Miji ya kashe matarsa saboda abincin buɗa-baki a Bauchi
Published: 2nd, March 2025 GMT
’Yan sanda sun cafke wani magidanci mai shekaru 50, Alhaji Nuru Isah kan zargin lakaɗa wa matarsa dukan da ya yi ajalinta a dalilin abincin buɗa-baki.
Bayanai sun ce taƙaddamar wadda aka soma gudanar da bincike a kanta ta auku ne a ranar Asabar a yankin Fadaman Mada da ke Jihar Bauchi.
Burina in yi fice kamar mahaifiyata — Maryam ‘Yar Auta Abubuwan da ya kamata a sani game da azumin watan RamadanaKakakin rundunar, CSP Ahmed Mohammed Wakil ya ce, “saɓani ne ya kaure tsakanin wani mai suna Nuru Isah mai shekara 50 da matarsa ta biyu, Wasila Abdullahi kan tsarin abinci da kayan buɗa-baki na gidan.
’Yan sanda sun ce bincike farko na nuna cewa mijin ya yi amfani da bulala wajen bugun matar mai shekaru 24, “inda ta yanke jiki ta faɗi, da aka kai ta asibitin koyarwa na jami’ar Tafawa Ɓalewa ne likitoci suka tabbatar da rasuwarta.”
Sanarwar ta ƙara da cewa ’yan sanda sun kama mijin, sun ɗauko bulalar da aka yi amfani da ita, sannan kuma za a yi binciken ƙwaƙwaf a kan gawar.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Auwal Musa Muhammad, ya bayyana cewa za a gudanar da bincike domin tabbatar da adalci a lamarin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Azumin Ramadan Jihar Bauchi
এছাড়াও পড়ুন:
Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — Trump
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar amfani da ƙarfin soji kan Najeriya matuƙar gwamnatin ƙasar ba ta dakatar da kisan da ’yan ta’adda masu iƙirarin jihadi ke yi wa Kiristoci ba.
A yammacin jiya Asabar ne Trump ya umarci Ma’aikatar Yaƙin Amurka ta Pentagon da ta soma tsara yadda za a kai hari Nijeriya bayan da ya yi zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a ƙasar.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce Amurka a shirye ta ke ta aike da sojoji da manyan makamai cikin Najeriya don bai wa Kiristocin kariya.
Barazanar shugaban na Amurka na zuwa ne kwana guda bayan ya yi iƙirarin cewa an kashe Kiristoci aƙalla 3,100 a Nijeriya ba tare da ya bayyana takamaimai inda ya samu waɗannan alƙaluma ba.
“Muddin gwamnatin Nijeriya ta ci gaba da bari ana kashe Kiristoci, Amurka za ta dakatar da dukkan tallafin da take bai wa Nijeriya nan-take, kuma mai yiwuwa za ta shiga wannan ƙasƙantacciyar ƙasar, cike da ƙarfin gwiwa domin kawar da ’yan ta’adda masu kaifin kishin Musulunci waɗanda ke yin wannan ta’asa,” in ji Trump.