2025-06-16@00:44:13 GMT
إجمالي نتائج البحث: 115

«ɗanwasan tsakiya na»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Jami’ai a yankin kudu masu yammacin Pakistan sun ce aƙalla mutum 11 sun mutu sakamakon fashewar wata motar da ke ɗauke da masu haƙar ma’adinai a yankin Harnai da ke lardin Balochistan. Jami’an yankin sun ce suna ci gaba da bincike kan abin da ya haifar da fashewar, to amma ana kyautata zaton abubuwan fashewa ne da ƴanbindiga ke amfani da su. Lardin Balochistan mai albarkar ma’ainai ya shafe gomman shekaru yana fama da matsalolin ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai na ƙabilar Baloch.
    Wata Babbar Kotu a Abuja, ta ɗage yanke hukunci kan buƙatar bayar da belin Tsohon Shugaban Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, wanda ke fuskantar zargin cin hanci da rashawa. A ranar Laraba ne, Mai shari’a Chinyere Nwecheonwu, ta bayar da umarnin ci gaba da tsare Yusuf a gidan gyaran hali na Kuje har zuwa ranar 27 ga watan Fabrairu. Sojoji sun doki ’yan sanda kan kama ‘mai laifi’ Fitaccen ɗan siyasa Ahmadu Haruna Zago ya rasu A lokacin ne kotun za ta yanke hukunci kan buƙatar bayar da belinsa. Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), na zargin Yusuf da karkatar da kuɗaɗen gwamnati lokacin da yake jagorancin NHIS a shekarar 2016. Ana...
    Babban layin wutar lantarkin Najeriya, ya faɗi a karon farko a shekarar 2025, lamarin da ya haddasa ɗaukewar wuta a wasu sassa. Wannan matsala ta haifar da katsewar wuta a wasu sassan ƙasar, wanda ya jefa masu amfani da lantarki cikin damuwa. Na yi nadamar yi wa Tinubu kamfe a 2023 — Ɗan Bilki Kwamanda Yadda na ƙi karɓar cin hancin N5bn a gwamnatin Tinubu – Tsohon Hadimi Cikin wata sanarwa da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC), ya fitar a shafinsa na X, ya bayyana cewa matsalar ta faru ne da misalin ƙarfe 11:34 na safiyar ranar Laraba. Sai dai AEDC, ya ce ana aiki tare da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da dawo da wutar da...
    An tafi da shi tare da wasu mutane uku da suka haɗa da ɗan uwansa da matarsa da ɗansa a yayin harin.   An tattaro cewa, jigon na APC ya kai ziyara gidan ɗan uwansa ne lokacin da ‘yan bindigar suka kai harin.   Sai dai, an tsinci gawar matar dan uwansa ​​mai suna, Madam Esther, a kusa da unguwar Ijah-Gbagyi da ke karamar hukumar Tafa a jihar Neja da safe.
    Kotu ta tsare wani ɗan fashi da ya yi wa ɗalibai mata uku na Jami’ar Jihar Kwara fyaɗe. Matashin da dubunsa ta cika yi wa ɗaliban fyade ne a yayin wani fashi a ɗakunan kwanan ɗalibai mata a cikin dare. Ya yi musu wannan aika-aika tare da yunƙurin kisa ne a daƙinsu kwanan ɗalibai mata da ke wajen harabar jami’ar a yankin Malete a ranar 2 ga watan Disamba, 2024. A yayin gurfanar da matashin a gaban Kotun Majiatare ta Jihar Kwara da ke birnin Ilorin, an tuhume shi da yin amfani da makami wajen yi wa ɗaliban munanan raunuka, tare da yi musu fyaɗe da kuma sace wayoyin iPhone 13 PronMax da iPhone 11 Pro Max. ’Yan sanda na...
    Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da wasu ’yan mata shida masu shekaru tsakanin 15 zuwa 17 a yankin unguwar Pandogari da ke Ƙaramar hukumar Rafi ta Jihar Neja. Mazauna garin sun shaida wa Aminiya cewa, da tsakar daren Laraba ne ’yan bindigar suka kaiwa unguwarsu hari inda suka kashe wani ɗan banga mai suna Aliyu Aminu tare da yin garkuwa da ’yan matan. ’Yan fashin teku sun sace jirgin fasinja mutum 11 sun ɓace a Ribas Jirgin Amurka ɗauke da mutum 10 ya ɓace Mazauna yankin sun ce, maharan da suke da yawa sun shiga cikin unguwar ne daga yankin Birnin Gwari, ta Kwalejin fasaha ta Mamman Kontagora da ke Pandogari. Majiyoyi sun ce an kai ’yan matan da...
    Ma’aikata a Jihar Alaska da ke Amurka sun bazama neman wani ƙaramin jirgin sama na kasuwanci a ranar Juma’a da ya ɓace ɗauke da mutum 10. Kamar yadda hukumomin yankin suka ce, a wani sabon afkuwar da ya afku ta jirgin Amurka. Magungunan Jabu: ’Yan majalisa sun nemi yin hukuncin ɗaurin rai da rai Lakurawa sun kashe mutum 1 sun jikkata 6 a Kebbi Rundunar ’yan sandan Jihar Alaska ta sanar da cewa, jirgin samfurin Cessna Caraɓan mai fasinjoji tara da matuƙin jirgi ɗaya ne, an samu rahoton ne ranar Alhamis. Jirgin da ya tashi daga Unalakleet zuwa Nome da ƙarfe 4:00 na yamma agogon Alaska (0100 GMT) da ya ɓace. Biranen biyu suna da nisan mil 146 (kilomita 235)...
    Shugaba Bola Tinubu, ya buƙaci hukumomin ilimi su tabbatar da cewa makarantun gwamnati da masu zaman kansu sun ɗauki matakan kare ɗalibai daga haɗura. Wannan kira na zuwa ne bayan da wata gobara ta yi ajalin almajirai 17 a wata makarantar tsangaya da ke garin Ƙauran Namoda, a Jihar Zamfara. Allah Ya yi wa Sheikh Ishaq Yunus rasuwa Tinubu ya yi sauye-sauye a Jami’ar Abuja Gobarar, wacce ta tashi da daddare a ranar Talata, ta kuma jikkata wasu almajirai bakwai, amma yanzu haka suna asibiti ana kula da su. Shugaba Tinubu ya jajanta wa Gwamnatin Jihar Zamfara da iyalan waɗanda da suka rasa ’ya’yansu a wannan iftila’in, tare da yin addu’ar samun sauƙi ga waɗanda suka jikkata. Ya buƙaci makarantu...
    An kama wani ɗalibin firamare mai shekara 13 ɗauke da bindiga a makaranta, inda yake barazanar harbe abokan karatunsa da ita. Bayan nan ne jami’an tsaro suka yi nasarar kama shi a Makarantar Firamare ta St. Paul da ke ƙauyen Ikot Ibiok a Ƙaramar Hukumar Eket a Jihar Akwa Ibom. A safiyar Alhamis ne kakakin runduanr ’yan sandan jihar, DSP Timfon John, ta sanar da kama yaron. DSP Timfon John ta bayyana cewa, a yayin bincike sun gano cewa yaron ya shafe kimanin wata uku yana zuwa da bindigar makaranta. An kashe wa ma’aurata ’ya’yansu uku an ɓoye gawarsu a firinji Zargin Tinubu: Gaskiya Naja’atu ta fada kan Nuhu Ribadu —El-Rufai NAJERIYA A YAU: Tasirin Yankan Angurya A Rayuwar Mata...
    Ɗan wasan gaba na tawagar Super Eagles ta Nijeriya da ke buga wasa a ƙungiyar Galatasaray Victor Osimhen, ya shigar da ƙarar wani ɗan jaridar Turkiya Tolga Bozduman bisa zargin ɓata masa suna. A cikin wani saƙo da wani makusancin Osimhen ya wallafa a shafinsa na X, ya ce za a fara sauraron ƙarar da ɗan wasan ya shigar bayan da ɗan jaridan ya zarge shi da naushin sa. Wannan dai na zuwa ne bayan da ɗan jarida Bozduman ya zargi Osimhe da cin zaraginsa, bayan tashi wasa 3-3 tsakanin ƙungiyarsa ta Galatasary da kuma Dynamo Kyiv. Yanzu haka dai Osimhen na fuskantar bincike kan lamarin, kuma ana ci gaba da ce-ce-ku-ce a kai. A makon da ya gabata ne...
    A wannan hirar, Shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatuil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS), Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya yi magana game da cece-ku-ce kan ɗaukar nauyin wani taron Al-Ƙur’ani da aka shirya. Da yake magana jim kaɗan bayan wata lacca ta musamman a sakatariyar JIBWIS ta ƙasa da ke Abuja a wannan makon, shugaban ya bugi ƙirji da cewa al’ummar Musulmi na da kuɗin da za su iya shirya taron. Aminiya: Za mu ka yi mana bayani kan mahimman abubuwa game da taron Al-Kur’ani da aka shirya? Amsa: Taron Al-Qur’ani mai zuwa a ranar 22 ga Fabrairu ya shafi gabatar da karatun Al-ƙur’ani mai girma, inda makaranta da mahaddata za su taru a bisa jagorancin Sarkin Musulmi na Sakkwato. Majalisar Ƙoli...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Adamawa ta kama wani mafarauci mai shekara 55 mai suna Yusuf Garba wanda aka fi sani da Gana kan zarginsa da tona kabari tare da yanke kan mijin mahaifiyarsa. A cewar jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan, SP Suleiman Yahaya Nguroje, wanda ake zargin ya amsa laifinsa ne a lokacin da ake masa tambayoyi. Matashi ya yi lalata da ’yan firamare biyu a Zariya Zaftarewar ƙasa ta kashe mata masu haƙar zinare a Mali Garba wanda ɗan asalin garin Tappare Kona Uku ne a ƙaramar hukumar Jada ta jihar, ya bayyana cewa ɗan marigayin ne ya tuntuɓe shi inda ya buƙaci kan mijin mahaifiyarsa don yin tsafi bayan rasuwarsa. Shekara guda bayan binne shi,...
    Wani jirgin kamfanin Max Air ya tsallake rijiya da baya yayin sauka a filin jirgin Malam Aminu Kano (MAKIA) a ranar Talata da daddare. Jirgin wanda yake ɗauke da fasinjoji 53 da ma’aikata shida yana dawowa daga Jihar Legas ne lokacin da haɗarin ya faru. Me kuka sani game da ficewar Mali, Nijar, da Burkina Faso daga ECOWAS? Mun kama mutum 46 da miyagun ƙwayoyi a Yobe — NDLEA Wani fasinja ya bayyana cewa jirgin ya rasa tayar gabansa yayin sauka a filin jirgin. Fasinjan ya yi karin bayani da cewa cewa tayar jigin ta fashe sannan ta kama da wuta a daidai lokacin da ya sauka cikin filin da misalin karfe 10:19 na dare. “Daidai lokacin da tayar ta...
    Ɗan wasan Nijeriya kuma gwarzon ɗan ƙwallon ƙafar Afrika, Ademola Lookman, ba zai buga wasan da Atalanta za ta kara da Barcelona a gasar cin kofin Zakarun Turai yau Laraba ba, sakamakon rauni da ya ji a gwiwarsa. A wata sanarwa da kulob ɗin Atalanta ya fitar, ya ce ɗan wasan mai shekaru 27 ya samu rauni a gwiwar dama a lokacin atisayen safiyar Talata, wanda ya hana shi tafiya Spain don buga wasan da ƙungiyarsa ke neman cancantar shiga zagayen 16 na ƙarshe. Tinubu Ya Yi Alƙawarin Inganta Wutar Lantarki A Nijeriya Gwamnan Bauchi Ya Sanya Hannu Kan Dokar Da Za Ta Daƙile Satar Yara A Bauchi  Duk da cewa kulob ɗin bai bayyana tsawon lokacin da Lookman zai...
    Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa Nijeriya na da wadataccen arzikin da za ta ci gaba da ɗawainiyar duk wasu tafiye-tafiyen Shugaba Bola Tinubu zuwa ƙetare. A bayan nan dai ’yan Nijeriya na ci gaba da bayyana damuwa kan yawan tafiye-tafiyen da shugaban ƙasar ke yi a kai-a kai zuwa ƙetare la’akari da tsadar rayuwa da ake fuskanta a ƙasar. Da kuɗin hayar gidana da ke Kaduna nake sayen abinci a yanzu — Buhari ’Yan sanda sun yi ƙarin haske kan barazanar harin ’yan ta’adda a Kano Ana kuma ci gaba da jefa ayar tambaya ko shin tafiye-tafiyen da shugaban ƙasar ke yi suna haifar da ɗa mai ido ta hanyar kalato wa ƙasar wata riba. Sai dai...