Muna jiran ganin hukuncin da za a ɗauka kan kashe ’yan Arewa a Edo — Sarkin Musulmi
Published: 31st, March 2025 GMT
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya bayyana rashin jin daɗinsa dangane da kashe matafiya ’yan Arewa da aka yi a Jihar Edo.
Saboda haka Sarkin ya ce suna dakon ganin hukuncin da za a ɗauka dangane da faruwar wannan mummunan lamari.
Kisan Mafarauta: Matakan da gwamnatin Edo da ta Kano suke ɗauka Dalilin da muka soke Hawan Bariki — Masarautar ZazzauDa yake miƙa saƙon gaisuwar Sallah ga Gwamnan Sakkwato, Alhaji Ahmad Aliyu a ranar Litinin, Sarkin ya ce “mun ga an ɗauki mataki kan yanayin da ake ciki a Jihar Edo.
“Saboda haka muna jiran ganin hukuncin da za a ɗauka bayan kammala bincike don ba wani dalili ka kashe mutum ba tare da wani haƙƙi ba.
“Muna kiran jami’an tsaro da su tashi tsaye domin tabbatar da cewa jama’a ba su fusata ba sun ɗauki hukunci a hannunsu.
“Idan a wani wurin mutanen banza sun ɗauki hukunci a hannunsu, mu a nan Sakkwato ba za mu bari a yi abin da bai kamata ba.
“Mu sanya ’yan uwanmu da abin ya faru da su a cikin addu’a sannan muna kiran gwamnati da jami’an tsaro su ɗauki matakin kare rayukkan jama’a,” a cewar Sarkin Musulmi.
Sarkin ya ƙara da cewa “bai kamata a riƙa yaɗa abin da bai dace ba a kafafen sadarwa na zamani da za su janyo tashin hankali a wurin da ake da zaman lafiya.
“Duk wani abu da ya faru a wani wuri, bai kamata wasu da ke can wani wurin na daban su ce za su ɗauki mataki a Sakkwato ko Kano ko Kaduna kan wani abun da ya faru a Jihar Edo ko Legas ba.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Kano mafarauta Yan Arewa
এছাড়াও পড়ুন:
An kashe Falasdinawa kusan 30 a wani sabon kisan kiyashin Isra’ila a Gaza
Bayanai daga Falasdinu na cewa akalla Falasdinawa 35 dane suka hada da kananan yara aka kashe a wanisabon kisan kiyashi na Isra’ila a zirin Gaza.
A cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza, wadannan hare-haren sun yi sanadin mutuwar mutane 35 tare da jikkata 109 a cikin sa’o’i 24 da suka gabata.
Adadin wadanda sukayi shahada sakamakon yakin kisan kare dangi da Isra’ila ke yi a yankin da aka yi wa kawanya ya zarce 52,400.
Adadin wadanda suka jikkata kuma ya kai kusan 118,014 tun daga watan Oktoban 2023.
Majalisar Dinkin Duniya dai ta yi gargadin barkewar ayyukan jin kai a Gaza.
Hukumar samar da abinci ta duniya (WFP) ta fitar da wani kakkausan gargadi game da matsalar jin kai da ke kara tabarbarewa a Gaza a dai dai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-haren bama-bamai da kuma killace fararen hula da ke fama da yunwa.
Tun cikin watan Maris ne Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya haramta kai kayan agaji zuwa Gaza, a wani mataki da ya ce na da nufin tursasa Hamas ta amince da tsawaita matakin farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Isra’ila.