Yawan Motocin Da Sin Ta Fitar Zuwa Ketare A 2024 Ya Karu Da Kaso 23%
Published: 11th, February 2025 GMT
Kungiyar masu samar da motoci ta kasar Sin CPCA, ta ce bangaren fitar da motoci daga kasar Sin zuwa kasashen ketare, ya ci gaba da samun tagomashi a shekarar 2024.
A cewar CPCA, kasar Sin ta fitar da jimilar motoci miliyan 6.41 zuwa kasashen waje a bara, adadin da ya karu da kaso 23 bisa dari a kan na shekarar 2023.
Kasashen da ke kan gaba, wadanda aka kai wa motocin na kasar Sin sun hada da Rasha da Mexico da Hadaddiyar Daular Larabawa, yayin da kasashen da suka ingiza ci gaban da Sin ta samu wajen fitar da motocin suka hada da Rasha da Hadaddiyar Daular Larabawa da Brazil da Belgium da Saudiyya. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
এছাড়াও পড়ুন:
Sin: Ya Kamata A Warware Sabanin Tattalin Arziki Da Cinikayya Ta Hanyar Tattaunawa
Yau Litinin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Guo Jiakun, ya shirya taron manema labaru na yau da kullum.
A wajen taron, wani dan jarida ya yi tambaya game da sabuwar yarjejeniyar kasuwanci da aka kulla tsakanin Amurka da kungiyar EU. A yayin da yake ba da amsa, Guo Jiakun ya ce, kasar Sin a ko da yaushe tana ba da shawarar cewa, ya kamata dukkan bangarori su warware bambance-bambancen tattalin arziki da cinikayya ta hanyar tattaunawa, domin kiyaye yanayin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa.
Bugu da kari, dangane da taron tattauna batun tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka a kasar Sweden, Guo Jiakun ya bayyana cewa, matsayin kasar Sin kan batutuwan da suka shafi tattalin arziki da cinikayya a bayyane yake. Ana sa ran Amurka za ta yi aiki tare da kasar Sin wajen aiwatar da muhimman shawarwarin da shugabannin kasashen biyu suka cimma a wata tattaunawa ta wayar tarho.
Game da rikicin kan iyakar kasashen Cambodia da Thailand, Guo Jiakun ya ce, kasar Sin za ta tsaya tsayin daka wajen tabbatar da gaskiya da adalci, da ci gaba da yin cudanya da kasashen Cambodia da Thailand, da sa kaimi ga zaman lafiya da tattaunawa.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp