Aminiya:
2025-11-03@09:58:29 GMT

Yadda bom ya tashi da ɗan gwangwan a Legas

Published: 12th, April 2025 GMT

Al’ummar garin Idi Araba da ke Ƙaramar Hukumar Munshin a Legas sun wayi gari da fashewar wani abu mai ƙarar gaske, wanda ya tayar da gobara a wani garejin ’yan gwangwan da ke unguwar.

Lamarin da ya faru ranar Alhamis na makon jiya ya yi sanadiyar mutuwar wani da ke sana’ar gwangwan mai suna Najib Zakiru, da ƙonewar sashin wani gida da ke daura da wajen da ’yan gwangwan ke sana’arsu.

Aminiya ta ziyarci inda lamarin ya faru unguwar IdiAraba, ta kuma zanta da mammalakin wajen sana’ar ta ’yan gwangwan, Alhaji Haruna Musa, wanda kuma shi ne shugaban masu sana’ar a yankin, inda ya shaida wa Aminiya cewa, suna zaune sai suka ji wata irin ƙara mai karfi, ko da suka zo wajen sai suka tarar da wuta ta tashi.

“Da muka zo mun yi ƙoƙarin kashe wutar, da jami’an ’yan sanda suka zo, sun fito da wasu bamabamai na soji guda biyu suka ce daya daga cikin bama-baman ne ya fashe. Wannan ne ya sa suka gayyato ƙwararrun jami’an tsaro a sashen kwance bam, suka zo, suka yi bincike, suka tafi da bama-baman.

“Wannan da Allah Ya yi wa cikawa shi ne ya taho da bama-baman kuma yana kokarin fasa guda daga cikinsu ne abun ya tashi, ya halaka shi, wanda zuwan jami’an tsaro ne suka sa aka killace wajen, aka rufe, aka hana mutane shiga, kuma haka ne ya janyo wutar da ba ta mutu ba, ta shafi wani gida da ke gefen wajen, inda ta kone ɗakuna biyar lamarin da ya janyo mutane gidan suka yi asarar kayayyakinsu da kuma mutsuguninsu”, in ji shi.

Haruna Musa ya shaida cewa, mutumin da hadarin ya rutsa da shi magidanci ne kuma ya bar mace guda da ’ya’ya biyu. Haka kuma baya ga shi babu wani da ya jikkata a sakamakon hadarin, ba kamar yadda ake faɗa a wasu jaridu ba cewa, mutum uku sun jikkata. Ya ce tuni aka yi jana’izarsa a bisa jagorancin Sarkin Hausawan IdiAraba, Alhaji Hassan Auyo.

“yanzu haka mutanen da wutar ta lalata wa gida ba su da wajen kwana, kuma yawancinsu mata ne zawarawa da tsofaffi da yaransu kanana. Mun yi magana da masu sana’ar gwagwan din domin a gyara masu wajen zamansu. Muna fatan mahukunta sun dubi wannan abu a matsayin hadari ne da ya auku, su kuma ba mu dama mu ci gaba da sana’armu. Muna jan kunnen manbobinmu, su guji kayayyaki masu hadari”, In ji shi.

Aminiya ta zanta da matan da suka rasa muhallinsu sakamakon gobarar da ta biyo bayan fashewar bam din. Maman Shahid da wutar ta kone kayan dakinta kurmus, ta shaida wa Aminiya cewa, ‘‘da fari ina kwance a kan gado ne sai karar bam din ta riguzo da rufin silin dakina suka zubo kuma sai na taso na fito daga dakin. Bayan nan kuma

ina zaune a waje ina kokarin yi wa yara abinci sai yaro ya ce, Umma hayaki. Ba mu yi aune ba sai ga wuta ta tashi, ta kone mana dakuna. A lokacin da na yi yunkurin fitar da tukunyar gas din da nake girki, bayan wannan duk kayanmu sun kone, yanzu haka rabe-rabe muke yi wajen da za mu kwanta tare da ‘ya’yanmu”, In ji ta.

Hakazalika, Malama Talatu da ita ma lamarin ya rutsa da ita ta shaida wa Aminiya cewa, tana wajen kasuwancinta na abincin da take dafawa, ta sayar lokacin da labarin ya riske ta, ta ce kayan ta da ke dakin duk sun kone ba su tsira da komai ba sai kayan da ke jikinsu, inda ta mika kokan bara ga mahukunta da masu hannu da shuni domin su taimaka masu.

A nata bangaren Malama Sa’adatu da aka fi sani da Maman

Fati cewa ta yi babu abun da za su ce sai dai su yi wa Allah Madaukakin Sarki godiya kasancewar babu wanda ya jikkata a cikin gidan nasu duk da cewa akwai tarin yara kanana da mata. “Wannan abin godiya ne, dukiya kuma da sauran kayan da muka rasa tunda dai muna da sauran kwana a gaba ai idan da rai akwai rabo. Babbar damuwarmu a yanzu ita ce wajen kwana, inda muke rabawa, mu kwana daban, inda yaranmu ke kwana daban. Muna fatan a gyara mana wajen kwana, mu samu inda za mu kwanta mu da yaranmu”, in ji ta.

Mista Olarewaju shi ne mamallakin gidan da gobarar ta kone, ya shaida wa Aminiya cewa, abun da ya fi damun sa shi ne halin da ’yan hayar da ke cikin gidansa. “Yanayin wahalhalun da ’yan hayarmu suka shiga shi ya fi damuna, domin mu gida ne ya kone za kuma a iya gyara mana, amma su sun yi asarar kayayyakinsu, kuma yanzu haka ba su da wajen kwana su da yaransu. Haka kuma lokaci ne na damuna, ka ga abun a tausaya masu ne, don haka muna kira ga mahukunta da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta kasa (NEMA) da su zo, su dubi halin da mutanen ke ciki, talakawa ne marasa karfi, yawancinsu ma zawarawa ne da tsofaffi, don haka suna neman agaji. Mu mun dauki wannan abu a matsayin hatsari ko ibti’la’i kuma muna zaune lafiya da Hausawa babu wata matsala a tsakankaninmu da su,” in ji shi.

A zantawar Aminiya da Sarkin

Hausawan Idi-Araba, Alhaji Hassan Abubakar Auyo ya shaida wa Aminiya cewa, sun sami labarin cewa dan gwangwan din da lamarin ya rutsa da shi ya tsinto bamabaman ne guda uku a wata kwata mai zurfi da ke bayan barikin soji na Ikeja, inda shekara 20 da suka wuce aka sami hadarin tashin bamabamai a Legas.

“Wannan wajen da sojin suka yi sharar bama-baman an samu wadanda suka watse jikin wannan kwata mai zurfi, mun sami labarin a nan ne ya tsinto bama-baman, ka san su ‘yan gwangwan da kayan karfe, ya zo, ya yi ta kokarin ya yanka abun ya ci tura, domin ba zallar karfe ba ne, daga nan ya sami guduma ya yi ta dukan bam din da ita, har ya kai ga ya ta shi, ya kuma yi masa mummunan lahani, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarsa, kuma bayan da labari ya zo mana, mun yi masa sutura bayan ‘yan sanda da ke bincike suka aminta da hakan. A kan wannan lamari babu irin jami’an tsaro da lamarin ya shafa da ba su zo nan ba, mun tattauna kuma mun shiga bincike ka’in da na’in, mun kuma gano lamarin ba shi da alaka da ta’addaci ko wani abu makamancin haka, kuma za mu dauki mataki domin kare afkuwar irin wannan a nan gaba. Don haka za mu yi zama na musamman mu yi taro da jami’an tsaro da shugabaninn ’yan gwangwan domin kawo tsaretsaren da za su tsaftace sana’ar domin zaman lafiyarsu da ta jama’a baki daya,” in ji shi.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Gwangwan shaida wa Aminiya cewa jami an tsaro yan gwangwan wajen kwana

এছাড়াও পড়ুন:

Al’ummar Kauru Sun Koka Game Da Karuwar Hare-hare Da Ke Barazana Ga Gonaki Da Rayuka

Daga Yusuf Zubairu Kauru 

Al’ummar Karamar Hukumar Kauru ta Jihar Kaduna sun shiga halin kaka-ni-ka-yi duba da yadda rayukansu ke kasancewa cikin hadari yayin da suke gonakinsu.

A wata tattaunawa ta wayar tarho, wani jagoran matasa, Junaidu Ishaq, ya bayyana cewa kusan shekaru biyar ke nan da hare-haren ’yan bindiga ke ta faruwa akai-akai, wanda ya bar al’umma cikin fargaba da ƙuncin rayuwa.

Ya ce manoma suna shiga gonakinsu ne cike da fargaba domin komi na iya faruwa yayin da suke aiki a gonakin.

Mazauna yankin sun bayyana cewa Kauru, wadda aka fi sani da yawan gonaki da ke taka muhimmiyar rawa wajen samar da abinci a jihar Kaduna, yanzu manoma ba sa iya shiga gonakinsu cikin kwanciyar hankali saboda yadda ‘yan bindiga ke yawan kai musu hare-hare.

A koda yaushe iyayen yara suna fargaba kada ‘ya’yansu su yi nesa da su, yayin da iyalai da dama da ke fama da ƙangin talauci ke kara shiga cikin matsanancin hali.

Sun yi kira gwamnati da hukumomin tsaro su yi gaggawar kai ɗauki wanda zai bai wa manoman karkara kwarin gwiwa, waɗanda su ne ginshiƙin samar da abinci a yankin.

Mazaunan sun yi gargadin cewa idan ba a ɗauki mataki cikin gaggawa ba, hare-haren na iya haifar da ƙaruwar matsalar rashin abinci da yawaitar ƙaura daga yankin.

“Idan zuwa gona zai sa mutumya rasa ransa, to lalle akwai babban matsala,” in ji wani manomi a yankin.

Sun yi fatan cewa za a dawo da zaman lafiya a yankin, yadda ƙasar da Allah Ya albarkace su da ita za ta ci gaba da ciyar da al’ummar Kauru ba wurin binne su ba.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yadda matata ta ɓace a Abuja aka tsince ta a Sakkwato
  • Al’ummar Kauru Sun Koka Game Da Karuwar Hare-hare Da Ke Barazana Ga Gonaki Da Rayuka
  • 2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su
  • An Kashe Mutum 3 Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kan Iyakokin Kano
  • Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori
  • Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini ba — Tinubu
  • Zargin Kisan Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini — Tinubu
  • Gwamnatin Jihar Kwara Ta Kafa Kwamitoci 2 Don Tantance Wadanda Suka Yi Ritaya
  • An raba wa iyalan jami’an ’yan sandan da suka rasu a bakin aiki a Borno N63.4m
  • Yan Nijeriya Na Ɗanɗana Kuɗarsu Kan Jinkirta Cire Tallafin Mai – Sarki Sanusi