CORET Zata Ciyarda Makarantun Makiyaya Shida A Jihohin Kaduna Da Jigawa
Published: 24th, February 2025 GMT
Kungiyar Tarayyar Makiyaya ta CORET ta ce zata tallafawa yara makiyaya 1,600 a makarantun makiyaya guda shida a Jihohin Kaduna da Jigawa a wani yunƙuri na rage ƙarancin abinci da rashin ingantaccen abinci.
Sakataren Janar na CORET, Mohammed Bello Tukur ne ya bayyana hakan a lokacin ƙaddamar da shirin ciyar da ɗalibai na haɗin gwiwa a Laddauga, wurin kiwon dabbobi na Kachia a Jihar Kaduna.
Ya bayyana cewa, manufar wannan shiri ita ce tallafa wa shirin ciyar da ɗalibai na makarantun makiyaya.
Sakatare Janar ya ƙara da cewa kashi 60 na waɗanda za su amfana ‘yan mata ne, kuma shirin zai ƙarfafa ilimin kyawawan ɗabi’u a fannin abinci mai gina jiki, tsafta, tsabtace muhalli, da kuma sarrafa albarkatun ƙasa yadda ya dace.
Mohammed Bello Tukur ya bayyana cewa shirin yana kuma da niyyar samar da damammakin tattalin arziki da haɗin kai ga mata a cikin al’ummomin makiyaya guda shida da aka zaɓa.
“Muna son rage nauyin ciyar da ɗalibai da ke kan iyaye da kuma ƙara yawan yara da ke shiga makaranta. Bayan Kaduna, muna kuma duba Jihar Jigawa, Katsina, Taraba, Adamawa da Neja. Mun haɗa al’umma don dorewar shirin. Muna son gudanar da shirin na tsawon watanni 36.”
A jawabin Ministan Raya Dabbobi, ya bayyana cewa wannan shiri ya zo a daidai lokaci, kuma zai samar da abinci mai gina jiki ga yara wanda zai ƙara musu basira.
“Shirin zai samar da abinci mai gina jiki ga yara wanda zai ƙara musu basira kuma zai ƙarfafa su wajen zuwa makaranta, wanda hakan zai rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta. Haka kuma zai sa su zama masu amfani ga al’umma.”
Ministan wanda ya samu wakilcin Mataimakinsa na Musamman, Dr. Ishaq Bello, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da bullo da manufofi da shirye-shiryen da za su inganta kiwon dabbobi a ƙasar.
Tun da farko, Daraktan Noma da Raya Kauyuka na ECOWAS, Alain Traore wanda Dr. Saater Kumaga ya wakilta ya bayyana cewa ECOWAS na aiwatar da ayyuka 127 a ƙasashe memba 15.
Ya bayyana cewa daga cikin waɗannan ayyuka, guda uku ana aiwatar da su ne a Jihar Kaduna.
Manajan shirin, Dr. Abdullahi Umar ya gode wa al’ummar Kachia, yana mai roƙon su su bayar da haɗin kai don nasarar shirin.
Hakimin Ladduga, Alhaji Ahmed Jibril ya tabbatar wa CORET da cikakken haɗin kai don nasarar shirin.
An aiwatar da shirin ne a Kachia, wurin kiwon dabbobi na Laddauga a Jihar Kaduna da kuma Maigatari Trans-boarder axis a Maigatari LGA Jihar Jigawa, tare da tallafin Hukumar ECOWAS – Cibiyar Raya Yankin Noma (RAAF) da haɗin gwiwar Kungiyar Taimakon Ci Gaba ta Sifen (SDC).
Makarantun da aka zaɓa a Kaduna sun haɗa da: Makarantar Firamare ta Makiyaya Wuro Nyako wurin kiwon dabbobi na Kachia, Makarantar Firamare ta Makiyaya Mbela Biradam Ladduga wurin kiwon dabbobi na Kachia, da Makarantar Firamare ta Makiyaya Tiggirde Ladduga wurin kiwon dabbobi na Kachia.
A Maigatari Trans-boarder axis a Jigawa kuwa sun haɗa da: Makarantar Firamare ta Makiyaya Lawan Dutsi, Makarantar Firamare ta Makiyaya Bulama Kauje da Makarantar Firamare ta Makiyaya Gidan Tinau.
COV: Adamu Yusuf
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Daliban Makarantar Kudi Suka Fi Na Gwamnati Kokari
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Duk da cewa gwamnati na da dubban kwararrun malamai a makarantunta, har yanzu ana ganin ɗaliban makarantun gwamnati na kasa da na makarantun masu zaman kansu wajen ƙoƙari da kuma sakamakon jarabawa.
Wannan matsala ta daɗe tana jawo muhawara tsakanin iyaye, malamai da hukumomin ilimi.
Wasu na ganin matsaloli ne da ba za su rasa nasaba da rashin kulawa da watsi da harkar ilimi da gwamnati ta yi ba.
Ko wadanne dalilai ne suka daliban makarantun masu zaman kansu suka fi kokari idan aka kwatanta da daliban makarantu na gwamnati?
NAJERIYA A YAU: Shin Ko Sauya Hafsoshin Tsaro Zai Kawo Karshen Aikin Ta’dda A Najeriya? DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa PDP Ta Ki Sayarwa Sule Lamido Fom Din Takarar Shugaban Jam’iyyaWannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan