Gwamnatin Kaduna za ta ɗauki ma’aikatan lafiya 1,800 aiki
Published: 29th, March 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Kaduna, ta sanar da shirin ɗaukar ma’aikatan lafiya 1,800 aiki don inganta tsarin Kiwon Lafiya a Matakin Farko (PHC) a faɗin jihar.
Wannan zai taimaka wajen rage matsalar ƙarancin ma’aikata da kuma inganta ayyukan kiwon lafiya a jihar.
Ƙungiyar JNI ta raba wa marayu 50 kayan Sallah a Borno An sake harbe wani ƙasurgumin ɗan bindiga a ZamfaraKamar yadda Kwamishiniyar Lafiya, Hajiya Umma Ahmad, ta bayyana, wannan mataki zai taimaka wajen rage yawan mace-macen mata masu juna biyu da yara.
“Wannan mataki zai cike giɓin da ake da shi a cibiyoyin lafiya, domin tabbatar da samun ingantaccen kiwon lafiya ga al’ummar Kaduna,” in ji ta.
Gwamnatin jihar ta fara gyara cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko guda 255 tare da samar da kayan aiki na zamani da magunguna.
Wannan zai bayar da damar kula da cututtuka kamar su ciwon suga, hawan jini, da kuma bayar da agajin gaggawa ga mata masu naƙuda.
“Ingantaccen kiwon lafiya ba gata ba ne, haƙƙi ne,” in ji Hajiya Umma, yayin da ta ke jadadda ƙudirin gwamnatin jihar kan kiwon lafiya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Daukar aiki gwamnati Ma aikatan Lafiya kiwon lafiya
এছাড়াও পড়ুন:
Tsoffin ma’aikatan NECO na neman a biya su bashin haƙƙoƙinsu
Tsoffin ma’aikatan Hukumar Shirya Jarabawar (NECO), da suka yi ritaya na neman a biya su haƙƙoƙinsu da suke bin bashi.
Shugaban ƙungiyar tsofffin ma’aikatan, Dokta Abdullahi Rotimi Williams ne ya bayyana hakan a bikin ƙaddamar da hedikwatar kungiyar a Minna, babban birnin Neja.
Dokta Bashir ya zama shugaban Majalisar Shari’ar Musulunci ta Nijeriya Dokta Bashir ya zama shugaban Majalisar Shari’ar Musulunci ta NijeriyaShugaban ya kuma koka kan yadda gwamnatin Nijeriya ta maida ritaya abin fargaba a wurin ma’aikata saboda tarin ƙalubalen da ke biyo bayan hakan, musamman maƙalewar haƙƙoƙinsu.
“Da yawa tsoron ritaya ake yi yanzu. Don haka wannan ƙungiyar za ta taimaka wajen rage waɗannan matsalolin.
“Babban ƙalubalen da muke fuskanta shi ne na lafiya. Don haka ina roƙon shugaban hukumar da ya tabbatar cewa daga yanzu an kammala shirye-shiryen da suka kamata kafin ma’aikacin NECO ya yi ritaya.”
Ya kuma ce duk da jagororin hukumar na yanzu sun biya wasu daga cikin haƙƙoƙin nasu, ba a kai ga biyan alawus ɗin ƙarin girma ba, da na tafiye-tafiye ba.