Manjo Shahir Natna’il, sai kuma Midgal Haimik a wani fada da aka yi a arewacin Gaza....
Majalisar Dokoki ta Kasa ta ɗage ranar dawowarta daga hutu zuwa 7 ga watan Oktoba, 2025. Karin bayani na tafe..
Yayin da “bikin girbi na manoman kasar Sin” na takwas ke karatowa, babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS, shugaban kasar, kuma shugaban kwamitin kolin soja Xi Jinping, a madadin kwamitin kolin JKS, ya mika gaisuwar bikin, da fatan alheri ga manoma da ma’aikatan dake gudanar da ayyukan da suka shafi...
Wani jariri ya rasu a bayan mahaifiyarsa a yayin da take guje wa harin ’yan bindiga a kauyen Allawa da ke Karamar Hukumar Shiroro a Jihar Neja. Sarkin yankin Bassa, Bagudu Amos, ne ya bayyana hakan a lokacin taron tattaunawa da mata kan zaman lafiya da kare su daga cin zarafi, mai taken: “Ƙarfafa kariya...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wata cuta mai cin naman jikin dan’Adam ta yi sandin mutuwar mutum takwas yayin da wasu fiye da 60 suke kwance a asibiti a garin Malabu dake Karamar Hukumar Fufure ta Jihar Adamawa. Wannan lamari dai ya jefa fargaba a zukatan mazauna yankin. NAJERIYA A YAU: Ayyukan...
Kin Amincewar Japan Game Da Muggan Laifukan Yakin Da Ta Aikata Ya Dakatar Da Bukatar Sin Ga Hukumar UNESCO
A ranar Alhamis 18 ga watan nan, aka kaddamar da fara nuna fim din nan mai taken “Evil Unbound” a dukkanin sassan duniya, fim din da ya ba da labarin yadda a yayin yakin kin mamayar dakarun Japan, wata rundunar dakarun sojin kasar Japan ta aiwatar da wani shirin sirri, na gwaje-gwajen kimiyya ta makamai...
‘Yan Ta’addan Lakurawa Sun Sake Zama Sanadin Mutuwar Mutane Da Dama A Turmutsitsin Shiga Kwale-kwale
Al’ummar Jihar Sakkwato na cike da fargaba da alhini bayan da wasu mazauna kauyuka da dama suka rasu a hatsarin kwale-kwale a Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato. Lamarin ya faru ne lokacin da jama’a ke tserewa daga wani sabon harin da ‘yan ta’addan Lakurawa suka kai, inda kwale-kwalen da ke dauke da mutane...
Kamfanin dillancin labaran Nijeriya ya bayar da rahoton cewa, lamarin wanda ya faru ne a lokacin da ake gudanar da aikin a ƙarshen mako a masana’antar, ya yi sanadin mutuwar ma’aikata biyu ciki har da wani jami’in soji da ke aiki tare da jikkata wasu huɗu. “Na ji wani babban ƙara har sai...
Sheikh Na’im Kassima wanda ya gabatar da jawabi a jiya juma’a ya kuma kara da cewa; A halin yanzu kungiyar gwagwarmaya tana fuskantar matsanancin yanayi mai hatsari,tare da jaddada cewa; Wanzuwar HKI, manufarsa ita ce a samar da wani yanki na turai da Amurka a cikin wannan yankin domin hana al’ummar yankin ci gaba da...
An tsinci gawar Igbonna Uzoma, kwamandan hukumar da ke yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) a otel da ke birnin Kalaba, Jihar Kuros Riba, a ranar Juma’a. Rahotanni sun ce Uzoma, wanda aka dawo da shi aiki daga wata jiha zuwa Kuros Riba a kwanan nan, bai daɗe da kama aiki a sabon ofishin ba...
Miyetti Allah ta roki Gwamntin Kwara da ta sa baki kan rufe Kasuwar Kara da Shugaban Karamar Hukuma Ya Yi
An bukaci gwamnatin jihar Kwara da ta gaggauta shiga tsakani kan rufe kasuwar Kara da ke yankin Kwara ta Kudu da shugaban karamar hukumar ya yi domin ceto harkokin kasuwanci daga durkushewa. Shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen jihar Kwara, Alhaji Shehu Garba ne ya yi wannan roko a wata sanarwa da ya rabawa manema...
Dubban ’yan Nijeriya ne ke zaune a ƙasar Saudiyya ba tare da takardun izinin zama ba, musamman a biranen Makkah da Madina. Rayuwarsu cike take da fargaba da rashin tabbas, a yayin da suke yin ayyukan hannu ko ƙananan sana’o’i ba tare da wata kariya ta doka ba. A yayin aiki Hajjin shekarar nan...
Kamfanin Kasar Sin Ya Bayar Da Gudunmuwar Kayayyaki Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Sudan Ta Kudu
Kamfanin man fetur na kasar Sin (CNPC), ya mika wasu kayayyakin agaji ga dubban mutanen da ambaliya ta raba da matsugunansu a jihar Unity mai arzikin man fetur dake arewacin kasar Sudan ta Kudu. Daraktan sashen hulda da jama’a na reshen kamfanin CNPC a Afrika Ren Yongsheng, ya ce gudunmuwar ta kunshi tantuna, da barguna,...
Wata matar aure ta shiga hannu kan zargin ƙone fuskar ’yar mijinta, Fatima Talba mai shekara 17 da tafasasshen man girki, a unguwar Jiddari Polo da ke Jihar Borno. Wata majiya ta tabbatar da cewa lamarin ya faru a ranar Asabar da ta gabata, bayan wata taƙaddama da kaure tsakanin Fatima da matar ubanta. Sauya...
Albarkacin bikin murnar cika shekaru 100 na kafuwar Jam’iyyar Zhigong ta Sin, shugaban kwamitin kolin Jam’iyyar Kwaminis ta Sin, JKS, kana shugaban kasar Xi Jinping ya aika wasikar taya murna, kuma a madadin kwamitin tsakiyar JKS, ya taya dukkan ’yan Jam’iyyar Zhigong murna tare da nuna musu gaisuwa. Xi Jinping ya jaddada cewa, a kan...
Idan aka yi ɗan nazari kan tafiyar siyasar Seyi Makinde a Jihar Oyo da kuma yammacin Nijeriya gaba ɗaya, za a fahimci sosai wane ne Makinde da kuma dalilin da ya sa ya dace kowanne ɗan siyasa mai hangen nesa ya yi hattara da shi kafin 2027. Ko da yake Gwamnan Jihar Oyo, wanda ake...
Aƙalla mutane 58 ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon barkewar cutar Kwalara a ƙananan hukumomi 14 daga cikin 20 da ke jihar Bauchi. Haka kuma, an samu sabbin mutane 258 da suka kamu da cutar a faɗin jihar. Amurka ta hau kujerar-na-ƙi kan buƙatar MDD ta tsagaita wuta a Gaza An yanke wa Soja hukuncin...
Bayanai na cewa, wannan munduwa mai ɗimbin tarihi, mallakin Fir’auna Amenemope ne, yayin da ta yi ɓatan-dabo a gidan tarihin da ake adana da ita. An rarraba hoton munduwar zinarin ga jami’an da ke aiki a kan iyakokin ƙasar daban-daban da suka haɗa da filayen jiragen sama da tashohin jiragen ruwa da zummar daƙile fasaƙaurinta...
Babban sakataren kungiyar Hizbullah, Sheikh Naim Qassem, ya yi jawabi ga wadanda suka tsira daga kisan Pager a bikin cika shekara guda da aiwatar da wannan harin ta’addanci da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta yi a ranar 17 ga Satumba, 2024. “Ku ne masu gani na gaskiya, tushen begenmu, kuma sadaukarwar ku ga Allah ita ce...
Saboda wannan baiwa daga Allah, iyalai da ‘yan uwan mai akuyar suka sanar da shirye-shiryen gudanar da bikin murnar haihuwar ‘ya’yan akuyar a ranar Lahadi mai zuwa a Garun Dakasoye, karamar hukumar Garun Malam ta Jihar Kano, inda za a yi musu suna da kuma karatun Alkur’ani mai girma. A nasa bangaren, mahaifin budurwar,...
Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Ondo ta tabbatar da kama wata mata mai suna Iluyemi Bosede bisa zargin kashe yayarta, Tewogboye Omowumi, a Akure, babban birnin jihar. A cewar sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, Olayinka Ayanlade, ya fitar a ranar Talata, ya ce lamarin ya faru ne a ranar shida ga Satumba,...
A daidaikun kasuwannin Abuja da wasu manyan birane na ƙasar nan, an bayyana yadda farashin doya ke ƙara hawa fiye da yadda ake tsammani. Wannan na faruwa ne duk da cewa yanzu sabuwar doya ta fara shigowa kasuwa, bisa al’ada, a duk shekara fitowar sabuwar doya kan karya farashin wanda yake kasuwa. Sai dai...
Al’ummar garin Dukku a Ƙaramar Hukumar Dukku ta Jihar Gombe sun koka kan mummunan halin hanyar da ta haɗa su da babban birnin jihar, tare da kira ga gwamnati da ta gaggauta gyaran ta. A cewar direbobi, tafiyar Dukku zuwa Gombe wadda a da take ɗaukar mintuna 50 kacal, yanzu ta koma fiye da awa...
Ya ce kuma kayan da ake fitarwa zuwa waje waɗanda ba man fetur yanzu su kusa yin kai da kai da fetur. Ya ƙara da cewa ajiyar kuɗaɗen ƙasar a waje ya haura kusan dala biliyan 42, daga biliyan 32 lokacin da Tinubu ya hau mulki. Har ila yau, ya ce an biya bashin da...
Hukumar ƙididdigar a Najeriya NBS ta bayyana cewa an samu raguwar hauhawar farashin kaya a watan Agusta idan aka kwatanta da watan Yulin da ya gabace shi. Cikin sabbin alƙaluman da NBS ta fitar a ranar Litinin sun nuna cewa an samu raguwar kashi 1.76 a watan Agustan saɓanin watan Yulin, wanda ya nuna karo...
Mataimakinsa kan harkokin majalisa Honarabul Attahiru Danmadi ne ya wakilci dan majalisar ya kuma tabbatarwa wadanda lamarin ya shafa kokarinsa kan daukar matakan da suka kamata domin tabbatar da tsaron rayukan su da dawowa da zaman lafiya a yankunan. Garuruwan da ‘yan bindigar suka tarwatsa a gundumar Kuchi sun hada da Fakku, sha’alwashi, tulluwa...
Mujallar Qiushi Za Ta Wallafa Sharhin Xi Jinping Mai Taken “Zurfafa Dunkulewar Kasuwannin Kasa Ta Bai Daya”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp