2025-08-15@22:56:03 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1275

«kayakin Amurka»:

    Gwamnatin kasar China ta bayyana cewa ba zata taba amincewa a sake dorawa JMI takunkuman tattatalin arziki wadanda MDD ta dauke mata su a watan octoban da ya gabata ba. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar China Lin yana fadar haka ya kuma kara da cewa kasashen turai guda uku faransa Burtaniya da kuma Jamus wadanda ake kiransu E3 suna son ya yi amfani da wani tsarin da ake kiran SnapBack da ya zo cikin yarjeniyar JCPOA ta shekara 2015 don sake maida dukkan takunkuman tattalin arzikin da MDD ta dorawa JMI kafin yarjeniyar JCPOA dangane da shirinta na makamashin nukliya. Lin ya kara da cewa a ganinta ba za’a taba warware...
    Bayan da shugaban kasar Amurka Donal Trump ya karawa kayakin da suke shiga Amurka daga kasar Indiya kudaden fito har na kasha 50% Narendra Mudi ya ki sauraran kiraya-kiraye na kada yayi m haka. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto ya ce, kiraye-kirayen kasar Indiya ta hana wasu kayakin Amurka shiga kasar yana kara karfi a cikin mutane. Firai ministan ya bayyana cewa, a halin yanzu kamfai yayi nisa a cikin mutanen kasar na kauracewa kayakin Amurka wadanda suke shiga kasar kamar  McDonald’s, Coca-Cola, Amazon, da Apple da sauransu, sannan mutane su koma wajen bunkasa na gida. Labarin yace kamfanoni masu girma na Amurka suna samun kasuwa mai yawa a kasar india wacce take da jama’a fiye...
    Mutum 12 sun rasu yayin da wasu biyar suka jikkata a wani hatsarin mota da ya auku a ƙauyen Samawa, da ke Ƙaramar Hukumar Garun Malam a Jihar Kano. Hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:40 na daren ranar Juma’a a kan titin Zariya zuw Kano. Ambaliya: Magidanta da dama sun rasa muhallinsu a Yobe An sake ceto matafiya 10 da aka sace a Kogi Tirela ƙirar DAF mai lambar KMC 931 ZE, wadda ke ɗauke da kaya da fasinjoji ta yi hatsarin. Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC) reshen Kano, ta ce bincike ya nuna cewar matsala ce ta haddasa hatsarin. Tirelar na ɗauke da mutum 19, wanda 12 daga cikinsu suka rasu, sai wasu biyar da suka...
    An gano gawar wani jami’in sojin gwamnatin mamayar Isra’ila da ya kashe kansa bayan yaki a Gaza Rundunar sojin Isra’ila ta sanar da gano gawar wani jami’in sojin gwamnatin mamayar Isra’ila a wani dajin da ke arewacin Isra’ila. Sojan ya kashe kansa ne a lokacin da yake aikin soja, wanda ya kawo adadin sojojin da suka kashe kansu tun farkon wannan shekara zuwa 18, kamar yadda kafafen yada labaran haramtacciyar kasar Isra’ila suka bayyana. Gidan rediyon sojojin mamayar Isra’ila ya bayyana cewa: Rundunar sojin ta bude bincike kan lamarin, tare da bayyana cewa jami’in da ya kashe kansa yana shiyya ta 99 da ke yaki a zirin Gaza. Jaridar Yedioth Ahronoth ya watsa rahoton cewa: Jami’in dan shekaru 28 ya...
    Amana a cikin sanarwar da Hukumar ta NPA ta fitar mai taken daukar matakai ga masu amfani da Tashoshin Jiragen Ruwan kasar biyo bayan bullar annobar Korona wadda kuma Janar Manaja na sashen Kula da walwalar jama’a da dabarun samar da bayanai na Hukumar ta NPA Jatto Adams ya fitar ta umarci daukacin masu Kula da harkokin Hukumar da su dakatar da cazar duk wasu kudaden na shigo da kayan zuwa cikin Tashoshin Jiragen Ruwan kasar har zuwa wasu Kwanuka 14. Wannan umarnin ya biyo bayan umarnin da tsohuwar gwamatin marigayi Shugaban kasa Muhammad Buhari ta yi ne bayan bullar annobar Korona a na fadadar da aka yi ne, bayan bullar annobar Korona a ranar 12 ga watan Afirilun shekarar...
    A cikin jahohin da aka lissafa, Kebbi ce ta fi kowacce yawan garuruwa a jerin sunayen, inda take da garuruwa kusan 10 da suka hada da Kamba, Kangiwa, Kalgo, Ribah, Sakaba, Saminaka, Gwandu, Jega, da Birnin Kebbi. Gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwar gargadin samun ambaliyar ruwa ga jihohi 15 daga cikin 19 na Arewa. Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya, wacce ta yi wannan gargadin a madadin gwamnatin tarayya, ta bayyana cewa dole ne a dauki matakan da suka dace a cikin al’ummomin da abin ya shafa. Sanarwar da Ma’aikatar Muhalli ta fitar ta ce, biyo bayan hasashen da ta yi na samun ruwan sama mai karfi a jihohin, za a iya samun ambaliyar ruwa tsakanin 10 ga Agusta zuwa 14...
    Shugaban ƙasar Lithuania, Gitanas Nauseda, ya zabi ’yar majalisa Inga Ruginiene ta jam’iyyar Social Democrat, a matsayin firaminista, bayan Gintautas Paluckas ya yi murabus sakamakon binciken rashawa da ake gudanarwa a kansa. Sai dai Ruginiene ta taba fuskantar suka kasancewar tana da alaka da ’yan uwa a Rasha, wadanda ta ziyarta a shekarun 2015 da 2018. Mun shirya wa zaben ciki gurbi a Kano —INEC Tinubu ya cancanci yabo kan daidaita tattalin arzikin Nijeriya —Ngozi Sai dai ta ce yanzu daina kai musu ziyara, kuma ta jaddada cewa tun farko Ukraine take mara wa baya a yakin da take yi da Rasha, wadda ta kaiwa mamaya a 2022. Majalisar dokokin ƙasar za ta amince da nadinta tare da ministocinta kafin...
    Al’ummar garin Talasse da ke Ƙaramar Hukumar Balanga a Jihar Gombe, sun ce sun gaji da rayuwa cikin duhu har na tsawon shekaru 19. Sun kuma bayyana takaicinsu bayan tsayawar aikin wutar lantarki da ya tsaya. Ba a ba mu dala 100,000 da gwamnati ta mana alƙawari ba — Super Falcons NDLEA ta lalata gonar tabar wiwi a Gombe Aikin, wanda ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Billiri da Balanga, Ali Isa JC, ya fara tun farkon wannan shekara, ya sanya al’ummar yankin farin ciki bayan an kafa turakun wuta da na’urorin taransifoma. Sai dai cikin watanni biyu da suka gabata, aikin ya tsaya ba tare da wani bayani ba. “Yan siyasa su kan zo da alƙawura a lokacin zaɓe, sannan...
    Babban sakataren kungiya Hizbullahi ta kasar Lebanon ya karbi bakwancin Ali Larijani ya kuma godewa Iran bisa goyon bayan da take baiwa kasar Lebanon da ‘yan gwagwarmaya Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Qassem ya gana da Ali Larijani, sakataren majalisar koli ta tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran da tawagarsa a gaban jakadan Iran a Lebanon Mojtaba Amani. A yayin taron, Sheik Qassem ya jaddada godiyarsa ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran bisa ci gaba da goyon bayan da take baiwa kasar Lebanon da kuma ‘yan gwagwarmaya da yakin da suke yi da makiya yahudawan sahayoniyyar Isra’ila da kuma goyon bayan da take baiwa hadin kai da ‘yancin kai na Lebanon da kuma ci gaba...
    Lauyan Maïga, Cheick Oumar Konaré, ya bayyana cewa kamun bai dace ba saboda Maïga ba shi da niyyar guduwa ko lalata shaidu, yana kuma zargin cewa wannan wani mataki ne na siyasa saboda tsohon Firaministan ya daɗe yana sukar gwamnatin soja tun bayan tsawaita mulkinsu ba tare da gudanar da zaɓe ba. Maïga, ya hau kujerar Firaminista a watan Yulin 2021 bayan gwamnatin sojoji ta yi juyin mulki, inda ya goyi bayan dakatar da shirye-shiryen zaɓe don bai wa gwamnatin soja ƙarin lokaci. Sai dai daga baya ya fara sukar wasu matakan gwamnati, musamman bayan an dakatar da shi daga kujerarsa a watan Nuwamban 2024. Tun bayan juyin mulkin 2020 da na 2021, Mali ta kasance ƙarƙashin mulkin soja, kuma...
    Gwamnan ya yi alƙawarin cewa gwamnatin jihar za ta yi aiki tare da hukumomi masu ruwa da tsaki domin hanzarta shari’o’i da kuma rage cunkoson gidan yarin. A lokacin ziyarar, ya lura da cewa yawancin fursunonin na zaune a ƙasa babu katifa. Don inganta rayuwarsu, ya umarci a samar musu da katifu 500. Gwamna Sule ya yaba wa jami’an gidan yari da sauran jami’an tsaro saboda sake kama wasu daga cikin waɗanda suka tsere. Ya kuma roƙi jama’a da su kasance cikin shiri su kuma sanar da hukumomin tsaro idan sun ga wani mai kama da wanda ake nema. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
    Ministan harkokin wajen Yemen Jamal Amer a ranar Laraba ya karbi wata wasika daga Dr. Khalil al-Hayya shugaban kungiyar Hamas a Gaza, wanda wakilin kungiyar a Sanaa, Moaz Abu Shamala ya mika. A cikin wasiƙar nasa, al-Hayya ya bayyana matuƙar godiyar Hamas ga sadaukarwa da tsayin dakan al’ummar Yemen, yana mai bayyana su a matsayin “‘yan’uwa na gaskiya, Ansar Allah,” a tinkarar mamayar Isra’ila da kawayenta duk da gagarumar sadaukarwa, barazana, da hare-hare. Ya tabbatar da cewa nisan da kasar Yamen ke da shi da Falasdinu ya kara dankon kusancinta da al’ummar Palastinu ne kawai da kuma kudurinta na ci gaba da ba da taimako da taimako da kuma kare Gaza da Palastinu. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe...
    Jakadan kasar Irak a washintong ya bayyana cewa kasar Iraki entacciyar kasa she, tana da yencin kulla yarjeniyar tsaro da ko wace kasa da take so, wannan bayan korafin da gwamnatin Amurka tayi na yarjeniyar tsaro wacce kasar Iraki ta kulla da JMI. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jakadan yana cewa, kasar Iraki tana da yencin kulla yarjeniyar tsaro da kasashe makobta musamman kasar Iran wacce take da iyaka da mai tsawo da ita don samun amincin a kan iyakokin kasashen biyu. Ba ruwammu da abinda wani yake yake cewa. Tehran ta bagdaza dai suna da dangantakan tsaro mai karfi da juna, tun bayan samun nasara da Daesh, kuma suna haka kai don tabbatar da cewa...
    Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya ce, “Idan ba a zarge ni wajen binciken gwamnoni da ministocin jam’iyyar da ke mulki ba, bai kamata a zarge ni idan na binciki ’yan hamayya ba.” Duk da haka, mutane da dama a kafafen sada zumunta sun nuna shakku, tare da tambayar dalilin da ya sa EFCC ba ta ɗauki mataki kan manyan ’yan siyasa na jam’iyyar APC kamar tsohon Gwamnan Delta Ifeanyi Okowa, tsohon Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, da tsohon Gwamnan Kogi Yahaya Bello ba. Wasu sun zargi EFCC da yin aiki ƙarƙashin ikon gwamnatin da ke mulki, yayin da wasu suka yi tsokaci ta hanyar buƙtar shugaban EFCC ya bayyana bayanan asusun bankinsa na yanzu. Daga kanmu, magana ta ƙare....
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Da aka tambaye shi dalilin da ya sa ya fito ƙarara ya goyi bayan shugaban ƙasa wanda ba a cikin jam’iyyarsu yake, Soludo ya ce goyon bayansa ga Tinubu ba sabon abu ba ne.   “An samar da waɗannan huluna tun lokacin da Shugaban Ƙasa ya ziyarci Jihar Anambra kuma kun ga allunan talla da sauran abubuwa da ke bayyana cewa masu ra’ayin kowa ci gaba suna aiki tare ne da juna,” in ji Soludo.   “Bayan haka, wannan wata babbar manufa ce da na yi imani da ita sosai, cewa ya kamata dukkan jam’iyyun siyasa da ke ikirarin ra’ayin ci gaba su haɗu a ƙarƙashin wata babbar ƙawance don zurfafa tunani da kawo ci gaba ba kawai a tafarkin...
    Ministan harkokin wajen kasar Armenia Ararat Mirzoyan ya tabbatarwa JMI kan cewa yarjeniyar sulhu da suka cimma da kasar Azairbaijan ba zai shafi bukatun kasar Iran ko kuma hanata wani hakkinta a yankin kaukas ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan harkokin wajen kasar Armenia yana fadar haka a safiyar yau Talata, ta wayar tarho a lokacinda yake zantawa da tokwaransa na kasar Iran Abbas Aragchi. A cikin wannan makon ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya jagoranci yarjeniyar zaman lafiya tsakanin kasashen Azarbaijan dangane da yankin karabakh a fadar White House. Sannan akwai labarin cewa za’a gina wani babban titi wanda zai ratsa kasashen bitu. Kasashen dai suna makobtaka da kasar Iran, don haka dangantakarsu...
    Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bai wa Gwamnatin Tarayya ranakun 24, 25 da 26 ga watan Satumba domin ta kammala shari’ar da ta shafe shekaru goma tana yi wa tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Kanal Sambo Dasuki mai ritaya, kan zargin mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba da kuma halasta kuɗin haram. Mai shari’a Peter Lifu ya bayar da wannan umarnin a ranar Talata, bayan amincewa da buƙatar gwamnati ta ɗage zaman domin kawo ƙarin shaidu da kuma ba wa Dasuki damar fara kare kansa. Nijeriya ta sake ƙulla alaƙar tsaro da Isra’ila Tinubu na amfani da EFCC ya muzguna wa ’yan adawa — Atiku Ya kuma umurci gwamnati ta kira sauran shaidunta domin...
    Hukumar Kwastam Najeriya ta kama kwantainoni 16 ɗauke da makamai da miyagun ƙwayoyi da magungunan da wa’adin aikinsu ya ƙare da wasu haramtattun kaya na kimanin Naira 10 a Tashar Jiragen Ruwa ta Apapa da ke Jihar Legas a ranar Litinin. Hukumar ta bayyana cewa ta kama mutane shida dangane da wannan haramtattun kaya da aka yi fasa-ƙwaurin su zuwa Najeriya. Kwanturola Janar na Kwastam, Adewale Adeniyi, ya sanar da cewa an yi ƙarya wajen bayyana kayan da  kwantainonin suke ɗauke da su, inda aka ɓoye makamai, harsasai da magungunan da ba su da rajista. “A yau, muna sanar da kama kwantainoni 16 da shigowarsu ke karya dokokinmu kuma suna barazana ga tsaron ƙasa. Darajar harajin da za a biya...
      Lokacin da bukatun Afirka suka hadu da karfin Sin, muna da dalilin yin imani cewa, tare da tallafin dandalolin kamar su “dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC)” da shawarar “ziri daya da hanya daya”, hadin gwiwar AI tsakanin Sin da Afirka tabbas za ta samar da samako mai armashi nan gaba. (Mai zane da rubutu: MINA) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Babban sakataren Majalisar Kolin Tsaron kasar Iran Ya bayyana cewa: Kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah ba ta bukatar juya akalarta Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya bayyana cewa: Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah tana da cikakken ilimin siyasar da zata gudanar da al’amuranta bisa dacewa, kuma gwagwarmaya ba ta bukatar horo. Larijani ya kara da cewa a wani taron manema labarai a birnin Bagadaza na kasar Iraki; “Dukkansu sun damu da tsaron yankin baki daya, kuma al’ummar Iraki ba sa bukatar wani takunkumi.” Larijani ya jaddada cewa: Rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro da kasar Iraki na da nufin hana duk wata barazana ga tsaron kasashen biyu. A yayin da yake mayar da martani ga wasu nazari...
    Babban sakataren Majalisar Kolin Tsaron kasar Iran Ya bayyana cewa: Kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah ba ta bukatar juya akalarta Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya bayyana cewa: Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah tana da cikakken ilimin siyasar da zata gudanar da al’amuranta bisa dacewa, kuma gwagwarmaya ba ta bukatar horo. Larijani ya kara da cewa a wani taron manema labarai a birnin Bagadaza na kasar Iraki; “Dukkansu sun damu da tsaron yankin baki daya, kuma al’ummar Iraki ba sa bukatar wani takunkumi.” Larijani ya jaddada cewa: Rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro da kasar Iraki na da nufin hana duk wata barazana ga tsaron kasashen biyu. A yayin da yake mayar da martani ga wasu nazari...
    Rijistaran makarantar, Alhaji Kasimu Salihu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa an rufe makaranta kuma an umarci ɗalibai su bar harabar makarantar har sai an bayar da sanarwa ta gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Dakarun Operation FANSAN Yamma (OPFY) sun yi nasarar fatattakar ‘yan ta’adda da dama a wani hari da suka kai ta sama da kasa a yankin Makakkari da ke dajin Gando a karamar hukumar Bukkuyum a jihar Zamfara.   Wannan farmakin wanda ya gudana a ranar 10 ga watan Agustan shekarar 2025, ya biyo bayan wasu bayanan sirri da suka samu cewa dimbin ‘yan ta’addan da ke biyayya ga marigayi Halilu Buzu da Alhaji Beti sun taru a cikin dajin inda suka shirya kai harin ramuwar gayya kan al’ummomin Addabka da Nasarawan Burkullu a garin Bukkuyum.   Jami’in yada labarai na rundunar ‘Operation Fansan Yamma OPFY’ Kyaftin David Adewusi, ya ce bayanan sirri sun nuna cewa, harin da suka shirya kai...
    Hukumar Kwastam Najeriya ta kama kwantainoni 16 ɗauke da makamai da miyagun ƙwayoyi da magungunan da wa’adin aikinsu ya ƙare da wasu haramtattun kaya na kimanin Naira 10 a Tashar Jiragen Ruwa ta Apapa da ke Jihar Legas a ranar Litinin. Hukumar ta bayyana cewa ta kama mutane shida dangane da wannan haramtattun kaya da aka yi fasa-ƙwaurin su zuwa Najeriya. Kwanturola Janar na Kwastam, Adewale Adeniyi, ya sanar da cewa an yi ƙarya wajen bayyana kayan da  kwantainonin suke ɗauke da su, inda aka ɓoye makamai, harsasai da magungunan da ba su da rajista. “A yau, muna sanar da kama kwantainoni 16 da shigowarsu ke karya dokokinmu kuma suna barazana ga tsaron ƙasa. Darajar harajin da za a biya...
    Sojoji sun samu nasarar kai wani gagarumin farmaki kan maboyar ’yan ta’addan da suka addabi manoma da mazauna wasu ƙauyuka a Jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Nijeriya. Bayanai sun ce dakarun sojin na sama da ta ƙasa, waɗanda ke ƙarƙashin rundunar Operation Fasan Yamma da ke sintiri a Arewa maso Yamma domin kawar da masu tayar da ƙayar baya, sun hallaka sama da ’yan ta’adda 400 a yayin wannan samamen. Za a gyara tarbiyar tubabbun ’yan daban Kano Direba ɗaya ya tsira a hatsarin tankokin dakon iskar gas a Zariya Majiyoyi sun bayyana cewa ’yan ta’addan, waɗanda ke fakewa a dajin Makakkari tare da shugabanninsu daban-daban, sun dauki haramar kai hari kan wani ƙauye ne kafin sojojin su...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya bayyana cewa, gwamnatin da ta gabata ce ta rufe cibiyoyin da aka kafa a gwamnatin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, amma gwamnatinsa ta yanke shawarar farfado da su domin magance matsalar rashin aikin yi. “Don haka ne a yau, kowane Dalibi wanda ya kammala karatun, ba kawai takardar shaida za a bashi ba har ma da kayan aikin sana’ar da ya koya” in ji Yusuf. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jami’an Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), sun kai samame a Ɗakin Karatun Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta, a Jihar Ogun, inda suka kama wasu matasa da ake zargin ’yan damfara ne. Samamen ya faru ne da safiyar ranar Lahadi a sashen otal na ɗakin karatun. ’Yan bindiga sun kashe gomman mutane a ƙauyukan Sakkwato An ɗaure tsohon Firaminista Succes Masra shekaru 20 a Chadi Gidan Obasanjo na musamman yana cikin harabar ɗakin karatun. Wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, ya nuna yadda wasu matasa ke gudu domin ka da EFCC ta kama su. Rahotanni sun ce jami’an EFCC sun ƙwace sama da motoci 20 tare da wasu kayayyaki masu daraja. Wani jami’in...
    A ranar Asabar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta sanar da cewa dan wasan bayanta, Inigo Martinez zai bar kungiyar, kuma jaridun Sifaniya sun ruwaito cewa zai koma kungiyar Al-Nassr da ke gasar Saudi Pro League. Tafiyar Martinez za ta taimaka wajen rage nauyin biyan albashin ’yan wasa a Barcelona, kungiyar da a bayan nan ke fama matsalar rashin kudi. MDD za ta yi zaman gaggawa kan yunƙurin ƙwace Gaza Dubban mutane sun yi zanga-zangar goyon bayan Falasɗinu a Isra’ila da Pakistan Martinez mai shekara 34 ya buga wasa a wasanni 71 a dukkan gasanni tun bayan komawarsa kungiyar daga Athletic Bilbao a shekarar 2023, inda ya taimaka wa Barcelona ta lashe kofin La Liga a kakar bara. Kafin haka,...
    Dubban mutane ne suka fito kan tituna a birnin Tel Aviv na Isra’ila ranar Asabar, domin yin kira da a kawo ƙarshen yaƙin Gaza, kwana guda bayan da gwamnatin Isra’ila ta lashi takobin faɗaɗa rikicin tare da ƙwace birnin Gaza. Masu zanga-zangar da ke riƙe da hotunan waɗanda har yanzu ake garkuwa da su a yankin Falasdinawa sun yi kira ga gwamnati da ta tabbatar da sakin su ’yan uwansu. Al-Hilal ta ɗauki Nunez daga Liverpool ASUU na shirin sake tsunduma yajin aiki ’Yan jaridar AFP a wajen gangamin sun ƙiyasta adadin waɗanda suka halarci taron a matsayin dubbai, yayin da wata ƙungiya da ke wakiltar iyalan wadanda aka yi garkuwa da su ta ce mutane kusan 100,000 ne suka...
    Ali Akbar Velayati mashawarcin jagoran juyin juya halin Musulunci da Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan harkokin kasa da kasa ya tabbatar da cewa “Jamhuriyar Musulunci tana adawa da shirin kwance damara na kungiyar Hizbullah” yana mai jaddada cewa Iran a ko da yaushe tana goyon bayan al’ummar kasar Labanon da kuma gwagwarmayarsu. Da yake magana da kamfanin dillancin labarai na Tasnim na Iran a ranar Asabar, Velayati ya ce bijiro da batun kwance damarar Hizbullah ba sabon abu ba ne a Lebanon. “Kamar yadda wannan yunƙurin ya gaza a baya, wannan karon ma ba za iyi nasara ba, kuma ‘yan gwagwarmaya zasu ci gaba da yin tsayin daka a kan manufofinsu da kuma dakile wannan makirci,” in ji shi. Ya...
    ‘Yan sandan Birtaniya a birnin Landan sun sanar da kame mutane 365 a wata zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinu, wadda kungiyar Palestine Action da gwamnatin Birtaniya ta haramta a watan jiya ta shirya. A cikin jerin rubuce-rubucen da aka yi a Shafin  X, ‘yan sanda sun ce “sun dauki tsauraran matakai a kan wannan laari,  tare da yin barazanar kame duk wanda ya nuna goyon baya ga Action Palestine. Masu zanga-zangar dai na dauke da alamomin da aka rubuta “Ku kawo karshen kisan kare dangi, ku goyi bayan matakin Falasdinu,” tare da rera taken “Ku kun ji kunya”. Kungiyar kare hakkibil adama ta  “Lift the Ban”, ta bayar da rahoton cewa ‘yan sandan Biritaniya sun gaba da kame mutane kan...
    Yansanda a kasar Burtaniya ta kama mutane fiye da 200 wadanda suka fito zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a birnin London. Tashar talabijinn ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kafafen yada labarai a birnin London na cewa mutane kimani 600-700 ne suka fito suka kuma tsaya a wani wuri kusa da majalisar dokokin kasar wanda ake kira ‘ in Westminster’s Parliament Square ‘ inda suke dauke da kwalaye da rubuton ina son mutuncin ma’aikatar sharia, bana son zalunci. Kafin haka dai gwamnatinn kasar ta haramta zanga-zangar da aka saba gudanarwa a birnin na Lodun a dukkan karshen mako, wato ranar asabar na goyon bayan Falasdinawa da kuma yin allawadai da kasashen yamma musamman gwamnatin kasar Burtaniya wacce daga daga cikin...
    Yawancin ‘yan Nijeriya sun nuna damuwa game da yadda majalisar dattawa ta 10 ke gudanar da harkokin majalisa, suna cewa ‘yan majalisar sun gaza bayar da muhimman ayyukan da aka ɗora musu na binciken ɓangaren zartarwa don kare ‘yan Nijeriya. Ana zargin majalisa dattawa ta 10 da ƙin tilasta wa gwamnatin tarayya wurin magance tarin ƙalubale da ke fuskantar ‘yan Nijeriya, ciki har da tsadar rayuwa, talauci, yunwa, yawan rashin aikin yi da rashin tsaro, da sauran su. Rahotanni su bayyana cewa akwai tsofaffin gwamnonin 13 da ke majalisar dattawa ta 10 a halin yanzu, wanda suka haɗa da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio (Akwa Ibom), Aliyu Wammako (Sakkwato), Abdulaziz Yari (Zamfara), Aminu Waziri Tambuwal (Sakkwato) da Adams Oshiomhole (Edo)....
    Bayan da aka ɗaura auren, masoyanta da abokan aikinta suka tura mata saƙonni taya murna daga sassa daban-daban na Nijeriya. Wannan aure ya zo watanni kaɗan bayan rasuwar mahaifinta, wanda ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau, ta yi aure da masoyinta, Ibrahim Garba. An ɗaura auren a ranar Asabar a Masallacin da ke Unguwan Rimi, a Jihar Kaduna, bayan Ibrahim ya biya sadaki Naira 300,000. Za a biya ma’aikata 445 garatutin sama da biliyan ɗaya a Kebbi Kotu ta ɗaure wata mata shekara 3 a kan damfara  Rahama, ta sanar da ɗaurin auren a shafinta na Facebook, inda ta gode wa Allah tare da neman addu’a daga masoyanta. Ta bayyana farin ciki da godiyarta, tare da fatan wannan sabon babi na rayuwarta zai kasance mai albarka. Auren mata na zuwa ne watanni biyu bayan rasuwar mahaifinta, Ibrahim Sadau. ’Yan uwanta sun yaɗa hotuna da bidiyon bikin a kafafen sada zumunta, inda...
    Al’ummar Japan na gudanar da bikin tunawa da ranar harin Nagasaki da ya faru shekaru 80 da suka gabata, wani hari da ke zama irinsa na farko kuma mafi muni da duniya ta taba gani. Tarihi ya nuna cewa Amurka ce ta fara harba makamin Nukiliya a garin na Nagasaki kwanaki uku bayan na garin Hisroshima a wani ɓangare na dakatar da yaƙin duniya na biyu.! Harin na ranar 9 ga watan!!!!!!!mutane dubu 70 a take bayan mutane 140 da suka mutu kwanaki uku da suka gabata a harin na Hiroshima. An yi ittifakin cewa wannan shine harin da ya tilastawa Japan miƙa wuya a ranar 15 ga watan Agustan wannan shekarar, matakin da ya kawo ƙarshen yaƙin. Bayanai sun...
    Wata babbar kotu a Jihar Borno, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Aisha Kumaliya, ta yanke wa Kalthum Mustapha hukuncin ɗaurin shekara uku a gidan gyaran hali bayan samun ta da laifin aikata damfara. Hukumar EFCC ta bayyana cewa, an fara gurfanar da Kalthum a ranar 13 ga watan Mayu, 2024. Tsohon Ministan Noma Audu Ogbeh ya rasu Fashewar gurneti ya kashe yara uku a Borno  Ana tuhumarta da karɓar kuɗi Naira miliyan 1.35 daga hannun Muhammad Lawan Sani, Abubakar Umar, da Yusuf Jafar domin samar musu da kayan abinci da ake amfani da su wajen ciyar da yara masu fama da rashin abinci mai gina jiki. Sai dai ba ta kawo kayan ba kuma ba ta mayar musu da kuɗinsu ba. A...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Mai ba da Shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci da tsohon fira ministan Iraki sun jadadda goyon bayansu ga kugiyoyin gwagwarmaya Mai ba da shawara kan harkokin kasa da kasa ga Jagoran juyin juya halin Musulunci ya tattauna kan ci gaban yankin Gabas ta Tsakiya a wata tattaunawa ta wayar tarho da tsohon fira ministan kasar Iraki Nuri al-Maliki, kuma dukkansu sun jaddada goyon bayansu ga kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa. A tattaunawar ta wayar tarho, Ali Akbar Welayati, mai ba da shawara ga Jagora kan harkokin kasa da kasa, ya yi tambaya game da lafiyar tsohon Fira ministan Iraki Nouri al-Maliki. A cikin kiran, Velayati ya yi fatan samun koshin lafiya ga al-Maliki da samun sauki cikin gaggawa, inda ya...
    Cin zarafin Amurka ta hanyar haraji ya kuma lalata amincinta tsakanin sassan kasa da kasa. A halin yanzu, fannin shigar da kayayyaki na Amurka ya yi kasa zuwa kashi 13% kacal a kasuwannin duniya.   Har ila yau, a jiya Alhamis 7 ga wata, bayanai sun nuna cewa, a cikin watanni bakwai na farkon shekarar nan, cinikayyar kayayyaki ta Sin ta ci gaba da nuna kyakkyawan ci gaba, inda ta samu karuwa tsakaninta da kasashe membobin kungiyar ASEAN, da Tarayyar Turai, da Afirka, da Asiya ta Tsakiya, wanda ke nuna karfin juriya da kuzari. Hakan ya kuma tabbatar da cewa, cin zarafi ta hanyar haraji ba zai haifar da alfanu na dogon lokaci ba, maimakon haka, budadden tsarin hadin gwiwa...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci a yi dukkan kokarin bincike da ceto da tunkarar ambaliya da ayyukan agaji, bayan aukuwar ambaliya a yankin tsaunika tun daga jiya Alhamis, a lardin Gansu na arewa maso yammcin kasar Sin. Zuwa karfe 3 na rana a yau Juma’a, ibtila’in ya yi sanadin mutuwar mutane 10 da batan wasu 33. Shugaba Xi Jinping na bada muhimmanci sosai ga yanayin ibtila’i da mamakon ruwan sama ya haifar a wasu yankuna ciki har da gundumar Yuzhong na Lanzhou, babban birnin lardin Gansu. Cikin umarnin da ya bayar, Xi Jinping ya ce aiki na gaggawa shi ne yin dukkan mai yuwuwa wajen bincike da ceton mutanen da suka bata da ganowa da sake tsugunar da...
    Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF), ta kai hare-hare ta sama a yankin Rann, wani gari da ke Jihar Borno, wanda ake zargin ya zama mafakar ’yan ta’adda. Wannan aiki na cikin shirin Operation Haɗin Kai, kuma ya yi sanadin hallaka ’yan ta’adda da dama. ’Yan damfara 2 sun shiga hannun ’yan sanda a Yobe PDP ta gargaɗi ’ya’yanta kan goyon bayan Tinubu a zaɓen 2027 Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa ’yan ta’addan sun fara guduws bayan yunƙurinsu na kai hari sansanin sojoji ya ci tura. Da suka hangi jiragen yaƙi na sojojin sama, sai suka fara tserewa daga maɓoyarsu, amma an kashe da yawa daga cikinsu ta hanyar ɓarin wuta. Wani mazaunin Rann ya ce da farko sun...
    Jam’iyyar PDP ta ce za ta ɗauki mataki kan wasu mambobinta da ke aikata abubuwan da ke kawo wa jam’iyyar koma baya. Shugabancin jam’iyyar ya fi damuwa da mambobin da ke bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu don sake tsayawa takara a zaɓen 2027. Isra’ila za ta mamaye ilahirin Zirin Gaza ya koma karkashinta – Netanyahu Tinubu zai kashe tiriliyan 1.5 wajen gina layin dogo na zamani a birnin Kano Mai magana da yawun jam’iyyar PDP, Debo Ologunagba, ya ce wasu fitattun mambobin jam’iyyar na yin magana a kafafen watsa labarai tare da ƙalubalantar jam’iyyar. A cewarsa wasu ma suna bayyana shirinsu na taimaka wa jam’iyyar APC ta samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa. Ya ce...
    Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Wakilai, Abubakar Kabir Abubakar, ya ce Gwamnatin Tarayya za ta kashe Naira tiriliyan daya da rabi don gina layin dogo na zamani domin saukaka harkar sufuri a cikin birnin Kano. Ya bayyana hakan ne lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a Kano, inda ya ce aikin zai saukaka wa mazauna birnin wahalar da suke sha a harkar sufuri. Zamfarawa sun yi zanga-zanga kan hare-haren ’yan bindiga Abba ya yi alhinin hadiminsa da ’yan daba suka kashe a Kano Ya ce, “Wannan aikin na gina layin dogo na zamani ya kai Dalar Amurka biliyan daya, kwatankwacin Naira tiriliyan daya da rabi. “Ga wadanda suke tafiye-tafiye zuwa kasashen waje, musamman kasashen Turai da nahiyar Asiya,...
    Fitaccen matashin nan mai barkwanci, Bello Habib Galadanci, wanda aka fi sani da Ɗan Bello, ya yi rashin mahaifinsa a yammacin wannan Alhamis din. Matashin lauyan nan ɗan gwagwarmaya, Abba Hikima, ne ya bayyana hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook. Abba ya yi alhinin hadiminsa da ’yan daba suka kashe a Kano NAHCON ta ƙayyade N8.5m kafin alƙalami na kujerar Hajjin 2026 “Innalillahi wa inna IlaiHi rajiun. Allah Ya yi wa Mahaifin Dokta Bello Galadanchi (Dan Bello) rasuwa yanzun nan. Allah Ya gafarta masa. Ameen,” a cewar saƙon da Abba Hikima ya wallafa. Kawo yanzu dai ba a bayyana dalilin rasuwar mahaifin Ɗan Bellon ba, amma wasu kafofin watsa labarai sun ruwaito cewa marigayi ya...
    Wasu daga cikin tsoffin kansilolin da suka halarci tattakin sun bayyana goyon bayansu ga gwamna Abba Kabir Yusuf.   A nasa jawabin, Dahiru Yusuf daga Gezawa kuma tsohon kansila ya ce, shi ma yana cikin wadanda tsohuwar gwamnatin Ganduje ta hana hakkinsu, don haka maganar Abdullahi Abbas ba gaskiya bane! “Sun ga gwamna Abba zai jikanmu ne shi ne suke neman bata mana ruwa”.   Tun da farko, shugaban tawagar, ya tabbatar da cewa, mai girma Gwamna ya amince zai biya su hakkokinsu wanda gwamnatin baya ta kasa biyansu, kuma yace baya bukatar sakamakon komai daga gare su wai don su koma jam’iyyarsa, ya yi ne domin Allah.   A karshe dubban tsoffin kansillolin wanda suka yi tattaki dauke da...
    Alummar duniya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan furucin firaministan Israila na fadada mamaya a Gaza. Sakamakon wani nazarin jin raayin jamaa da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar ya nuna cewa, kaso 86.6 na wadanda suka bayar da amsa sun bayyana adawa mai karfi da matakin firaministan, suna masu kira da Israila ta dakatar da bude wuta da kawo karshen rikici da Gaza nan take. Sakamakon ya kuma nuna cewa, kaso 80.8 na wadanda suka amsa na ganin cewa mafita ga rikicin Palasdinu ya dogara ne da kafuwar kasashe biyu, inda suka yi kira da a dawo da halaltattun hakkokin kasar Palasdinu. Kafar CGTN ta wallafa nazarin ne a dandalinta na harsunan Ingilishi da Spaniyanci da...
    Mazauna kauyen Chatta da ke karamar hukumar Hawul a jihar Borno sun fada alhini sakamakon rasuwar wasu mutum hudu ’yan gida daya. Ba a dai tabbatar da ainihin musabbabin rasuwarsu ba, amma mazauna yankin da lamarin ya faru sun ce suna zargin hayakin injin samar da lantarki na janareta ne ya yi ajalin su. An kama bama-baman da aka boye a cikin kayan gwangwan a Kaduna Ana zargin ‘yan sanda da karya hannun Sowore Majiyoyin da ke kauyen na sun shaida wa rundunar ’yan sandan jihar cewa wadanda suka mutun sun hada da Yakubu Samanja, matarsa Esther Yakubu, da ’ya’yansu biyu, Amos Yakubu da Maryamu Yakubu. Wani dan uwan mamatan mai suna Ibrahim Samanja, ya ce ya gano faruwar hakan...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta kama wasu bama-bamai da ba su fashe ba da wasu tarin makamai da aka shigar da su jihar cikin kayan gwangwan daga jihar Borno. Lamarin dai ya jefa fargaba a zukatan mutane kan yadda kayayyaki ke yawo babu bincike daga jihohin da ke fama da rikici. Yadda kwacen babur da waya ya maye gurbin garkuwa da mutane a Birnin Gwari Bai kamata ake bai wa ɓarayi muƙamin ministoci ba — Sarki Sanusi II Kakakin rundunar a jihar, DSP Mansir Hassan ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce an kama kayan ne ranar Asabar bayan wasu bayanan sirri da rundunar ta samu. Ya ce an samu kayan ne a cikin wani kamfanin da ke...
    Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar da kyautar fuloti da kuɗi naira miliyan biyar ga kowane ɗaya daga cikin iyalan tawagar ’yan wasan nan na Kano 22 da suka rasu a wani mummunan haɗarin mota da ya auku a watan Yuni. Mai bai wa gwamnan shawara kan yaɗa labarai, Ibrahim Adam, ne ya tabbatar da wannan kyauta cikin wani saƙo da ya wallafa a Facebook a wannan Larabar. Ministocin Ghana biyu sun rasu a hatsarin jirgin sama Gwamnan Kano ya gargaɗi muƙarrabansa bayan murabus ɗin Kwamishina “Mai girma Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bai wa iyalan ’yan wasan da suka rasu fuloti ɗaya da kuma naira miliyan biyar kowannensu,” in ji sanarwar. Aminiya ta ruwaito cewa, tawagar ’yan wasan...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya taya Larijani murnar nadin da aka yi masa a matsayin sakataren majalisar koli ta tsaron kasa Abbas Araqchi, ministan harkokin wajen kasar Iran, ya taya Ali Larijani murnar nadin da aka yi masa a matsayin sakataren majalisar koli ta tsaron kasar. A cikin sakon taya murna, Araqchi ya taya Larijani murnar nadin da aka yi masa a matsayin sabon sakataren majalisar koli ta tsaron kasar, tare da yi masa fatan samun nasara a sabon mukamin nasa. A cikin sakon taya murnarsa, Araqchi ya bayyana cewa, shi da takwarorinsa na ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran a shirye suke su ba da hadin kai sosai ga Larijani wajen gudanar da muhimman ayyukansa, musamman a fannonin diflomasiyya...
        Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban ya kuma yabawa cibiyoyin koyon ilimi tare da bayyana cewa wadannan nasarorin da aka samu shaida ne na ingancin ilimin Nijeriya wanda ke kekkenshe yara masu basira a duniya.   Tinubu ya yi imanin cewa, ilimi muhimmin abu ne ga ci gaban kasa; don haka, babbar hobbasar da gwamnatinsa ta yi a fannin, shi ne kawar da matsalolin kudi ga ‘yan Nijeriya marasa galihu da ke neman manyan makarantu ta hanyar ba su ba shi a ashirin Asusun ba da lamuni na ilimi na Nijeriya (NELFUND). Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki...
    Gwamnatin kasar Sin ta samar da kudi har yuan biliyan 1.015, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 142 ga lardunan kasar daban daban, domin gudanar da ayyukan jin kai, sakamakon ibtila’in ambaliyar ruwa da ta shafi wasu sassan kasar. Rahotanni na cewa ma’aikatar kudin kasar, da ma’aikatar gona da raya karkara, da ma’aikatar albarkatun ruwa ne suka samar da kudaden, wadanda za a yi amfani da su a ayyuka daban daban na tallafawa yankunan da ambaliyar ta shafa, ciki har da birnin Beijing, da lardin Hebei, da Mongolia ta gida da Guangdong. Kana cikin kudin za a samar da tallafin sake shukar da ruwa ya lalata, da ma kayayyakin aikin gona da ambaliyar ta shafa. Kazalika, za a yi amfani da bangaren...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gargaɗi maƙarrabansa cewa duk wanda ba zai iya sauke nauyin da aka ɗora masa, ya yi murabus. Wannan gargaɗi na zuwa ne bayan murabus ɗin Kwamishinan Sufuri, Alhaji Ibrahim Namadi, ya yi biyo bayan belin wani da ake zargin dilan miyagun ƙwayoyi, Sulaiman Danwawu. Manoma sun koka kan rabon takin gwamnati a Sakkwato Hatsarin Mota: Yadda hanyar Lambata ke laƙume rayuka a Neja Wannan lamari ya tayar da ƙura, wanda hakan ya sa Gwamna Abba, ya ɗauki mataki. A cewar sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, gwamnan ya bayyana rashin jin daɗinsa kan lamarin. Hakan ta sa ya jaddada buƙatar dukkanin mambobin majalisar da sauran manyan...
    Shugaban Kasa Bola Tinubu, ya taya daliban nan ’yan mata ‘yan asalin jihar Yobe su uku da suka lashe gasar harshen Turanci da aka yi a birnin Landan na Burtaniya. A farkon makon nan ne dai Nafisa Abdullahi Aminu da Rukayya Muhammad Fema da kuma Hadiza Kashim Kalli suka zama zakaru a gasar TeenEagle ta 2025 da aka yi a birnin na Landan. Ambaliya ta lalata kauyuka 3 a Sakkwato Yadda ’yan bindiga suka sace Zamfarawa 150 a cikin kwana 4 A cikin wata sanarwa daga bakin kakakinsa, Bayo Onanuga, ranar Laraba, Shugaba Tinubu ya ce nasarar ’yan matan abin alfahari ce ga Najeriya. Tinubu ya kuma yaba wa makarantun da daliban suke karatu, inda ya ce nasarar daliban wata...
    Kakakin dakarun juyin juya halin musulun a nan Iran ya bayyana cewa nasarar da JMI ta samu na tunkude hare-harenda HKI ta kawowa kasar ya saya abubuwa da dama a bangaren siyasa da wasu al-amura a yankin da kuma duniya gaba daya. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto General Ali Mohammad Naeini yana fadar haka a wani wani taro na tunawa da daya daga cikin shahidan yakin kwanaki 12 wanda HKI da Amurka suka kallafawa kasar. Ya kara da cewa duniya ta sauya sabada nasarar sannan musamman a fagen diblomasiyya da kuma kafofin yada labarai a duniya, wanda ya bar tasiri mai kyau ga kasar. Labarin ya kara da cewa, akalla kasha 60 % na mutanen duniya...
    ‘Yansanda a kasar Iran sun bada labarin cewa suna amfani da jiragen leken asiri da wasu kayakin masu aiki da lantarki na zamani don tabbatar da lafiyar masu tattalin 40 zuwa wurare masu tsarki a kasar Iraki. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Brigadier General Ahmad Ali Goodarzi  shugaban yansanda a nan kasar Iran ya bayyana cewa, yansandan kasar suna aiki tare da rana wajen kyautata ayyukan tsaro a dukkan kofofi shiga Iraki daga Iran guda 6 saboda tabbatar da tsaron masu zuwa 40 na Imam Hussain (a). Ya ce:  Yansa a kan iyakokin kasar suna sanya kula da musamman a kofofin shiga kasar Iraki, wadanda suke da cinkoson mutane. Tare da amfani da jiragen marasa matuka...
    Mataimakin shugaban kasar Iran Muhamad Reza Aref ya bayyana cewa kasar Iran tana goyon bayan dukkan shirin zaman lafiya a yankin musamman tsakanin kasashen Armenia da kuma Azarzaijan. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Aref yana fadar haka a lokacin ganawarsa da shugaban kasar Armenia Vahagn Khashaturyan a kasar Tukeministan ake ake gudanar da taron kasashen wadanda basa kan bakin ruwa a duniya a ranar Litinin. Majalisar dinkin duniya ce ta take shrya wannan taron don ci gaban irin wadannan kasashe a duniya karo na 3TH. Aref yace yana fatan zaman zafiya ta dore a cikin kasashen yankin don amfanin kowa. Daga karshe mataimakin shugaban kasan Iran ya bayyana cewa Iran tana goyon bayan kasar Armenia ta...
    Ta sake kafa tarihi bayan da jaridar National Concord mallakar MKO Abiola ta naɗa ta a matsayin editan jaridar ta farko, inda A shekarar 1986, aka ɗaga darajarta zuwa matsayin Manajan Darakta kuma Babban Edita mace ta farko da ta riƙe wannan matsayi a tarihin jaridun Nijeriya. Ta auri MKO Abiola a shekarar 1981, kuma ta tsaya tsayin daka tare da shi wajen gwagwarmayar siyasarsa da rikicin da ya biyo bayan zaɓen 12 ga watan Yuni, inda ta bayar da gagarumar gudunmawa a fagen jarida, tare da shafe kusan shekaru 30 tana jan ragamar kafafen yaɗa labarai a Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
    Kotun tsarin mulkin Kamaru ta haramta wa jagoran adawar ƙasar, Maurice Kamto tsayawa takarar shugaban ƙasa, a babban zaɓe mai zuwa na watan Oktoba, kan abin da ta bayyana rashin cika ka’idojin tsayawa takara. Lauyansa, Hippolyte Meli Tiakouang ne ya tabbatar wa manema labarai hukuncin kotun wanda ba za a iya ƙalubalanta ba, bayan kammala zamanta na wannan Talata. A cewarsa, kotun ta yi watsi da ƙarar da suka shigar kan matakin hukumar zaɓen ƙasar na cire shi daga cikin jerin ’yan takarar da za su fafata a zaɓen ranar 12 ga watan Oktoban bana. Mulkin Tinubu ya fi na Buhari muni — Maina Waziri ’Yan gida ɗaya sun kitsa garkuwar ƙarya domin karɓar N5m a wurin mahaifinsu Mista Kamto...
    Mai ba da shawar ga Jagora ya jaddada cewa: Iran za ta mayar da martani da karfi ga duk wata gwamnati da ke neman yin amfani da hanyar Zangezur ta hanyar da ba ta dace ba Ali Akbar Wulayati, mai ba da shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran kan harkokin kasa da kasa, ya yi gargadin cewa: “Duk wata gwamnati a yankin ko a wajenta da ke son maimaita gwajin da aka yi a baya game da hanyar Zangezur, za ta fuskanci martani mai karfi daga Iran.” A shafinsa na Twitter, Ali Akbar Welayati ya rubuta cewa: “A nan ma, wasu gwamnatocin da ba su nuna halin ko-in-kula ba, ba ruwansu da muradun kansu da na yankin,...
    Jiniyoyin gargadi sun tashi a HKI bayan da sojojin Yemen sun cilla sabbin makamai masu linzami kan HK. Kafafen yada labarain na HKI sun bayyana cewa makamai na yemen sun haddasa tashin jiniyoyin ne a tsakiyar kasar da kuma yankunan da kuma yankunan da ke gewaye da birnin Qudus. Majiyar sojojin yemen kuma ta bayyana cewa sun cilla makaman ne don tallafawa falasdinawa a gaza, wadanda HKI take kashewa da yunwa da kuma makamai a ko wace rana. Labarin ya bayyana cewa dubban dubatan yahudawan sun kideme suna kuma neman inda zasu fake daga boma-boman kasar ta yemen. Hukumar kwana, kwana, ta HKI wato ‘Israel’s Magen David Adom (MDA)’ bata bada wani rahon jikata da kuma rushe-ruehen da aka samu sanadiyyar faduwar...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk da karin kudin da gwamnatoci a matakin jiha suke samu daga asusun tarayya, ’yan Najeriya da dama suna korafin ba sa gani a kas.   Manazarta dai sun ce ko kafin karin ma ya kamata ya yi a ce ayyukan da gwamnatcin jihohi suke yi sun fi da ake gani Ko mene ne ya sa jihohi “ba sa kashe karin kudaden da suke samu yadda ya kamata”? NAJERIYA A YAU: Yadda Talauci Ke Hana Shayar Da Yara Nonon Uwa Zalla A Najeriya DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure Wannan shi ne batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin,...
    Shugaba Bola Tinubu ya bai wa ’yan wasan ƙwallon kwandon mata D’Tigress kyautar Dala dubu 100 da gidaje da lambar girmamawa ta OON, a matsayin karramawa bayan lashe kofin gasar ta bana. Shugaban ya kuma ba masu horar da ’yan wasan dala 50,000 kowannensu. Gwamnatin Kano ta karɓi rahoton binciken Kwamishinan da ya yi belin Danwawu WAEC ta saki sakamakon jarabawar 2025 Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan shugaban ya ’yan wasan ƙwallon ƙafa mata wata Super Falcons makamanciyar wannan kyautar ta dala 100,000 da lambar girma. A wannan Litinin din ce tawagar ’yan wasan ƙwallon kwando ta mata ta Nijeriya ta koma ƙasar bayan lashe gasar ƙwallon kwando ta mata ta Afirka, wato Afrobasket. Tawagar ta D’Tigress ta...
    Gwamnatin Kano ta karɓi rahoton kwamitin bincike da ta kafa domin gano haƙiƙanin gaskiya kan zargin da ake yi wa Kwamishinan Sufuri na jihar, Ibrahim Ali Namadi da shiga sha’anin belin wani da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi. Shugaban kwamitin, Barista Aminu Hussain, ne ya miƙa rahoton ga Sakataren Gwamnatin Kano, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, a ranar Litinin, inda ya bayyana cewa sun gudanar da cikakken bincike na adalci, tare da tuntubar dukkan masu ruwa da tsaki. WAEC ta saki sakamakon jarabawar 2025 Za a mayar da gidan yarin da ya haura shekara 100 zuwa gidan tarihi a Kano Babu dai cikakken bayanin abin da rahoton ya ƙunsa, to sai dai matakin da gwamnati za ta ɗauka ne zai...
    Shugaban Amurka ya aike da jakada zuwa Rasha tare da yin barazanar sanyawa Moscow takunkumi Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da cewa: Manzonsa na musamman Steve Witkoff zai ziyarci kasar Rasha a mako mai zuwa, yayin da wa’adin da ya sanyawa Moscow na kawo karshen yakin da take yi da Ukraine ke gabatowa. A halin da ake ciki kuma, ana ci gaba da gwabza yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine, inda Moscow ta sanar da lalata jiragen Ukraine guda 18. Yakin da ake yi a Ukraine na kara kamari zuwa ci gaba mai hatsari a daidai lokacin da wa’adin da shugaban Amurka Donald Trump ya gindaya wa Rasha ke gabatowa, da kuma halayensa na tunzura jama’a,...
    Sama da mayakan kungiyar ta’addanci ta Al-Shabaab 50 ne suka halaka a yankin kudu maso yammacin birnin Mogadishu fadar mulkin kasar somaliya Tawagar wanzar da zaman lafiya ta Tarayyar Afirka a Somaliya ta sanar a ranar Lahadin da ta gabata cewa; Sama da mayakan kungiyar ta’addanci ta Al-Shabaab 50 ne suka halaka a wani samame da dakarun sojin Somaliya suka kai a garin Bireire da ke kudu maso yammacin Mogadishu fadar mulkin kasar. Tawagar ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa: “A samamen hadin gwiwa da sojojin kasar Somaliya domin kwato garin Bireire a ranar 1 ga watan Agusta, ya haifar da hasara mai yawa ga ‘yan ta’addar, tare da kashe mayakan Al-Shabaab fiye da 50, wasu...
    An nemi wata jaririya sa’o’i kaɗan bayan haihuwarta an rasa a Cibiyar Lafiya ta Okeyinmi da ke Ado-Ekiti, babban birnin Jihar Ekiti, a ranar Litinin. Wani ganau ya ce an gano ɓatan jaririyar ne lokacin da ma’aikatan jinyar da ke bakin aiki suka je su duba lafiyarta da safiyar wannan Litinin ɗin. Za a samu ruwan sama kamar da bakin ƙwarya na kwanaki uku a faɗin Nijeriya — NiMet Shirin kashe N712bn kan gyaran filin jirgin Legas ya tayar da ƙura Lamarin na ba-zato-ba-tsammani ya haifar da fargaba musamman yadda ɗimauta uwar jaririyar da kuma wasu daga cikin mutanen da ke cikin harabar asibitin. Tuni dai an garzaya da ma’aikatan da ke kula da ɗakin haihuwa da uwar jaririyar da...
    Shugaban kungiyar malaman addinin musulunci ko –Council Of Ulema-na Tafawa Balewa a jihar Bauchi na tarayyar Najeriya Sheikh Dan’azuki Musa tafawa balewa, yayi kira ga kasashen musulmi da kuma sauran kasashen duniya da su dauki darasi a jajircewar JMI da turjiyarta ga HKI, a kuma matsayin hanya tilo ta kawo karshen HKI. Kamfanin dillancin labaran Iran Press ko IP na kasar Sheikh Dan’azumi yana fadar haka a lokacinda yayi hira da shi a Bauchi. Sheikh Dan’azumi ya kara dacewa , gwamnatin Amurka ce bayan dukkan ayyukan ta’addancin da HKI take aikatwa a Gaza. Ya ce kafin yakin kwanaki 12 da HKI ta kallafawa JMI, musulmi sun debe kauna da samun mafita ga matsalar al-ummar Palasdinu wacce aka dade ana fama...
    Rahotanni daga Gaza na cewa sojojin Isra’ila sun sake buɗe wuta kan Falasɗinawa da ke cikin tsananin buƙatar agaji a kusa da inda ake rabon kayan tallafi a cibiyoyi biyu, a jiya Lahadi. Asibitoci a Gaza sun ce aƙalla Falasdinawa 27 aka kashe. Rahotanni na cewa sojojin sun buɗe wa mutane wuta bayan isa gab da ɗaya daga cikin cibiyoyin rabon agajin na gidauniyar da Amurka da Isra’ila ke mara wa baya a Rafah. Sanan sauran kuma an kashe su ne a sansanin da ke tsakiyar Gaza. Har yanzu sojojin Isra’ila ba su yi martani ba kan wannan rahoton. Hamas ta ce ƙungiyar agaji ta Red Cross kaɗai za ta iya miƙa wa ‘yan Isra’ilar da take riƙe dasu a...
    Tawagar ƴan wasan kwando na matan Najeriya ta lashe gasar ƙwallon kwando ta Afirka karo biyar a jere, lamarin da ya sa ta kafar tarihin wannan bajinta a Afirka. Tawagar D’Tigress ta samu nasara ne a wasan ƙarshe bayan doke Mali da ci 78-64 domin ɗaukar kofin gasar karo na bakwai a tarihi. Ƴan wasan Najeriyar sun kankane gasar ƙwallon kwandon Afirka, inda suka yi nasara sau 29 a jere a duka wasan da suka buga ba tare da rashin nasara ba tun 2015. Nasarar D’Tigress na zuwa ne kimanin mako guda bayan da tawagar Super Falcons ta ƴan wasan ƙwallon kafar matan Najeriya ta lashe gasar ƙwallon ƙafar matan Afirka, karo na 10 a tarihi.
    Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Gusau/Tsafe ta tarayya Kabiru Amadu (wanda aka fi sani da Mai Palace) ya shirya taron addu’a na musamman ga jihar Zamfara da Najeriya baki daya, domin neman zaman lafiya da cigaba mai dorewa.   Taron addu’o’in wanda ya gudana a babban masallacin Juma’a na Tudun Wada da ke Gusau, ya hada malaman addinin Musulunci, da sarakunan gargajiya, da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa, da kuma daruruwan al’ummar jihar baki daya, duk sun ba da hadin kai wajen ganin an samar da zaman lafiya mai dorewa a jihar.   A nasa jawabin, Kabiru Mai Palace, ya bayyana taron a matsayin wani shiri na ruhi da nufin neman taimakon Allah wajen magance matsalar rashin...
    A ranar Lahadin da ta gabata ne dubban masu zanga-zangar suka yi zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasdinawa da kuma yin Allah wadai da kisan kiyashin da “Isra’ila ke yi” a Gaza. Taron wanda masu shirya taron suka yi wa lakabi da “March for Humanity”, ya ga mahalarta taron suna daga tutocin Falasdinawa da harba tukwane da kwanonin tukwane, abin da ke nuni da yanayin yunwa da yunwa da ke yaduwa a Gaza. Daga cikin wadanda suka halarci taron har da wanda ya kafa WikiLeaks Julian Assange da ‘yan majalisar Labour biyar, wadanda bayyanarsu ta ja hankali a cikin yanayi mai cike da rudani. Assange, wanda ya koma Ostiraliya a bara bayan an sake shi daga wani gidan yari na...
    Kocin Tottenham Frank, wanda ya koma Spurs daga Brentford a watan Yuni, ya yi godiya ga kyaftin din na Koriya ta Kudu, “shi gwarzo ne na gaskiya ga Spurs a kowane fanni, daya daga cikin manyan yan wasan da suka taba taka leda a gasar Premier inji kocin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rundunar Sojin Najeriya tare da haɗin gwiwar jami’an Hukumar DSS sun ceto Injiniya Joshua Saleh, wani malami a Jami’ar Taraba, wanda ’yan bindiga suka sace. An sace malamin ne a ranar 31 ga watan Yuli, 2025, a hanyar Chinkai–Kente zuwa Wukari, da ke Ƙaramar Hukumar Wukari a Jihar Taraba. Sai an samar da ’yantacciyar ƙasar Falasɗinu za mu ajiye makamai — Hamas An ƙara hakimai 6 a Masarautar Katsina Bayan samun sahihan bayanai, sojoji da DSS suka fara bincike tare da ƙoƙarin ceto shi a wurare da dama, ciki har da Kente, Sondi 1 da 2, Yaku, da Warawa. A cewar Laftanar Umar Muhammed, mai magana da yawun rundunar, sojojin sun yi arangama da ’yan bindigar, inda suka yi musayar...
    Kungiyar Hamas wacce takr iko da Gaza kuma take gwagwarmaya da HKI tun shekara ta 2023 a baya-bayan nan, ta bayyana cewa ba za ta ajiye makamanta ba sai an kafa kasar falasdinu mai zaman kanta, wanda yin watsi ne da bukatar HKI na shafe kungiyar daga doron kasa. Shafin labarai na Internet Arab News na kasar Saudiya ya nakalto kungiyar tana fadar haka bayan da taron tattaunawa ta tsagaita budewa juna wuta na kwanaki 60 ya tashi baram-baram a birnin Doha na kasar Qatar. Labarin ya kara da cewa, a ranar Talatan da ta gabata ce, kasashen Qatar da Masar suka amince da ra’ayin samar da kasashe biyu a kan kasar Falasdinu da aka mamaye, a matsayin hanya Tilo...
    Ƙungiyar Hamas ta sake jadadda matakinta na cewa ba za ta taɓa ajiye makami ba, har sai lokacin da duniya ta amince da samar da ’yantacciyar ƙasar Falasɗinu a yankin Gabas ta Tsakiya, wani abu da zai sake mayar da yarjejeniyar zaman lafiya da ake ƙoƙarin ƙullawa baya. A halin da ake ciki yanzu haka ana wata tattaunawa wadda ba ta kai tsaye ba tsakanin Isra’ila da Hamas don ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki 60, da kuma sakin mutanen da ke riƙe a hannun ɓangarorin biyu. A Talatar da ta gabata ne ƙasahen Qatar da Masar suka sanar da matakin ƙasashen Saudi Arabiya da Faransa na goyon bayan samar da ƙasar Falasdinu, don tabbatar da dawamammen zaman lafiya a...
    Rundunar sojin Jamus ta fara gudanar da aikin jefa kayayyakin gaji da suka hada da abinci da magunguna ta sama a Zirin Gaza. Ma’aikatar Tsaron Jamus da ke Berlin, fadar gwamnatin kasar, ce ta tabbatar da hakan, inda ta ce jiragen rundunar sojin sama sun ajiye kunshin tallafi 34 dauki da tan 14 na abinci da kuma magunguna. Ambaliya: Mutum 165 sun mutu a Nijeriya a bana — NEMA Dadiyata: Buhari ya gaza nemo shi, Tinubu yana da lokaci — Amnesty Sai dai a cewar Ministan Tsaron Jamus, Moris Pistorius kai tallafi ta sama ba zai yi wani babban tasiri ba. A cewar Majalisar Dinkin Duniya, Zirin na bukatar tallafin tan dubu 62 na abinci a duk wata domin...
    Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International, ta ce Gwamnatin Tarayya ta yi sakaci game da ɓacewar ɗan gwagwarmaya Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata. A wata sanarwa da ta fitar, Amnesty, ta ce abin takaici ne ganin cewa shekara shida kenan da Dadiyata ya ɓace ba tare da wani sahihin bayani ba. Mutum ɗaya ya rasu, an jikkata wasu yayin arangama da ’yan sanda a Abuja Rufe gidan rediyo ya haifar da cece-ku-ce a Neja Dadiyata ya ɓace ne a ranar 2 ga watan Agustan 2019, bayan wasu mutane ɗauke da makamai sun shiga gidansa da ke unguwar Barnawa a Jihar Kaduna, suka tafi da shi. Tun daga wannan lokacin, iyalansa da abokansa ke jiran jin...
        Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wani fim mai suna “Dead to Rights”, wanda aka shirya game da kisan kiyashin da aka yi a birnin Nanjing, ya mamaye kasuwar fina-finai ta lokacin zafi ta kasar Sin, inda kudin shigar da aka samu da shi ya zarce yuan biliyan daya, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 140 cikin kwanaki takwas kacal. Wanda aka yi amfani da ingantattun shaidun hotuna na ta’asar yakin da Japanawa suka aikata a lokacin kisan kiyashin Nanjing, Fim din na “Dead to Rights” ya ba da labari ne na wani rukunin fararen hula na kasar Sin da suka nemi mafaka a dakin daukar hoto a lokacin muguwar mamayar da azzaluman Japanawa suka yi a birnin Nanjing. A wani yunkuri na neman tsira da rayukansu hajaran-majaran,...
    Bayan mutane da dama sun nuna ɓacin ransu kan al’amarin, gwamna Abba Yusuf ya kafa kwamiti domin bincikar lamarin, tare da umarnin a miƙa masa rahoton cikin mako guda. Gwamnan, ya taɓa goyon bayan jami’an tsaro wajen kama Danwawu, kuma ya umarci NDLEA ka da su sake shi. Wani jami’i ya ce: “Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ɗauki wannan aiki na Kwamishina a matsayin cin fuska ga gwamnatinsa da kuma yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi.” An ruwaito cewar gwamnatin Jihar Kano ta shirya wani shiri a ɓoye domin kama Danwawu, wanda Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Bakori ya jagoranta. Me Ya Sa Gwamnan Bai Kore Shi Ba? Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yi niyyar korar Namadi nan take, amma ya dakatar...
    Ƙungiyar Ma’aikatan Jinya ta Najeriya (NANNM), ta dakatar da yajin aikin gargaɗi na kwanaki bakwai da ta fara a faɗin ƙasar nan. Ƙungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata takarda da shugabanta ƙasa, Haruna Mamman, da sakatarenta, T.A. Shettima, suka sanya wa hannu. Rufe gidan rediyo ya haifar da cece-ku-ce a Neja Jami’ar Umaru Yar’adua ta kori ɗalibai 57 kan satar jarabawa Sun fara yajin aikin ya fara ne a ranar Laraba tare da niyyar shafe kwanaki bakwai suna yin sa. Ma’aikatan jinyar sun shiga yajin aikin ne saboda ƙarancin albashi, ƙarancin ma’aikata, da kuma rashin ingantattun wuraren aiki. Wannan yajin aiki na zuwa ne a daidai lokacin da likitoci ke takun saƙa da gwamnati kan batutuwan suka shafi jin...
    A cewar NANNM, sun dakatar da yajin aikin ne domin ci gaba da tattaunawa bisa alƙawarin da gwamnati ta ɗauka na aiwatar da buƙatun cikin ƙanƙanin lokaci. Takardar ta ce, “Kwamitin zartarwa na ƙasa ya yaba da matakan da gwamnatin tarayya ta fara ɗauka, musamman yadda ta bayyana lokacin da za ta aiwatar da buƙatunmu guda tara da muka gabatar.” Takardar da shugaban ƙungiyar NANNM, Kwamared Haruna Mamman, da sakataren janar, Dr. A. Shettima suka sanya wa hannu, ta umarci mambobinsu da su koma bakin aiki nan take. Haka kuma shugabannin na ƙasa za su ci gaba da lura da yadda gwamnati za ta cika alƙawuran da ta ɗauka. Ƙungiyar ta kuma gargaɗi duk wata cibiyar lafiya ko hukuma da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kasar Iran Masuod Pezeshkiya ya yi juyayin shahadar Isma’ila Haniyya marigayi shugaban kungiyar Hamasa a nan Tehran shekara guda kenen. Ya kuma jaddada cewa JMI ba za ta taba manta da shi ba. Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto shugaban yana bayyana wannan juyayin a ranar da  Haniya yake cika shekara guda da shahada, sannan shahadarsa ya zo dai dai da ranar da Pezeshkiyan ya fara shugabancin kasar. Labarin ya kara da cewa shugaba Pezeshkiyan ya bayyana haka ne a shafinsa na X ya kuma kara da cewa a ranar da na fara aiki a matsayin shugaban kasa kenen, makiya HKI da kuma Amurka suka sanyamu cikin bakin ciki tare da kashe bakommu wanda ya zo ya taya mu...
    An yi jana’izar Marigayi Sarkin Gudi da ke Jihar Yobe, Alhaji Isa Bunuwa Madugu Ibn Khaji, ranar Juma’a a Abuja, inda ya rasu a wani asibiti bayan fama da jinya. Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni ya ranar Juma’a ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar wajen hakartar taron. Sanarwar da Mamman Mohammad daraktan yada labarai na gwamna Buni ya fitar ta ce, gwamnan da ke halartar wani taro a Abuja ya yanke ziyarar tasa domin halartar jana’izar marigayi Sarkin da kansa. Gwamna Buni ya samu rakiyar Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Yobe, Alhaji Chiroma Buba Mashio, Sanata Ibrahim  Mohammed Bomoi, Sanata Musa Mustapha, da ’yan Majalisar Wakilai. Sauran sun haɗa da sakataren gwamnatin jihar, Baba Malam Wali, ’yan majalisar dokokin jihar, da  kwamishinoni,...
    Iyalai ‘yan Sudan da dama ne suka taru a babbar tashar jirgin kasa ta birnin Alkahira, dauke da jakunkuna da kayayyaki a lokacin da suke shirin komawa gida bayan da suka tsere daga rikicin Sudan. Suna cikin dubban ‘yan kasar Sudan da suka rasa matsugunansu da ke kan hanyarsu ta komawa daga Masar zuwa yankunan da sojojin Sudan suka kwato kwanan baya daga dakarun gaggawa na gaggawa a birnin Khartoum da bayanta tun farkon wannan shekara. Iyalan sun kasance suna jiran shiga jirgin kasa da zai nufi birnin Aswan da ke kudancin Masar. Daga nan ne za su yi tafiya ta bas zuwa babban birnin kasar Sudan, Khartoum, a cewar wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayar....
    A yanzu haka dai ratotannin sun tabbatar da cewa APC da ADC suna gogayya wajen neman samun goyon bayan mutanen arewa kafin babban zaɓen 2027 ya ƙariso. A ranar 1 ga Yuli, manyan ƴan adawa da suka hada da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi da dan takarar shugaban ƙasa a APC a 2023, Rotimi Amaechi, da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, sun gabatar da ADC a matsayin hadakar jam’iyyar adawa domin ƙalubalantar Tinubu a 2027. Shugabannin ADC sun ci gaba da yin ƙoƙari don samun goyon bayan mutanen arewacin Nijeriya da sauran yankuna tun bayan buɗe jam’iyyar. A taron, Mark ya buƙaci shugabannin arewacin Nijeriya da...
    Kungiyar Ma’aikatan jinya da Ungozoma ta Ƙasa (NANNM) ta mayar wa da gwamnati martanin cewa har yanzu tana ci gaba da gudanar da yajin aikin da take yi. Ministan Lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Ali Pate, ne dai ya bayyana cewa ƙungiyar ta janye yajin aikin gargaɗin. An ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su a Kebbi Rundunar sojin ruwa za ta kafa sansaninta a Kebbi Da yake magana da manema labarai bayan wani taron sirri da aka yi a Abuja ranar Juma’a, Pate ya ce matakin ya biyo bayan yarjejeniyoyin da gwamnati da shugabannin Ƙungiyar NANNM suka cimma ne. Amma da aka tuntuɓi shugaban Ƙungiyar na ƙasa, Morakinyo Rilwan ya ce ba gaskiya ba ne cewa an...
    Tarihin dan’adam ya nuna yadda ƙabilu daban-daban, ke nuna ƙin amincewa da auratayya ta haɗin gambiza a tsakanin ƴaƴansu da wasu ƴan ƙabilar da ba tasu ba. Hatta a cikin ƙabila daya ana samun wannan nuna wariya, tsakanin dangi, ko masu hali da talakawa. Hatta a tsakanin addini daya, bambancin aƙida ko fahimta na sa a hana masoya aure, ko da kuwa sun cancanci kasancewa tare. Kodayake zamani na sauyawa, ilimi na ƙara yawa, mutane na dada samun wayewa kan ƴancin su, amma a wurare da dama aure daga wata ƙabila zuwa wata, abin kyama ne. Wasu na son ko da za a auro daga wata ƙabila to, ya kasance ba auren fari ba ne. Ko kuma ya kasance...
    A Alhamis din nan ne dai kasar ta Habasha ta fito da Shirin shuka bishiyoyi har miliyan 700 a rana daya, ta hanar shigar da miliyoyin mutanen kasar. Fira ministan kasar ta Habasha Abi Ahmad yana son a rika tunawa da shi anan gaba ta hanyar shuka bishiyoyin da za su kai biliyan 50, daga nan zuwa shekara ta 2026. Tun da safiyar jiya Alhamis ne dai miliyoyin mutanen kasar ta Habasha su ka fito zuwa wuraren yin shukar, inda su ka rika haka ramukan da za su yi dashen bishiyoyin. Kakakin gwamnatin kasar ta Habasha, Tesfahun Gobezay ya bayyana cewa, da jijjifin Safiya, gabanin cikar karfe; 6;a.m, mutane miliyan 14.9 sun dasa bishiyoyin da sun kai miliyan 355.  Shi...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ruwan sama kamar da bakin kwarya tare da iska mai karfi da aka tafka a kwanan nan ya yi sanadin mutuwar mutane 44, yayin da wasu tara suka bace a birnin Beijing, kamar yadda aka bayyana a wani taron manema labarai da ya gudana a yau Alhamis. A yayin taron manema labarai da gwamnatin birnin Beijing ta gudanar a yau game da rigakafin ambaliyar ruwa da bayar da agajin gaggawa, an bayyana cewa, bala’in ambaliyar ruwan da ya auku kwanan nan ya shafi mutane sama da 300,000 tare da lalata gidaje 24,000 a birnin Beijing. Sai dai, yanzu haka birnin na Beijing na kara kokarin farfado da wutar lantarki, da share tituna, da kai muhimman kayayyaki ga mazauna yankin da...
    Yayin da yajin aikin gargadi na kasa baki daya da kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta kasa (NANNM) ta kira ya shiga rana ta biyu, iyalai sun fara kwashe ‘yan uwansu daga asibitocin gwamnati zuwa masu zaman kansu a jihar Filato. A Asibitin Kwararru na Jihar Filato, dogon layin masu amsar katin asibiti don neman kulawa da lafiyarsu ya yi batan dabo a lokacin da wakilinmu ya ziyarci asibitin. Gwamna Zulum Ya Sauke Kwamishinoni Biyu Tare Da Maye Gurbinsu Da Wasu Uganda Ta Jinjinawa Gudummawar Sin Ga Manufofin Wanzar Da Zaman Lafiya A Yankin Kahon Afirka Wata mata mai suna Misis Mary David, wacce ta yi rajista a asibitin duba lafiyar mata masu juna biyu, ta shaida wa wakilinmu cewa...
    Firaminista Mark Carney ya ce Canada ta shirya amincewa da kafa ƙasar Falasɗinu a cikin watan Satumba, inda ta zamo ƙasa ta uku daga cikin ƙungiyar G7 da ta fitar da irin wannan sanarwa a cikin kwanakin nan. Carney ya ce za su ɗauki matakin ne ta la’akari da wasu sharuɗɗan gyara daga ɓangaren hukumomin Falasɗinu da suka haɗa da amincewa da tsarin dimokuraɗiyya da kuma gudanar da zaɓe ba tare da ƙungiyar Hamas ba a shekara mai zuwa. Sanarwar tasa na zuwa ne kwana ɗaya bayan Birtaniya ta bayyana goyon bayan ta ga kafa ƙasar Falasɗinun a watan Satumba mai zuwa, kuma mako ɗaya bayan Faransa ta yi irin wannan sanarwa. Ma’aikatar harkokin wajen Isra’ila ta yi watsi da...
    Hukumar kula da da’ar ma’aikata ta sanar da cewa, a halin yanzu ana iya  bayyana kadarorin ma’aikatan ta hanyar yanar gizo, wani mataki da aka tsara domin saukaka aikin da kuma kara yin lissafi.   Daraktan ofishin na jihar Jigawa Abubakar Bello ne ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci shugaban ma’aikatan jihar Alhaji Muhammad K. Dagaceri a ofishin sa.   Abubakar Bello ya jaddada cewa sabon shirin na da nufin rage dinbin aikin dake gaban ma’aiakata da kuma saukaka tantance kadarorin domin yaki da cin hanci da rashawa a cikin tsarin.   “Mun sauya dabara zuwa rajista ta yanar gizo don bayyana kadarorin, muna ba wa mutane damar kammala aikin daga gidajensu. Duk da haka, muna neman goyon...