Man City ta nace wa Guimaraes, Chelsea na son Rodrygo
Published: 10th, April 2025 GMT
Manchester City na nace kan buƙatar ɗanwasan tsakiya na Newcastle da Brazil Bruno Guimaraes, mai shekara 27, yayin da take shirin rabuwa da ɗanwasanta na Belgium Kevin de Bruyne, mai shekara 33. (UOL esporte – in Portuguese)
Chelsea a shirye take ta biya fam miliyan 102 kan ɗanwasan Real Madrid da Brazil Rodrygo, mai shekara 24.
Manchester City na nazarin taya ɗanwasan tsakiya na AC Milan da Netherlands Tijjani Reijnders, mai shekara 26, kan tsakanin fam miliyan 42 zuwa fam miliyan 51 duk da ya sabunta kwangilar shi har zuwa 2030. (Calciomercato – in Italian)
Ana sa ran Everton za ta rasa ɗanwasan bayanta na Ingila Jarrad Branthwaite, mai shekara 22, yayin da Manchester United da Tottenham ke hamayya kan ɗanwasan. (Sun)
Chelsea da Newcastle na son ɗauko ɗanwasan Benfica da Girka Vangelis Pavlidis, mai shekara 26, kan fam miliyan 85 amma suna fuskantar hamayya daga Barcelona da Atletico Madrid. (Record – in Portuguese)
Arsenal da Liverpool na neman wani zaɓi maimakon Alexander Isak yayin da Newcastle ta dage cewa ba za ta sayar da ɗanwasan na gaba ba. (i paper)
Newcastle da Wolves da Brentford na hamayya kan golan Angers da Ivory Coast Yahia Fofana, mai shekara 24. (Football Insider)
Chelsea na kan gaba wajen buƙatar ɗanwasan tsakiya na Sunderland da Ingila Jobe Bellingham, mai shekara 19, duk da Manchester United da Arsenal da Tottenham da Brighton da Crystal Palace na ribibinsa. (Caught Offside)
Juventus za ta sayar da ɗanwasan tsakiya na Brazil Douglas Luiz, mai shekara 26, a bazara amma tana son kusan fam miliyan 34. (Tuttosport – in Italian)
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Wasanni ɗanwasan tsakiya na mai shekara fam miliyan
এছাড়াও পড়ুন:
Najeriya Na Asarar Dala Biliyan 10 Bayan Girbi Duk Shekara- Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin Tarayya ta ce Najeriya na rasa sama da Dala Biliyan 10 duk shekara sakamakon asarar amfanin gona bayan girbi.
Ministan Noma Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a wajen kaddamar da shirin Hanyar Inganta Noma da Kayayyakin Mire Rayuwa a Yankunan Karkara G.R.A.I.N a ƙaramar hukumar Birnin Kudu ta Jihar Jigawa.
Ya ce asarar na faruwa ne saboda rashin ingantattun wuraren ajiya, karancin ababen more rayuwa, sauyin yanayi da kuma ambaliya.
Kyari ya bayyana cewa noma na bada gudunmawar kashi 24 bisa 100 na Jimillar Darajar Kayayyaki da Ayyuka da Kasa ta Samar a Cikin Shekara GDP, inda ƙananan manoma ke samar da sama da kashi 70 bisa 100 na abincin da ake ci a ƙasa.
Ya jaddada cewa gwamnati za ta tallafa musu da kayan noma na zamani da wuraran kasuwanci domin inganta tattalin arziki.
A nasa jawabin, Gwamna Umar Namadi na Jigawa ya yaba da samun Cibiyar Cigaban Karakara ta Pulse ta farko a Jigawa, yana mai cewa za ta kawo sauyi a harkar noma da rayuwar jama’ar karkara.
Haka zalika, shi ma Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya ce haɗin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu zai taimaka wajen ci gaban tattalin arziki.
Shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kudu, Alhaji Builder Muhammad Uba, ya jaddada goyon bayansa ga shirin Renewed Hope Agenda na Shugaba Tinubu tare da yabawa gwamnatin Namadi kan sauya fasalin noma a jihar.
Usman Muhammad Zaria