Najeriya ta kama hanyar gyaruwa – Remi Tinubu
Published: 7th, March 2025 GMT
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta shirya buɗa-baki a Fadar Gwamnati da ke Abuja, inda ta tabbatar wa ’yan Najeriya cewa ƙasar nan na kan hanya gyaruwa nan ba da jimawa ba.
A yayin jawabinta, ta jaddada muhimmancin tausayi da jin-ƙai a tsakanin rayuwar ɗan adam.
Wani mutum ya yanke jiki ana salla a Masallaci, ya rasu a asibiti Dakatarwa: Har yanzu ni Sanata ce — NatashaTa buƙaci kowa ya kasance mai aikata alheri tsakaninsa da Allah, ba don neman yabo ko amincewar mutane ba.
A yayin buɗa-bakin, Farfesa Azeezat Adebayo, Shugabar Sashen Nazarin Addinin Musulunci na Jami’ar Ilorin, ta bayyana cewa tausayi da jin-ƙai su ne ginshiƙai na kyakkyawar rayuwa a tsakanin al’umma.
Ta tunatar da mahalarta buɗa-bakin cewar watan Ramadan lokaci ne na koyon kyawawan ɗabi’u, kuma ana buƙatar a aikata alheri ga kowa, ba wai ga Musulmai kaɗai ba.
Daga cikin manyan baƙi da suka halarci buɗa-bakin akwai Uwargidan Tsohon Shugaban Ƙasa, Dame Patience Jonathan da matar Mataimakin Shugaban Ƙasa.
Sauran sun haɗa da matan gwamnonin jihohi, ministoci mata, matan ministoci da matan shugabannin hukumomin tsaro.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Buɗa baki gyara Najeriya Ramadan shan ruwa Uwargidan Tinubu
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya tsawaita wa’adin aikin shugaban hukumar Kwastam
Shugaba Bola Tinubu ya ƙara wa Bashir Adeniyi, Shugaban Hukumar Kwastam ta Ƙasa, karin shekara ɗaya a kan wa’adin da ya kamata ya yi na shugabancin hukumar.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa a ranar Alhamis.
Mutum 9 sun rasu a hatsarin kwale-kwale a Jigawa NNPCL ya sake haƙa sabbin rijiyoyin man fetur 4 a KolmaniA cewarsa, wa’adin Mista Adeniyi zai ƙare ne a ranar 31 ga watan Agusta, 2025.
Amma yanzu Shugaba Tinubu ya amince da ƙara masa shekara ɗaya, wanda hakan ke nufin zai ci gaba da zama a kan kujerarsa har zuwa watan Agustan 2026.
Sanarwar ta bayyana cewa ƙarin wa’adin zai ba shi damar kammala wasu muhimman ayyuka da yake yi.
Waɗannan ayyukan sun haɗa da gyara da inganta harkokin Kwastam, kammala wani shiri da zai sauƙaƙa kasuwanci a Najeriya, da kuma taimaka wa ƙasar wajen cika alƙawuran da ta ɗauka ƙarƙashin yarjejeniyar ciniki ta Afirka (AfCFTA).
Shugaba Tinubu, ya yaba da ƙwazon Mista Adeniyi da yadda yake gudanar da ayyukansa.
Ya ce ƙarin wannan wa’adin zai taimaka wajen inganta hanyoyin tara kuɗaɗen shiga a hukumar, da kuma tabbatar da tsaro a iyakokin Najeriya.