Gwamna Lawan Ya Shaidawa Bankin Duniya Cewa Sun Yi Nasarar Yakar ‘Yan Bindiga A Zamfara
Published: 9th, February 2025 GMT
“Ina so na fara da godiya ga Bankin Duniya kan tallafin da yake ci gaba da bai wa jiharmu. Mun daidaita manufofin ci gabanmu da manufar Bankin Duniya na kawar da talauci da inganta ci gaba mai dorewa.”
“Mun kuma lura da kalubalen tsaro da a baya suka yi tasiri wajen aiwatar da ayyuka a jihar Zamfara, musamman wadanda suka kawo cikas ga cimma burin da aka sanya a gaba.
“Mun inganta matakan tsaro ta hanyar kwararan matakai da jihar ta dauka na inganta tsaro da kara daukar matakan dakile barazanar tsaro.”
“Gwamnatinmu ta dukufa wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi ta hanyar samar da isassun kayan aiki da tallafi ga jami’an tsaro domin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.” Cewar Gwamna Dauda
Gwamna Lawal ya baiwa ma’aikatan bankin duniya tabbacin tsaron lafiyarsu a lokacin bayar da tallafi da sanya ido da kuma samar musu masauki da sufuri da dai sauransu.
কীওয়ার্ড: Bankin Duniya Gwamna Lawal Yan bindiga Zamfara
এছাড়াও পড়ুন:
Xi Jinping Ya Ziyarci Sabon Bankin Raya Kasashen BRICS
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp